| Wahalar da muka sha
in ji wata mata musulma
Daga M.M. Awwal
Kullum idan wani rikici ya faru, wanda ya kai ga kashe rayuka, to yawanci mazaje akan kashe, kuma su suka fi tafka asara. To amma a karshe duk wata wahala tana karewa a kan mata, domin sune ake kashe masu mazaje, ake kone masu dukiyoyinsu da ya kamata su gada wajen mazansu domin kula da marayu. Saboda haka sai ka ga sun shiga wani mummunan hali Wakilinmu na Kaduna Musa ya leka unguwar Sabon Tasha domin jin halayen da wasu irin wadannan mata suke ciki, inda ya sami hira da wata mata mai suna Malama A’ishatu Sa’idu. Ta fada masa yadda aka kashe mijinta da irin asarar da suka yi, da halin da suke ciki da dai sauran bayanai. Ga yadda hirar ta kasance.
MUJAHIDAH:Malama menene sunanki?
MALAMA A’ISHA: Sunana Aisha matar Sa’idu.
MUJAHIDAH:A takaice za ki iya ba ni labarin abin da ya faru gare ku a lokacin rikicin?
MALAMA A’ISHA:Eh, to ni dai lokacin da abin ya faru, bayan an dade ana ba-ta-kashi da arnan, bayan kura ta lafa sai na ga ban ga Maigidana ba, saboda haka sai na tashi ina shiga cikin gawarwaki ko na gan shi, amma ban gan shi ba. Ba inda ban duba, ko in tambaya ba, domin ko an gan shi, amma ban sami ganin shi ba. Domin ni na bar shi a gida, da shi da babban yarona, amma da ya ga abin ya fi karfinsu suka ruga da gudu suka bi ta wani layi, a can ne akwai wani Ibo sai ya ce yarona ya je domin ya boye shi, shi kuma mijina da Mahaifinsa da kannan mijina su biyu, sai suka fita da gudu, to suna cikin gudu ne sai suka hadu da arnan. Nan take aka kashe su duka su hudun, aka jera gawarwakinsu, da ubansu da shi da kannansa biyu aka kona. Kuma a wannan wurin kawai su ashirin da tara ne aka kashe kuma aka kona su duk.
MUJAHIDAH:Yawanci irin wadannan bala’o’i sun auku mata sukan shiga cikin wani hali to ban sani ba ko ke ma kin shiga wani irin wannan hali?
MALAMA A’ISHA:Eh, to gaskiya mun ga hidima irin na kaka-nikayi, to amma duk da haka ni kam da sauki, domin surikina shi ya kawo ni nan, kuma aka ba mu wannan daki kafin komai ya yi daidai.
MUJAHIDAH:To yaya maganar abinci da sutura da sauran kayan rayuwa?
MALAMA A’ISHA:To, a gaskiya a halin da muke ciki, maganar abinci kam sai dai muna nema ga Allah tunda ba a bar mana komai ba. An kona abincinmu, an kona dukiyoyinmu, an kona gidajenmu, abin da muka mallaka duk an kona shi, domin shi ma kanshi Maigidan nawa bayan an kashe shi sai aka je (arna) inda yake sana’ar bulo dinshi na siminti, aka farfasa bulon, duk an kwashe aka zuba a rijiya da yake debo ruwan aikin, aka cika rijiyar yashin da tifa ta kawo domin aikin bulo an kwashe an watsar a kan titi, kuma gidan bulo din yana nan ne FAMA kusa da Sabon Tasha.
MUJAHIDAH:Yawanci idan irin wannan firgici ya faru wasu mata masu ciki yakan zube, kuma wasu sukan haihu a wajen gudun hijira, to ban sani ba ko an sami irin wannan a Sabon tasha?
MALAMA A’ISHA:Eh, to lallai na san wasu. Domin akwai wata ana ce mata A’isha, itama ta haihu. Akwai kuma wata matar Badamasi. Akwai wasu ma ana cikin wannan gudun cikunansu suka zube har su uku, domin ma a nan gidan aka rufe su, saboda tsananin fargaba.
MUJAHIDAH:Amma ba za ki iya sanin hakikanin, ko mata nawa bane?
MALAMA A’ISHA:Eh, to lallai abin da ya sa ba zan iya sanin yawansu ba shi ne lokacin da ake guje-gujen ni hankalina ya tashi saboda ban san halin da mijina yake ciki ba, to amma a takaice wanda na sani a nan eriyarmu kawai shi ne mata uku sun yi bari kuma na ga mata uku sun haihu.
MUJAHIDAH:Yaya maganar taimako, domin mun ji an ce wai gwamnati da jama’arta sun ba da taimako, to ban sani ba ko ya iske ku?
MALAMA A’ISHA:To a gaskiya ni dai bai same ni ba, domin sai ma a yau ne na samu zuwa Nasiril Islam, to shi ne na sami wani mutum ya taimaka mani da rabin buhu na dawa da garin rogo, ya kuma ba ni Naira ashirin ya ce in yi kudin mota.
MUJAHIDAH:To yanzu tunda ga shi an bar ki da ‘ya’ya takwas kuma ba ki samun gudummuwa daga hukuma ko Jama’atu, to yaya kike rayuwa da ‘ya’yanki?
MALAMA A’ISHA:A gaskiya rayuwa, ina da jama’a. Na gode wa Allah, ina nan zaune akan kawo mani dan abin da ba a rasa ba, kuma surikina yana dan taimaka mani.
MUJAHIDAH:Da ma can kina sana’a ne, kamar wasu mata, ganin cewa kina da iyalai da yawa?
MALAMA A’ISHA:To a gaskiya ni ina daga cikin mata masu sana’a, domin na sami kamar shekara goma sha takwas a nan Sabon Tasha, duk wanda ka tambaya cewa A’i Mai gado ko A’i mai kabat za a kawo ka wajena, domin a takaice asarar da na yi, to ta ran mijina ne kawai ya share man komai, domin ina da injin nika biyu, na wuta daya, na ruwa ma haka. Amma duk arna sun kona. Kuma ina da katon firji shi ma sun kona. Ina da kabot-kabot, wadanda na saya na tara don in sayar, su ma an kona. Kuma ina da gadaje wadanda na sara zan sayar su ma an kona, domin ka ga ma irinsu can a cikin gida kusa da katanga, ka gan su ma a kone ko.
MUJAHIDAH:To yaya maganar tsagwaron kudi?
MALAMA A’ISHA:Lallai akwai wasu kudi Naira dubu hamsin da biyar 55,000 da Maigidana ya ba ni in ja jari da su, su ma sun kone.
|