Rikicin Kaduna: Yadda aka jefa mata cikin bala’i da masifa
Daga M.M. Awwal
Rikicin da ya faru a Kaduna, na kabilanci cakude da addini ya sanya jama’a da dama, musamman mata musulmi cikin wani mummunan hali na rayuwa. Kuma wannan hali ya fi muni ne ga mata, saboda sune aka kashe masu mazajensu aka bar su da marayu, ba abinci ba sutura, wasunsu ma babu wuraren kwana, domin an kone masu gidaje, kuma ba su da kudin kama gidan haya.
Wakilinmu na Kaduna, Musa, ya yi takakka har zuwa Narayi inda abin ya fi munana ga musulmi. Kodayake yawancin matan ba su son magana da ‘yan jarida, amma ya sami wasu mutane da suka san halin da matan suke ciki.
Wani Malami mai suna Alh. Kauta Narayi ya shaida wa Wakilinmu cewa akwai wata mata mai suna Malama Wasilatu, matar marigayi Alh. Bawa, wanda abokinsa ne na kusa sosai, wacce tana cikin wani hali na rayuwa domin mijinta ya mutu ya bar ta da ‘ya’ya takwaas ba wani hanyar samun abinci, sai dai idan an samo dan abin da ake taimakawa, wanda ba a rasa ba, domin a nan garin akwai masu hali irin nata fiye da tamanin.
Da yake amsa tambaya game da taimakon da ake kawowa daga gwamnati da Jama’atu, Malamin ya ce tunda wannan abin ya faru, sau daya ne kawai aka taba samun taimako, kuma ba wani mai yawa bane. Kuma taimakon da ake karbowa daga Jama’atu ba ya isowa gare su. “Ba a karbowa ne ko kuwa ana sake masu hanya ne?” tambayar da Wakilinmu ya yi masa kenan. “Oho!” in ji Alh. Kauta, saboda haka ne ma ya sa suka sake nada wani kwamiti a karkashin Alh. Muntari Ango. “To har sun fara samo mana taimako, domin jiya ma sun samo mana buhu goma, kuma a nan aka yi layi aka ba duk wanda rabonsa ya ratsa. Sai da aka fara ba matan da aka kashe mazajensu, amma a gaskiya taimkon bai taka-kara ya karya ba.” In ji Alhaji Kauta.
Alhaji Kauta ya ci gaba da shaida wa Wakilinmu cewa “A gaskiya mata suna cikin halin kaka-nikayi domin kamar yadda na fada maka, an kashe masu mazaje, an kona masu gidaje da dukiyoyi. Ga ma wannan matar ta Alh. Bawa ce, amma an kona, kuma ba su da abinci ba tufafi. Sannan abin bakin ciki shi ne su masu karbo kayan taimakon sai su rinka yin gaban kansu da shi. Shi ya sa ma muka sake nada wani kwamitin karbo taimako.”
Saboda haka Alhajin ya yi kira ga gwamnati cewa idan irin wannan rikici ya taso ta rinka daukar mataki cikin gaggawa, “Domin a nan Narayi, tun ranar Litinin (a fadan Fabrairu) arna ke ta kashe musulmi da kona masu dukiya, sai ranar Alhamis, sannan aka turo sojoji. A cikin wadannan kwanakin duk inda ka duba a nan gidaje da dukiyoyin musulmi ne ke cin wuta. Hatta masu gidaje ma idan an kashe mutum sai a jefa cikin rijiya ko a kona. Misali a ranar Talata da abin ya faru wata mata ta same ni a hanya za mu gudu zuwa Barnawa, take ce mani tana rike da yaranta suna gudu, amma arnan suka tare su suka kwace yaron. Ta yi juyin duniyar nan kada su kashe mata da, amma ina, yaron yana cewa ‘ki yafe mani mama,’ a gabanta suka kwantar da yaron suka yanka,” in ji shi.
Shi kuwa Malam Abubakar Aliyu Haske, wanda shi ne Na’ibin Limamin Narayi, kodayake arna sun kashe babban Limamin, ya shaida wa Wakilinmu a hirarsu cewa a yanzu haka akwai diyarsa tana nan a cikin gidansa wacce an kashe mata miji, kuma akwai irinta da yawa a wannan unguwa ta Narayi. Kuma ya ce abin takaici da ban tausayi ba su da abinci ba tufafi, wasu ma ba wurin kwana. Ya ce “an ce wai ana aiko da taimako to amma a gaskiya mu dai taimakon ba ya samun mu.” Ganin haka ne ma ya sa wasu mata da kansu suke tafiya can Ja’matun suke karbo dan abin da ya samu.”
Malamin ya ce “Wata rana na je Jama’atu domin wani mutum ya ja ni wai ko ma samo ‘yan tufafi, to a can ne na ga wasu mata su biyar sun zo neman taimako, to amma abin da na ga an ba su wato masara. Wallahi sai da na zubar da hawayena. Saboda haka irin wadannan mata da suka rasa mazajensu, suna cikin wani mummunan hali, kuma suna bukatar a taimaka masu. Domin a gaskiya abin ya yi wa gwamnati yawa, sai al’ummar musulmi sun taimaka, musamman ma Jama’atu, domina cikin gidana akwai diya ta da aka kashe wa miji da kuma matar kanina, amma ba abin da na taba samu daga Jama’atu, ko wani wuri.”
Da yake amsa tambayoyi game da halin da suke fuskanta a daminar nan da ta sauka, Malam Abubakar Haske ya shaida mana cewa “A gaskiya matan nan suna fuskantar babbar matsala ta ruwan sama, saboda yawancin gidajen nasu babu rufi, kuma ginin kasa ne, da zarar ya sha ruwa sai ya rushe, domin su arna bukatarsu shi ne su ga ba gidajen musulmi a gurin.” Malamin ya ce shi kansa sai da ya je kauyensu ya dan roro dan abin da zai gyara gidansa da shi.
|