| Taron nasarar Hizbullah a kan Yahudawa a Lebanon
Daga Yusuf Abdullahi
Malamai da dama ne suka gabatar da jawabai masu matukar muhimmanci da fa'idantarwa a taron mu'utamar din da 'yan uwa mata suka shirya a Zariya mai taken 'Nasarar Hizbullahi a kan Yahudawa a Lebanon.' A ranar Asabar 19/05/1421, rana ta biyu bayan fara taron, an gabatar da laccoci ne guda hudu a otel din Kongo daga safe zuwa yamma. An fara taron ne da misalin sha daya na rana da jawabin budewa daga bakin Malama Zeenat Ibraheem. A gajeren jawabin nata ta tabo tarihin kafuwar gwagwarmayar 'yan uwa mata a kasar nan, inda ta ce sun fara ne suna 'yan kadan, ana nuna musu kyama da izgilanci, suka daure har Allah ya kawo su ga wannan matakin na yanzu, ta yadda har gayyace-gayyace kan yi musu yawa ma a halin yanzu, sakamakon fahimtar harkar da ake yi da yawa. Malamar ta ce daga cikin matakan da suka dinga bi wajen isar da sakon harkan nan har da kai ziyarori na wa'azi ga makarantun 'yan mata daban-daban a kuma lokuta daban-daban. A nan ta yi godiya ga manyan Malaman da suka amsa gayyatarsu suka zo duk da nisan su. Sannan kuma ta yi godiya ga dukkan wadanda suka taimaka ga samun nasarar wannan taro.
Daga nan ne kuma ake kirawo Malami na farko wato Shaikh Ali Hasan Kazeem, wanda a cikin jawabinsa ya kawo batutuwa masu tarin yawa, wadanda suka hada da tarihin kafuwar wasu kungiyoyi kafin zuwan Hizbullahi, sannan kuma kafuwar hizbullahi din, wadda ya ce an kafa ta ne saboda dalilan da suka hada da gwagwarmayar neman 'yanto kasar daga mamaya, danniya da kuma bakin zaluncin Isra'ila tare da kokarin rayuwa cikin 'yanci, walwala da kuma kyakkyawan rayuwa. Shaikh Ali ya ce an kafa wannan kungiya ne domin Allah (T) da kuma wadannan manufofi a karkashin jagorancin Shugaba, wanda al'umma ta yarda da shi, suka bi shi kuma suka sallama masa a kan wannan. Wannan kungiyar, tun bayan kafuwarta, in ji Shehin Malamin, ta kasance mai amfanar da jama'a matuka domin tana yin iya kokarinta wajen kyautata halin zamantakewar jama'a. Hizbullahi tana yin haka ne kuwa ta hanyar sama wa jama'a asibotoci da makarantu da gyara magudanan ruwa da kuma taimaka wa marasa galihu. Hizbullahi kuma har wa yau takan shirya tarurruka da bitoci da sauran abubuwan da ke hada kan jama'a domin gudanar da ayyukan da suka kamata. Sakamakon irin wadannan hidimomin da Hizbullahi ke gabatarwa ne ta samu kyakkyawa kuma kakkarfan alaka tsakaninta da kusan dukkanin al'ummar musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, kamar kiristoci alal misali. Shaikh Ali ya ce hakika wannan kungiyar ta Hizbullahi ta ci sunanta domin kuwa kungiya ce mai karfin gaske, ta yadda har tana da gidan rediyo da telebijin da makamantansu, kuma ya yi nuni da cewar hatta gwamnatin da ke akwai a Lebanon ta sallama domin ta san da zaman Hizbullahi, kuma ba yadda za ta yi da ita. Malamin ya ce wannan fa duk a halin yanzu kenan, nan gaba abubuwan ma za su fi haka, insha Allah, in ji shi.
Har ila yau ya dan tabo da bayani a kan hadaddiyar kungiyar malamai da ke akwai a can Lebanon, wadda ke magana da murya daya, wadda ya ce ita ma ba karamar nasara bace a gare su. A karshe ya yi godiya ga Malam Zakzaky (H) saboda gayyatar su da ya yi zuwa Nijeriya, ya kuma yi fatan nan ba da dadewa ba shi ma zai ziyarce su. Ya kuma gode wa 'yan uwa da dama da duk masu taimakon addinin Allah (t) a ko'ina suke cikin duniya.
Bayansa ne kuma aka kirawo wani masanin tarihi dan kasar Sudan wato Farfesa Ahmad Khami, wanda aka ba shi maudu'in a kan halin gwagwarmayar Sudan. A cikin jawabinsa Farfesan ya kawo masaniyar da yake da ita game da can Sudan daga shekarar 1985. duk da haka ya yi bayani a kan kugiyoyin kwatar 'yanci dadaddu da aka samu a can Sudan din tun da dadewa. Daga nan ne kuma Farfesan ya kawo bayani a kan abin da ya kirawo 'tafiya tare' da malamai suka yi ta yi da gwamnati, musamman daga lokacin Ja'afar Numeri, har zuwa kan Janar Albashir na yanzu, da kuma yadda alakar Dk. Hasan Turabi ta kasance da Albashir tunda dadewa izuwa halin da ake ciki yanzu, halin da ya ce ya fito fili a halin yanzu cewa wannan alakar ba kyakkyawa bace, kuma ba haka ya kamata ta kasance ba, domin kuwa wannan alaka tasu ba ta haifar da da mai ido ba, kamar yadda kowa ke iya gani a halin yanzu, in ji shi.
Bayan jawabinsa ne aka ba da damar yin tambayoyi, kuma masu jawaban suka amsa. Daga nan ne kuma aka bukaci Malam Zakzaky ya ba da jawabi a takaice a kan jawaban masu jawabai na baya, inda a nan kuma Malam ya yi tsokaci a kan nasarar ta Hizbullahi da kuma hanyar da suka bi wadda ta dace. Sannan kuma Malam ya fito da wasu darussa muhimmai da ya kamata a lura da su a irin alakar da ta auku wadda a baya aka kwatanta da aure da saki a tsakanin shugaban kasa Albashir, wanda Malam ya nuna ya fi kama da miji da kuma shi Dk. Turabi, wanda aka kora daga majalisar dokoki, harkar kuma da yake yi wa jagoranci ta koma baya sosai. Malam ya yi cikakken sharhi a nan, inda ya nuna cewa hanyar Allah daban take da ta Shaidan kuma ba sa haduwa. Daga nan ne kuma ya juya ga harkar Musulunci ta wannan nahiya tare da matakan da takan bi daki-daki da kuma irin nasarar da take haifarwa kamar yadda kowa yake gani. Malam ya ce "Mune Hizbullahi a nan, kuma kamar wadancan da sannu insha Allah (T) mu ma harkarmu za ta bunkasa a nan din sosai." Daga nan ne aka bukaci Malam din da ya rufe taro da addu'a, inda aka tashi da misalin karfe biyu na rana.
Bayan cin abinci da sallah ne, kuma aka dawo domin kammala zangon karshe na laccocin wannan rana, inda aka da laccoci guda biyu. A wannan yammacin an fara laccocin ne da misalin karfe hudu da sauraron jawabi daga Shaikh Mahir daga Lebanon. A jawabin nasa da ya dauki lokaci yana gabatarwa. Shi ma ya yi cikakken bayani ne a kan matakan da Hizbullahi ta bi har Allah (T) ya ba ta nasara, wadanda suka hada da hadin kan da ya samu asali daga hadaddiyar 'kungiyar Malamai' wadda ta taimaka matuka wajen hada kan sauran al'ummar Lebanon baki daya.
Malamin ya kammala da nuni a kan cewa lalle nasarar da kungiyar Hizbullah ta samu a kan Yahudawan Isra'ila ba komai bane illa yin Allah (T). Ya yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki a kan wannan nasarar da ya ce ta musulmi ce duk ba su mutanen Lebanon kawai ba. Daga nan ne kuma aka kirawo mai magana na biyu, kuma na karshe, wanda shi ne Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). A nasa jawabin da za a iya kira talkhisin dukkan jawaban da aka gabatar, Malam ya yi nuni a kan nasarar da Allah (T) ya ba wa kungiyar Hizbullahi da cewa nasara ce da za ka iya kira ta Musulunci a kan kafirci baki daya, musamman da yake ita Isra'ila ne samun kariya da tallafin kumajin karfirci na duniya baki daya.
Malam har wa yau ya yi cikakken sharhi a kan hanyoyin da Hizbullahi ke bi wajen tafi da al'amuranta, hanyoyin da ya jinjina mata a kansu. Da Malam yake kwatanta matsayin gwagwarmayar Musulunci a nan Nijeriya da ta Lebanon, ya ce mu gwagwarmyarmu ta nan jaririya ce, sai dai falillahil hamd muna koyi ne da wadanda suka yi gwagwarmaya kuma suka ci nasara. A nan ne ma ya ce tun farkon gwagwarmayar nan an san ta da sallama wa jagorancin bawan Allah Imam Khumaini (Q) kuma a bayansa Magajinsa, Sayyid Ali Khamne'i. Kuma ita wannan harkar na yin koyi da kyawawan ayyukan magabata, musamman ayyukan taimakon jama'a domin dada kyautata alakarmu da su.
Malam har wa yau ya yi nuni a kan koyi da kyawawan ayyukan Hizbullahi da ma'abota harkar Musulunci suke yi a wannan nahiyar, kodayake akwai 'yan bambance-bambance tsakanin mu da su. A nan ne ma Malam ya ce game da misalin hadin kan da Shaikh Mahir ya fada da ke akwai a Lebanon tsakanin ba ma musulmi da musulmi kawai ba, hatta ma da kirista, Malam ya nasabta hakan da ilimi ne da ake da shi a can, sabanin nan, inda ake da matukar jahilci, inda ake da Bakatafe wanda ke ganin zaman lafiya zai samu ne kawai idan an kashe Bahaushe! Abin takaici. Sai dai duk da haka Malam ya ce in da za a dage wajen isar da sako da kyakkyawan usulubin da ya dace har a cocina, wannan zai iya haifar da muhimmiyar natija matuka, in ji Malam.
Da ya juya kuma kan batun 'kungiyar malamai' ko 'majalisar malamai' ya ce sabanin Lebanon mu a nan akwai malamai ne masu matsanancin kwadayin da gwamnatin za ta iya yin amfani da su ma domin kawo wa addini cikas. Har Malam ya ba da misali da wani Malami da yake zuwa taro da rekoda, ya dauka, kuma kafin ya kai ma sai ya dauki kansa a rediyon ko da ta cikin aljihun ne ya ce 'to ga shi nan ni dai ba ruwana,' abin takaici da bakin ciki. Da ya juya kan shugabanni kuwa, ya ce mu a nan Allah ya sawwake, domin kuwa sabanin wsu wuraren, muna da wasu shugabanni ne barayi, azzalumai, fasika, kuma tsinannu, wadanda al'amarin jama'a sam bai dame su ba, illa iyaka su da iyalinsu suka sani. Har Malam ya ba da misali da wani hadama da babakere da arigizon kwangilar da 'yan majalisa ke ta yi kawai, alhali talakawa na nan na ta fama da wahalar gaske. Malam ya kammala jawabinsa da cewa kuma ba abinda zai kai mu gaci ya kwace mu daga irin wannan faganniyar illa bin tafarkin Allah Madaukakin Sarki daki-daki kamar yadda sunnar Allah ta tabbatar.
Daga nan ne aka rufe taron da addu'a daga bakin Shaikh Ali Hasan Kazeem da misalin karfe biyar da wasu mintuna na yamma. Dukkan mahalarta wannan taron sun yi matukar farin ciki, sakamakon kyawawan fa'idojin da suka samu daga cikinsu.
|