Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 12                                     Jimada Thani 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 12
  Jimada Thani
 DAGA TEBURIN EDITA
Irin Wainar da muka toya
 SHARHIN MUJAHIDAH
A gaida 'yan uwa mata
 WASIKU
Wasiku uku daga 'yan uwa mata
 BABBAN LABARI
Taron Nasarar Hizbullah a Zariya

Hizbullah ba za ta taba daukan kaskanci ba

Dole ne Malamai su hada kansu

Wajibi ne mu zama abin koyi

 HIRA TA MUSAMMAN
Shawara ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a

 LABARI
Lalacewar mata a Nijeriya

 FADAKARWA
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata
 NASIHA
Rayuwar aure a Musulunci

Kishiya Ko Abokiyar Zama?

 YARA
Ka tausaya ma dabbobi
 LIKITA
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda
 TARIHI
Gwarzantakar Ummu Wahab(R.A)
 RAYUWA
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Shirin hana almajirai bara zai yi nasara kuwa?

Hattara 'yayan talakawa

Kikan duba shafin

Almizan
  kuwa?
The Witness
  kuma fa?
Babban Labari
Hizbullah ba za ta taba daukar kaskanci ba

Daga Yusuf Abdullah

An bayyana shahararriyar kungiyar nan ta Hizbullah da cewa wannan kungiya ce da ba za ta taba daukar kaskanci ba. Wanda ya bayyana hakan shi ne Shaikh Ali Hasan Khazim, daya daga cikin 'yan kungiyar ta Hizbullah da suka kawo ziyara a nan Najeriya. Ya kuma bayyana hakan ne a ranar Alhamis 7/08/2000 a lokacin da ya gabatar da jawabi ga dubban al'ummar musulmi da suke taru domin sauraron jawabinsa a masallacin Juma'a na cikin gari da ke Kanon Dabo.

Tun farko an bude taron ne da karatun Alkur'ani, sannan aka gayyato dalibai na Madrasatul Fodiyya da ke Rijiyar Lemo, wadanda suka rera wakoki na yabon Manzo (s) da Sayyida Zahra (AS) tare da fareti wanda ya kayatar da kowa. Daga nan ne kuma aka kirawo mai masaukinsu a Kanon Dabo, wato Malam Muhammad Tur,i wanda bayan takaitaccen jawabi da bayyana wa 'yan uwa sunayen wadannan baki, ya mika abin magana ga daya daga cikinsu, wato Shaikh Ali Hasan Khazim.

A farkon jawabin nasa ya yi godiya ga Allah, Mabuwayi, Madaukaki a kan wannan dama da ya ba su na ziyartar 'yan uwa a nan Nijeriya. Sannan kuma ya yi jinjina da kuma godiya har wa yau ga wanda ya kira Hujjar Musulunci da musulmi (Hujjatul Islam wal muslimin) wato Shaikh Ibraheem Zakzaky (h).

Bayan nan ne kuma ya nuna matukar gamsuwarsa da yadda ya ga dalibai sun gabatar da abin da suka gabatar. Abin da ya ce ya sa shi kwalla. Daga nan ne kuma ya juya ga kungiyar ta Hizbullah, wadda ya ce akwai wasu kungiyoyi da suka gabaci wannan kugiyar ta fuskacin assasawa, sai dai, in ji Shaihin Malamin, tun bayan bayyanar ita wannan kungiyar ta Hizbullah ta tsere sa'a, ta yadda baya ga dimbin nasarorin da ta samu zuwa yanzu, ta kuma shahara. Sannan ta samu karbuwa matuka a ko'ina cikin duniya.

Ya ci gaba da cewa wannan kungiyar ta Hizbulla ta kunshi dukkan musulmi ne 'yan Shi'a da Ahlus sunnah. kuma 'yan wannan kungiyar na gwagwarmaya ne domin kare addininsu da kasarsu da mutuncinsu. A nan ne ma ya yi wata ishara da wajibci hadin kai a tsakanin dukkanin al'ummar musulmi ba tare da la'akari da mazhaba ba. Ya ce bai kamata mazhabobi su zama sanadin rabuwarmu ba. Ya nuna cewa "bambancin mazhabobi ana samun sa a ko'ina, sai dai mu a Lebanon wannan ba ya raba kanmu, domin wannan kungiyar ta hizbullah na da Shugaba guda ne, wanda dukkan musulmi suka yarda da jagorancinsa wato Shaikh Hasan Nasrullah (H)."

Shehin Malamin ya ce saboda haka ma "mu duk muna sauraron sa ne, kuma muna kokarin ganin bayan makiyanmu ne Yahudawa da masu taimaka musu, wadanda ba ruwansu da mazhabar da kake yi matukar dai kai musulmi ne." Malamin ya ci gaba da cewa wannan kungiyar ta Hizbullah ta dade tana samun goyon bayan al'ummar musulmi da ma taimakonsu a ciki da wajen Lebanon.

Wani abin da ya ba wa mahalarta mamaki shi ne cewar Malamin dukkan al'ummar lebanon sun amince da wannan kungiyar ta Hizbullah, hatta kiristoci ma suna girmama ta domin suna ganin ta a matsayin kungiyar kwato 'yanci da kuma kare kasa daga ta'addancin yan ta'adda, wato Yahudawa. A nan har ya ba da misali da mutanen da kan kaurace wa mutanensu, su zo su mika wuya ga Hizbullahi su kuma karfafa su a kan yakar Isra'ila.

Malamin, a cikin wannan jawabin ya dan waiwayo tarihin kafuwar wannan kungiyar tare da kuma wasu gudummawa da kuma muhimmiyar rawar da wasu malamai suka taka wajen kara karfafa kungiyar, musamman Shaikh Nuri da kuma Shehin Malamin nan na Lebanon wato Ayatullah muhammad husaini Fadhlullah. Malamin ya ci gaba da cewa "Rashin yardarmu da rayuwa a karkashin mulkin dawagitai ne da kaskanci a karkashin Isra'ila ya sa muka dage tsawon lokaci muna fuskantar rundunonin Isra'ila har zuwa wannan lokaci da Allah ya ba mu nasara." A nan ne Malamin ya ce ya zame dole al'ummar musulmi su hada kansu su kuma dage wajen dawo da martabarmu ta duniya baki daya. Ya ce wannan wajibi ne a kan al'ummar musulmi baki daya. Ya ce da haka ne muke samun nasara. Kuma ya ce wannan ne bin Manzo (saw) da Allah yake cewa "In kun kasance kuna son Allah ku bi ni…" Malamin har wa yau ya yi nuni a kan kyakkyawar nasara da sakamakon da gwagwarmayar Imam khumaini ta haifar a Farisa, wanda ya bayyana da "Gwarzo kuma jagoran al'umma," domin a Iran Imam ya samu ba Allah ake bi ba sai bakin zalunci da danniya kuma an mika wa mutanen yamma kasar. "Sai dai sakamakon kyakkyawan fikira da jagorancin Imam sai ga shi Allah (T) a bisa rahamarsa ya kwato wannan al'umma daga halin danniya da bakin zalunci da ta dade tana matukar fuskanta," in ji shi.

Da ya juya ga 'yan uwa musulmi kuwa mahalarta wannan taron, ya yaba masu matuka, ya kuma yi kira a gare su da su tsaya daram a kan riko da addini da kuma malamai, musamman Shaikh Zakzaky. Daga nan ne ya kammala jawabinsa da isar da sakon fatan alkhairi na Shugaban Hizbullah Sayyid Fadhlullah da sauran 'yan uwa na Hizbullah ga Shaikh Zakzaky da sauran 'yan uwa baki daya.

Daga nan ne kuma mai masaukinsu, Malam Turi ya yi talkhisin abin da Malamin ya fada, musamman domin wadanda ba sa fahimtar harshen na Larabci. Ya kuma yi godiya a gare su saboda wannan muhimmiyar ziyara da suka kawo mana. Ya kammala da fatan 'yan uwa za su yi aiki da shawarwarin da wannan Shehin Malami ya bayar.

Daga karshe an gayyaci bako na biyu wato Shaikh Mahir domin addu'ar rufewa, inda ya nufe taron da addu'a da misalin karfe bakwai saura. Mahalrta wannan taro duk sun yi matukar farin ciki da murna a kan wannan taro da aka yi mai matukar fa'idantarwa. In za a tuna dai irin wannan taro ba bakon abu bane, musamman a sauran sassan duniya, domin ba da dadewa ba ma an shirya wani taron kasa da kasa a Afrika ta kudu, inda aka gayyaci Malamai daga sassan duniya, ciki kuwa har da Malam wanda shi ma ya gabatar da jawabai a can. Sai dai muna iya cewa kamar wannan ne lokacin farko da aka gayyato wasu 'yan uwa takanas daga can Lebanon zuwa nan kasar domin jawabi a irin wannan taro.

   

Komawa Babban shafinmu