Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 12                                     Jimada Thani 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 12
  Jimada Thani
 DAGA TEBURIN EDITA
Irin Wainar da muka toya
 SHARHIN MUJAHIDAH
A gaida 'yan uwa mata
 WASIKU
Wasiku uku daga 'yan uwa mata
 BABBAN LABARI
Taron Nasarar Hizbullah a Zariya

Hizbullah ba za ta taba daukan kaskanci ba

Dole ne Malamai su hada kansu

Wajibi ne mu zama abin koyi

 HIRA TA MUSAMMAN
Shawara ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a

 LABARI
Lalacewar mata a Nijeriya

 FADAKARWA
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata
 NASIHA
Rayuwar aure a Musulunci

Kishiya Ko Abokiyar Zama?

 YARA
Ka tausaya ma dabbobi
 LIKITA
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda
 TARIHI
Gwarzantakar Ummu Wahab(R.A)
 RAYUWA
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Shirin hana almajirai bara zai yi nasara kuwa?

Hattara 'yayan talakawa

Kikan duba shafin

Almizan
  kuwa?
The Witness
  kuma fa?
Babban Labari
Dole ne malamai su hada kansu

Daga Yusuf Abdullah

Shaikh Ali Hasan Khazim, dan kungiyar Hizbullah daga Lebanon ya nuna matukar muhimancin tare da fa'idojin da ke tattare da hadin kan al'ummar musulmi, musamman ma malamai daga cikinsu. Ya bayyana hakan ne a lokacin da shi da abokinsa Shaikh Mahir suke ganawa da Malam Muhammad Turi a masaukinsu da ke otal din Kongo, Zariya. Shaikh Khazim ya yi cikakken bayani a kan cikakkiyar jituwar da ke akwai a tsakanin malamai mabiya mazhabobi mabambanta a Lebanon karkashin 'kungiyar Malamai', ta yadda Malamai ke da karfi da kuma ikon fada-a-ji matuka, ta yadda har gwamnati kan yi shahin ja da su, musamman saboda dimbin mabiyan da suke da su. Irin wannan kyakkyawar alaka da ke akwai a tsakanin malamai, akwai irinta a tsakanin sauran al'ummar musulmi na Shi'a da Sunni baki daya, ta yadda suke tafi da al'amuransu na aiki da karatu da kasuwanci da auratayya da ma sauran mu'amaloli baki daya tare.

Shi ma Shaikh Mahir ya yi karin haske ne a kan kyakkyawan halin zamantakewa da mu'amaloli da ke wanzuwa a wannan kasa. Sun yi nuni da cewa da 'yan matsaloli da akan samu nan da can a wasu lokutan. A jimlace dai mutum zai iya cewa komai falillahil hamd. Sun ma yi mamakin ganin rashin samuwar irin wannan kungiyar a nan, musamman da yake kasar cike take da musulmi.

A nasa bangaren Shaikh muhammad Mahmud Turi ya yi musu karin haske a kan yadda al'amura suke a kasar nan, musamman da yake akwai bambance-bambance tsakanin Nijeriya da kuma can Lebanon. Daga nan ne kuma Malam Muhammad Turi ya mika wasu tsarabobi ga wadannan baki, tsarabobin da suka hada da riguna dogwaye ga kowane dayansu da wandunansu dinkin mutanenmu na nan kasar tare da huluna da Alkur'ani mai tsarki rubutunmu na nan da kuma tafsirin Alkur'ani na Shaikh Abdullahi Gwandu da ake kira Dhiya'ut tawheed da kuma kayan sawa dogaye, huluna da kuma takalma. Dukkaninsu sun nuna matukar farin cikinsu da wadannan kyaututtuka, wadanda suka gwaggwada kuma suka yi musu daidai. A nan ne ma Shaikh Ali Hasan ya ce su zai sa ya yi khutuba ya kuma ba da sallar Juma'a da zarar ya koma, musamman da yake shi Limami ne a can. Bayan wannan muhawarar ne aka yi sallama da juna, inda suka jarraba Hausa da fadin "Mun gode muku."

   

Komawa Babban shafinmu