| Dole ne mu zama abin koyi a cikin al'umma
Daga Yusuf Abdullah
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana cewa dole ne 'yan uwa musulmi maza da mata masu gwagwarmaya su zama abin koyi a cikin al'umma. Malam ya bayyana haka ne a ranar Lahadi 20/8/2000 a lokacin da yake rufe mu'utamar din da 'yan uwa mata suka shirya na kwana biyu. An rufe wannan taro ne a Jim Harrison Hotel da ke Zariya.
Shehin Malamin ya yi jawabi a kan batutuwa da dama masu muhimmanci, inda ya fara da ilimi da aiki. A wannan bangaren Malam ya nuna cewa dole ne 'yan uwa su nemi ilimi, kuma ya tafi tare da aiki, domin ba wata fa'ida ga mai ilimin da ba ya aiki da iliminsa; abin da Malam ya kwatanta ta da kamar labaran duniya mai karantawa wane,wane.
Har ila yau dai game da wannan batu, Malam ya ce kuma dole ne neman ilimi ya zama saboda Allah ba domin nuna sani ba ko kuma jayayya; abin da Malam ya ce wasu kan yi ta yadda suke haddace hadisai da isnadu da matani ba domin Allah ba, sai dai kawai domin nuna sani da kuma jidali. A nan kuma Malam ya ce falillahil hamdu a daidai gwargwado muna iya cewa 'yan uwa na kwatantawa, sai dai a kara, domin sabili da kwatantawar ne ma wasu da yawa kan sha mamakinmu, musamman da yake su sun saba da karatu ne ba tare da aikin ba. Ya ba da misalin hijabi, wanda tilas ne a kan kowace mai imani ta saka shi, kuma ya rufe dukkanin jikinta baki daya. Sai dai abin takaici mutane ba su damu da dabbaka wannan sunnar ba, sai dai kasancewar tsayin dakan da 'yan uwa mata suka yi a kan saka shi ya jawo mata da dama na sakawa. Sai dai wani babban abin da ke bambanta 'yan uwa mata na wannan harkar da sauran mata shi ne dabi'u. Malam ya ce domin wata na iya saka hijabin kuma ta dinga shewa ko guda ko ta hau babur ko ma ta je wajen kalangu da dai sauransu. Har Malam ya ba da misalin wadansu da ke saka hijabi, sai dai abin tausayi da sunan yunifom maimakon sutura ta wajibi a kan mata masu imani. A nan ne Malam ya kara jaddada muhimmanci ko wajibcin dacewar fadi da aiki. Malam ya ce "Dole ne a matsayinki na 'yar uwa musulma da ta kasance mai kyawawan halaye baya ga lazimtar hijabinta, wanda babban alami ne ga addini," in ji shi.
Wani babban batun kuma da Malam ya yi magana a kansa shi ne tarbiyya, abin da ya ce dole ne 'yan uwa su yi karatun tarbiyyar addini ta kowane janibi na rayuwa. Hakika a nan Malam ya karfafa wannan batu matuka ga 'yan uwa mata musamman, da yake su ke tarbiyyar yara. Ya ce tilas ne a matsayinsu na masu tarbiyyantarwa su zame masu cikakkiyar tarbiyyar a matakin farko.
Malam ya jawo hankalinsu a kan hanyoyin da suka fi dacewa wajen jan kunnen yara ta hanyar dasa musu tsoron Allah da kuma Musulunci da kuma kushe miyagun al'adun Bature maimakon tsoratar da su da irin su mage da dodo da makamantansu domin neman su bar abin da suke yi mara kyau.
Wani muhimmin batun kuma da Malam ya yi magana a kansa shi ne tsafta. A kan wannan batu Malam ya dauki dogon lokaci yana nuni a kan wajibci da kuma muhimmanci tsafta ga 'yan uwa baki daya. Ya dada fadakar da 'yan uwa game da hadisin tsafta rabin addini ne. A nan ne ya ce lalle kuma dole ne 'yan uwa mata su bai wa wannan janibi matukar muhimmanci ta yadda dole ne su kula da kansu fiye ma da maza. Sannan kuma dole ne har wala yau su dage wajen kula da tsaftar yara domin abin da matukar takaici ne a zo taro a dinga jin wari. Ya ce wannan lokacin ma sai ka ji warin ko da an sa turare. Dole ne ko da wasu suna datti da wari mu mu zamo masu matukar tsafta ta yadda dole ne a yi koyi da mu ta wannan janibi. Sannan kuma dole ne tsaftar ta hade kowa da kowa a cikin iyali, tare kuma da dukkan sassan gida, wanda ya hada da kula da tsaftar gida da bandaki da dai sauransu.
Daga cikin muhimman abubuwan da Malam ya tunatar a kai har da batun mujahada, wanda ya ce shi ma janibi ne mai muhimmancin gaske, abubuwan da suka hada da sallolin dare da karatun Kur'ani da kuma sauran nau'oin zikiri baki daya. "Da haka ne ake samun al'umma ta gari," in ji shi, "domin idan kowanenmu ya yi kokari ya zama mutumin kiriki, hakan zai haifar da iyalin kirki, inda daga nan kuma sai a samu al'umma ta gari baki daya."
A karshe Malam ya jaddada muhimmancin tsayawa daram a kan hanyar Allah (T). Ya ce dole ne a kan kowanenmu. Ya kammala da fatan Allah ya taimake mu, ya kuma tabbatar da mu a kan hanyarsa baki daya. Bayan nan ne aka ba da dama ga 'yan uwa mata suka yi tambayoyi, Malam kuma ya amsa musu. Da yake manyan bakin nan da aka gayyato daga Lebanon suna nan 'yan uwa mata sun bukaci nasihohi daga gare su, a matakin karshe. A nan ne Shaikh Mahir ya fara da fadin, "Addini dai nasiha ne, kamar yadda ya zo a hadisi. Abin da zan ce muku ya ku 'yan uwa shi ne ku ji ku kuma yi biyayya ga wanda yake jagorantar ku zuwa ga Allah (swt), domin idan kun bi Shugabanninku a kan hanyar Allah kun bi Allah ne, kuma hakan ne zai kai mu ga samun cikakkiyar nasara."
A nasa bangaren Shaikh Ali Hasan Kazeem ya kawo wa 'yan uwa wasu 'yan gajajjerun kissoshi ne guda uku, wadanda ke dauke da darussa masu dama. Daga ciki ya kawo gwagwarmayar Ayatullahi Nuri tun shekarun 1905 kafin makiya Allah (t) su batar da shi, har ya gangaro ga jihadin Imam Khumaini, ya yi sharhi da karin haske a kan sadaukarwar da ya yi shi da mabiyansa, abin da ya kwatanta da sadaukarwa shigen irin ta Imam Husain (AS). "Wannan sadaukarwa ce ta haifar da samuwar jamhuriyar Musulunci a Iran," in ji shi.
A game da Hizbullah kuwa, cewa ya yi kada a dauka wannan nasara ta samu kawai cikin ruwan sanyi ne, sam ba haka bane, domin kuwa nasarar Hizbullahi wata aba ce da ta dauki dogon lokaci. Kuma ita sakamako ce ta sadaukar da dukiya da ma rayuka da wasu bayin Allah muminai da dama suka yi.
Daga nan ne ya kammala da yin nuni a kan wajibcin da ke kan 'yan uwa na tsoron Allah (t), abin da ya ce zai sama wa mutum ilmi da daukaka, har ya karanta ayar ku ji tsoron Allah, sannan Allah ya sanar da ku …" A nan ne ma har ya ce in ka je Lebanon akwai malamai da yawa masu yawan shekaru da ilmi, amma malamai 'yan Hizbullah duk da karancin shekarunsu suna da ilmi sakamakon aiki da kuma tsoron Allah da su ke da shi. Malamin ya kammala jawabinsa ne a karshe da addu'ar alkhairin ga Shaikh Zakzaky (H) da sauran 'yan uwa almajiransa baki daya, da kuma fatan samun kariya da nasara tare da dacewa a kan wannan gwagwarmaya da ake yi.
An dai kammala taron ne da rufewa da addu'a da misalin karfe daya na rana, inda aka tashi kowa cikin murna da annashuwa.
|