Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 12                                     Jimada Thani 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 12
  Jimada Thani
 DAGA TEBURIN EDITA
Irin Wainar da muka toya
 SHARHIN MUJAHIDAH
A gaida 'yan uwa mata
 WASIKU
Wasiku uku daga 'yan uwa mata
 BABBAN LABARI
Taron Nasarar Hizbullah a Zariya

Hizbullah ba za ta taba daukan kaskanci ba

Dole ne Malamai su hada kansu

Wajibi ne mu zama abin koyi

 HIRA TA MUSAMMAN
Shawara ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a

 LABARI
Lalacewar mata a Nijeriya

 FADAKARWA
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata
 NASIHA
Rayuwar aure a Musulunci

Kishiya Ko Abokiyar Zama?

 YARA
Ka tausaya ma dabbobi
 LIKITA
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda
 TARIHI
Gwarzantakar Ummu Wahab(R.A)
 RAYUWA
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Shirin hana almajirai bara zai yi nasara kuwa?

Hattara 'yayan talakawa

Kikan duba shafin

Almizan
  kuwa?
The Witness
  kuma fa?
Fadakarwa
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata

Wannan shine cikakken jawabin Malam Ibraheem Zakzaky a wurin rufe Mu'utamar da 'yan uwa Musulmi mata suka yi a Zariya kwanakin baya. A sha karatu lafiya.

Assalamu alaikum warahmatullahi Ta’ala wa barakatuhu.

Kullum a irin wadannan tarurrukan tamkar akan kwakkawafa tunanin mutum ne don ya zama masa kamar tsarin matakan da zai bi har ya zuwa mai yiwa wani taro shigen irinsa. Amma ba zai wadatar ba a matsayin makaranta. Makaranta ana yin karatu, kamar misali a nan zai koyi karatun Alkurani, da tafsiri. A nan mutum zai koyi hukunce-hukunce na tsarki alwala da salla da sauransu. A nan ne zai koyi sira, tarihi, a nan zai koyi sauran fannoni na ilimi. Wannan makaranta kenan shi ko wannan taron ya sha bamban da makaranta, domin kamar wani abu ne da akan tattaro abin da aka dai karanta, musamman ma bangaren da ake tattaunawa, wanda ya shafi tunanin mutum, yadda zai harhada masa tunaninsa ya zama yana da tunani sahihi.

Shi tunani a wajen mutum muhimmin abu ne, ganin cewa kwakwalwa da Allah ya yi masa, ya sa masa tunani shi ne ma mahimmin abin da ya bambanta shi da sauran halittu masu rai. Idan mutum ya lura da sauran halittu masu rai, dabbobi, banda tsire-tsire, su ma suna da kwakwalwa, amma ba su da fahimta irin wadda Allah Ta’ala ya yi wa mutum. Irin kwakwalwar da Allah ya yi wa mutum, wanda ya ba shi hankali, shi ya bambanta shi da sauran dabbobi. Kuma ya yi masa wannan baiwan ta tunani domin ya yi amfani da shi. Don haka a cikin Alkur’ani Allah Ta’ala a gurare da dama yakan rika cewa “Me zai sa ba za su yi tunani ba? Me zai sa ba za su lura ba? Me zai sa ba za su hankalta ba? A hankalta mana. Wannan ga ma’abotan hankali ne,” da sauran su, da sauran su. Wanda kowane lokaci aya tana magana a kan mutum ya sa kwakwalwarsa ya yi tunani, ko kuma in ce ya sa zuciyarsa ko dukkan biyu. “Ku yi tunani.”

Sakamakon tunaninka, sai ya zamana ayyukanka gaba daya sun sake. Tunanin mutum shi ya bambanta shi da sauran halittu. Baiwa ce wadda Allah Ta’ala ya ba mutum, kuma ya yi masa ne domin ya yi amfani da shi. Ayyukanmu dukka sakamakon yadda muke tunani ne. Don haka ne ma ya zo a hadisi cewa tunanin sa’a guda ya fi ibadar shekara. Domin fakam da yawa a lokacin da ka tuna abu, ka yi tafakkuri na wani gajeren lokaci, to abin da ka hankalta sakamakonsa, sai ya zama ka kanza rayuwarka har ka mutu, duk tsawon rayuwarka. Sakamakon tunanin da ka yi.

Abin da muke nufi da tunani a nan shi ne yadda dan Adam yake hangen abubuwa, yake kallon su da idanu na basira, yake gane su. Kamar yadda Allah Ta’ala yake cewa “Dama ba idanu ke makanta ba, zukatan da suke kirazza su suke makanta.” Idan mutum makaho ne a basira (ana ce wa gani na zuciya basira sabanin ganin ido), wato idan ya zama idonsa na gani amma zuciyarsa ba ta gani, to zai ga abubuwa amma ba zai fahimce su ba. Kuma ta fuskacin wannan tunani (fikira) ta nan ne muka bambanta da sauran (Me zan ce musu? Ba zan iya ce musu harkoki ba. To bari in ce musu harkokin) harkoki na Musulunci a kasar nan. Akwai harkoki daban-daban na ma’abuta addini. Akwai harkan addini wadda za mu iya cewa na gargajiya, wanda yake dama mutum haka ya girma ya ga ake yi, haka kuma ya san kowa yake yi.

Akwai harka wadda za mu iya ce mata ta gargajiya, wadda yake mutane suna addini kamar yadda suka girma suka ga ana yi. Sun saba dama akwai yadda suka dauki ma’anar addini a matsayin hanyar bautan da suka wayi gari suka ga iyayensu da kakanninsu a kai. Wannan harka ta gargajiya ita kawai abin da ta sani shi ne abin da daman aka saba ake yi. Da za a ga wani abu sabo, ko da ma yana littafi, in dai ba a san ana yi ba, sai ma a yi ta cewa to an ji akwai a littafi, to amma wa ka ga yana yi? Fakam da yawa ma akan sami wasu su ce “Ka fi Malam wane ilimi ne, shi yaushe ka ga yana yi? Kamar misali lokacin da al’amarin lullubi ya zo. Abin da kawai suka sani suna karantawa a littafi, sun ga ka’ida ana yin lullubi, amma dai a aikace ba sa yi, illa iyaka dai in mace za ta yi sallah, sai ta dan debi duk abin da za ta iya samu ta saka a kanta, shi kenan. Sauran jikinta ma duk da yawa yana waje. Haka nan kowa ya girma ya ga ana yi. Haka ma matar Malam take yi. Saboda haka idan wani ya tashi ya ce ai ana rufe duk jiki ne banda fuska da tafuka, sai a ce “E,to haka aka ce a littafi, amma wa ka ga yana yi? Ko matan Malamai ma ka ga suna yin wannan ne?” Wannan muna iya cewa harka ta addini ta gargajiya har yanzun akwai ta. Wadanda yake su duk wani abu yadda dai suka saba suka ga haka ake yi, haka nan ne.

Ko a na gargajiya din akwai lokacin da aka sami harkan Faila ko? Wanda yake su sun dan bambanta. Alal misali akwai wadansunsu su matansu na lullubi, sukan sa matansu su yi lullubi. Har ma akan kira su da sunannaki daban-daban. Wasu ana ce masu ‘yan kabalu. Ai matan dan kabalu za ka ga duk ka lullube jikinta, ko abin da ya yi kama da haka nan.

To ana nan kuma, muna iya cewa aka sami harka ta Musulunci da ta bullo a tsakanin mutanen da ba a tsammani, sune harkar Musulunci da ta bullo tsakanin ‘yan boko a makarantun boko, musamman tsakanin dalibai. Wanda yake ita ba ta yi tasiri sosai-sosai a gari ba, amma muna iya cewa an fara jin duriyarta, wanda yake daga cikinta ne harkarmu ta tsiro. Ko ba a lura ba? Amma lallai harkar Musulunci wadda ta fito daga fuskacin dalibai harka ce wadda ta fara nunar da mutane mafuskanta, wato makomar kasar nan a nan gaba, al’umma. Kuma tana magana a kan abubuwan da suka shafi al’umma. Ga dai harkoki nan da yawa ba sai na lissafa maku ba.

Yanzu ma ga harkar wadansu gungun mutane da ake cewa Izala, ga wasu harkoki kuma suna ta kirkirowa daban-daban. Amma wani abu da ya bambanta mu duk a wadannan harkoki shi ne a yadda muke kallon abubuwa da irin namu idon basira. Ta yadda wani abin sai mu hange shi mu ce ga yadda yake, amma wasu sai su ce sam ba haka bane. Kuma haka din ne, amma su suna fadan abin ne ta yadda su suke kallon sa, sakamakon yadda muke tunaninmu.

Tunani, da yake da kwakwalwarka kake yi, ba kawai kana ganin sa bane, kana dora shi a kan abin da ka sani ne. Akwai wani lokaci da nake yi wa ‘yan uwa bayani, na ce a gaskiya fikirar mutum ta doru ne a kan abubuwa guda biyu. Ta doru ne a kan iliminsa da kuma shiriya. Shi ilimi karatu ne, za ka yi ta karanta shi daga tushe. Kuma bai da iyaka. Daidai gwargwado mutum yana diban abin da yake iya diba ne. To amma shiriya baiwa ce daga Allah, wanda Allah kan ba wanda ya so. Shi ya sa sai ya zama wani mutum yana da ilimi, amma kuma tana iya yiwuwa bai da shiriya. Amma da wuyan gaske ka samu mutum yana da shiriya bai da ilimi. Sai dai a ce yana da guntun ilimi, kuma fikirarsa za ta zama nakisa idan yana da shiriya bai da ilimi. In ana iya samun ‘yan uwa sun damfaru da harkar sosai, amma ba su da ilimi, dole ne kuma fikirarsu ta zama nakisa.

Shi kuma a wannan bangare na fikira, ana son kai ka fahimci abin, ba ana son ya zama kawai kai kana yin abu ne kawai saboda an ce maka ka yi ba. Ana son kai ma a kanka ka fahimta ne. Ba wai ka ce tunda dai haka ake yi a harkan nan, to kai ma bari ka yi haka nan ba, ba tare da ka fahimci menene wannan abin ba da me ya sa ake yi ba. Wato kana yi ne sakamakon ka yarda haka ne, shi ya sa ma kake yi. Musamman ma akalla an ga ‘yan misalai, musamman a waki’ar da ta gabata, wanda ainihin mahukuntan kasar nan suka zartar da shawarar cewa za su murkushe wannan harka din gaba daya su huta. Kuma suka gwada wa harkar iyan karfinsu. Sun yi amfani da duk abin da suke da shi na karfi, amma kuma a karshe sai ya zama harkar ba ta rusu ba.

A daidai wannan lokacin kuma har wala yau an fuskanci jarabawowi, wanda ya nuna lallai mutanen nan suna da wata fikira, wadda ta bambanta su da mutane sauran jama’a. Kuma sun san abin da suka sa ma gaba. Don alal misali duk yadda aka yi a harzuka ‘yan uwa su yi wadansu ayyuka na cikin harzuka ba a iya sa su sun yi ba. Har ma suna cewa idan suka rinka tursasa wa ‘yan uwa, tursasawar ta yi tsanani za su harzuka su zo su yi fada, su yi kashe-kashe. Amma sai ya zamanto har aka gama, a rubuce, a sane ba wani wanda ya ce ga mutum daya rak da ‘yan uwa suka kashe, walau dan sanda ko soja ba a kashe ko guda daya ba. Da ko an kashe ma, da ka ji suna ta babatu. Ko da wani ne ya mutu bisa hatsari da ka ji sun ce ‘yan uwa suka kashe shi. Amma sai ya zama yanzu da za a ce a yi wa ‘yan uwa shaida, a fadi gaskiya, ‘yan uwa suna kashe mutane? Da za su ce ba sa kashewa.

Kuma duk sun yi abin da ka iya harzuka mutum domin ya rasa hankalinsa ya yi abin da duk ya ga dama, amma sai ya zama ‘yan uwa ba su rasa hankali ba. Alal misali sun san cewa in suka taba iyalan musulmi, musulmi kan zama idonsa ya rufe, don haka ma har suka kama matayenmu suka kulle, suka ci zarafin ‘ya’yanmu kanana, tsammaninsu ko mu ma za mu ce, to shi kenan tunda abin haka nan ne, to mu ma bari mu je mu yi masu. Su suna da hanyoyin da suke abubuwansu, mu kuma muna da namu hanyoyin. Sakamakon mu mun san inda za mu, kuma mun san hanyar da za a bi a je shi ya sa muka bambanta da sauran mutane.

Wani yana iya sanin inda za shi, amma bai san ta inda za a bi ba, saboda haka in ya kama hanya sai ya yi ta baganniya, sai ya fada ma wani guri ya saki hanyar gaba daya. Wanda ko ya san inda za shi, ya kuma san inda ake bi, to sai ka ga duk wani abu da za ka yi masa ba za ka ja hankalinsa ba. Sai ya yi ta tafiyarsa a kan hanya ya san dama inda za shi, kuma ya san nan ne ake bi a je.

Wannan muna iya cewa ba wani abu bane illa sakamakon kyakkyawan fikira na ‘yan uwa a wannan al’amari. Kuma wannan abu yana bukatar a kullum a dinga kwakkwafa wa mutane, don kada ya zama tunanin mutum ya zo ko ya sauya ko kuma shi kansa yau da kullum ya fara manta wasu abubuwa. Don haka ne makasudin irin wadannan tarurrukan a kwakkwafa wa mutane tunaninsu.

Da yake wannan na ‘yan uwa mata ne, sau da yawa bayan abin da ya shafa harka gaba daya a wajen ‘yan uwa mata akan karfafa bangaren da su kuma bangaren da ya shafe su su kadai, wato bai shafi ‘yan uwa maza ba, ko kuma su ya fi karfafuwa a nasu bangaren. Wato kodaya suna hada da maza da mata duk sun hadu a kai, amma dai wannan ya fi karfi ta fuskacin dabi’a. Ta wannan yana da muhimmanci alal misali a san cewa, kamanninmu fa ba shi ne hijabobi da ‘yan uwa mata suke sawa ba, ba shi ne ya bambanta su da sauran mutane ba. Ba ‘uniform’ ne ba, wanda kamar yake bambanta soja da dan sanda ba, ko dan agaji, ko mai gadi. Idan da ‘uniform’ ne na riga wanda ake sawa, sakamakon kana harka sai ka sa irin wannan riga din, to shi kenan wata ma wadda ba ta wannan harkar idan ta shigo ta sa irin wannan, sai a ce ga ta da riga irin na su wadancan. To amma ba riga bace, imani ne da aiki. Sakamakon ta yi imani da wani abu, ta san wani abu, tana aikata wani abu. Shi ya banbanta ta.

To rigar na daya daga ciki ne ba shi ne ba. Kuma yana da muhimmanci lallai ‘yan uwa mata ya zama ba suna alamta rayuwarsu ta fuskacin riga ne kawai ba. Domin fakam da yawa wasu sun dauka abin da ake neme su da shi shi ne su sa riga din, su yi ‘uniform’. In suka sa ‘uniform’ din, shi kenan sun gama. Kuma sau da yawa ma idan aka dinga taron mata, abin takaici sai a yi ta yi masu magana a kan hijabi. Kai ka ce daman abin da aka ce kawai shi ne “Ya ku wadanda kuka yi imani mata ku sa hijabi,” shi kenan sai aka kyale su. Allah Ta’ala yana cewa a cikin littafinsa ya saukar mana da tufa domin mu yi ado. “Ya ku ‘ya’yan Adam mun saukar muku da tufa wanda zai suturce muku tsiraicinku, kuma ado.” Ana sa sutura saboda dalilai daban-daban, saboda kariya, ana sa shi kuma saboda ado. Kariya daga zafi ko rana, kuma ana sa don ado. Sai kuma ya ce “Amma suturar takawa ita ta fi.” Wato tufa ta takawa, ita kuma a zuciya take, to shi kuma ya fi sutura ta riga.

Suturar takawa fa za a ji shi ne daga lokacin da mutum ya bude baki ya yi magana, za a ji irin maganar da zai yi. Daga lokacin da ya aikata wani aiki, za a ga irin aikin. Kuma wannan sakamako ne na abin da yake zaune a zuciyarsa, abin da ya kulla a ransa. Ta nan ne za a iya ganin sutura irin ta takawa.

To idan ya zamana sutura ce kawai ta kyalle, amma babu takawa a zuciya, za mu ga dabi’a wadda ta fito daga wannan suturar ta ma muzanta suturar. Wannan fikirar, wadda zai mikar da rayuwar mutum, ya rinka kwakkwafa shi yau da kullum, wani abu ne da lazim yake bukatar karatu. To shi fa karatu ba shi da wani iyaka. Ba ana yin shi ne a gama ba.Ana yin shi ne a yi ta ta yi, ko ba a lura ba? Da ana yi ne a gama da sai mutum ya ce lallai duk na gama karatu. Ko da a ce ka karanta Alkur’ani, ka kuma karanta fassarar Alkur’ani, to ba kana gamawa bane. Kakan karanta ne a matsayin ibada. Sannan kuma har wala yau har fassararsa kana nan kana ta nema ne. Kullum kuma kana kara fahintar wani abin da ba ka fahimta bane. Haka kuma hadisan Manzon Allah, ballantana su ma da ba za ka iya gama karanta su ba. Duk karatunka wata rana sai ka ci karo da abin da ma ba ka taba ji ba; kuma lallai daga Manzon Allah ya gangaro, kuma ba ka taba sanin sa ba, kuma hadisi ne. Mutum yana iya dukan kirji ya ce ai ya karanta ayoyin Alkur’ani, saboda suna da iyaka, amma ba wanda zai ce shi ya san duk hadisai, saboda su har yanzu karuwa suke yi. Ba wai sun karu ne tuntuni ba, tallansu, inda muke samun su ta yiwu wani bai zo maka ba, yana nan tun tuni amma kai bai zo maka ba. Wata rana sai ka zo ka gani. Ko wani dadadden littafi ne, amma ga shi ba ka san shi ba, sai wata rana ka zo ka gan shi. Ko kuma ka dade kana karanta wani hadisi, amma ba ka gane ma’anarsa ba; sai da ka ga wani hadisi, sai ka ce, to ashe shi ya sa aka ce kaza a guri kaza.

Ko kuma wancan ashe an yago wani bangare ne na magana din, aka ce Manzon Allah ya ce kaza, alhali cikon magana ne. Ainihin tushen maganar ma ba ka ji ba. Sai ran da ka ji tushen, sai in ka hada ma’anar ta fito daban. Kila ma ya zamanto sabanin yadda kai ka fahimta ne a da, ko akasin ma kai yadda ka fahimta ba. Saboda haka karatu za a yi ta yi. Wannan ilimi da ambaton Allah sune ma ainihin abincin da ruhin mutum ke ci. kamar yadda gangan jikin mutum ke cin abinci ya sha ruwa domin ya raya, to haka ma ran mutum shi kuma yana rayuwa ne da ilimi da ambaton Allah. Wato ba ana gama ba shi bane.

Kamar yadda muka san cewa mutum matukar yana da rai ba yakan ci abinci bane, ya gama cinyewa shi kenan sai ya zama ya bari ba. Kamar ya yi lissafi ya ce tun daga lokacin da aka haife shi kawo yanzu, ya ce ya shekara kaza, saboda haka idan aka yi lissafin buhun shinkafa da ya ci, a ce ya ci buhunhuna, ka ce kai! Ya kuma ci dawa, kila ma buhunhuna, ya ce daga yanzu ba ya sake cin abinci ba. To ai fa in ya zauna shi kenan, sai ya kanjame, ya kanjame! Matukar yana da rai yana cin abinci, ko ba alura ba?

Haka kuma riga ba za ta wanku ta yi fes-fes ba kamar farar riga a wanke ta ta yi fes-fes a goge ta, ya ce tun da ya wanke ta ya goge ta, to ya kara wani, yanzu ba zai sake wankewa ba, sai ya yi ta sawa kawai. To ba da jimawa ba, za ka ga ta yi daka-daka. To kamar yadda kullum kan cin abinci ne, kuma kullum kana wanka ne, kullum kana wanki ne, haka nan ma ranka kullum kana raya shi ne da kusanta shi da Allah ta hanyar ilimi da ibada.

Idan ka yi sake ta wajen neman ilimi, to ainihin zuciyarka za ta fara dodewa, ta fara tsatsa, ballantana ma a ce ka yi sake wajen ibada. Ko duka biyun, da ibada da ilimi. Idan ka yi sake wajen ibada kana ta karatu ne, to tana iya yiwuwa ka yi ta karatu din, har ma ainihin abin da ya kamata a karanta a yi kuka, kai sai ka yi dariya! Ka iya fassara! Kamar wasu da wani ke gaya min cewa Malaminsu ana karantawa yana fassara masu tabara. Aka karanta ayar da ke magana ta ‘yan uwata cewa “masu gargadi ba su zo maku bane?” Su ce “Sun zo mana muka ce karya suke yi, kaza-kaza.” Aka fadi irin yadda su ‘yan wutan suke, halin da suke ciki, wato ‘yan aji suka yi zugum, shi kuma Malamin sai yana dariya. Ya iya fassarawa ne. Ko ba a lura ba? Fassara ne daidai ya iya, ba lallai wai ya damu da abin da yake cewa bane. Ko ma ka ga mutum ya yi wata magana, sai ya ce to “menene naka na damuwa, ko ma ka yi ka shiga ne?” Ko abin da ya yi kama da haka nan. Wato tana iya yiwuwa mutum ya yi ilimi, amma ya zama ba shi da takawa. Ya iya karatu, ya iya fassara, amma ba aiki, kuma ba ya shigar sa sam-sam. Wannan sakamako ne na rashin ibada.

Tana yiwuwa mutum shi kuma ya yi ta ibada, shi kuma ba ya da ilimi. Ya zama ya yi ta jin kansa, har ya rinka ganin cewa, to ai shi wane ne, shi na kusa da Allah ne, mai yawan ibada ne. Amma idan ya zamana mutum ya gwama biyu, ilimi da ibada, yana sani yana aikatawa, ta nan ne za mu rinka ganin ginannen mutum yana ta ginuwa. Haka nan yake rayuwa har ya zuwa lokacin da mutum zai cimma Ubangijinsa. Ba wani abu ne da ake fasawa ba, ba kuma ana kare shi bane. Kamar misalin da na ba ku na cin abinci da wanka da wanki. Da mutum zai yi wankansa duk gaba daya. Ya sami sabulansa fakiti guda, ya wuni yana wanka da bokiti wajen hamsin, duk ya gama wankanshi, ya ce to daga yanzun sai badi, ba zai sake wanka ba. To in aka fara zubawa a guje in aka gan shi saboda tsananin warinsa ai ka ga..

Haka ibada, ba za ka ce da watan Ramadan za ka yi duk salloli, da daddare ba ka barci, kuma kana ta karatun Alkur’ani, to amma tunda Ramadana ya kare kuka yi sallama da bauta. Dama al;adar ruhi kenan, an ce yana kyau ne ko mini, wato ruhin mutum yana iya zama mummuna, sakamakon mummunan aikinsa. Kuma yakan zama kyakkyawa, sakamakon kyakkyawan aikinsa. Ka ga in yana da kyau aka munana shi, ba dole ya yi muni ba? Kamar yadda yake in yana da muni aka kyautata shi zai yi kyau. Saboda haka wani abu ne da mutum ba yana yi ne ya gama ba. Idan ya bari, to shi kenan zai koma baya ne.

Ka ga waton kenan wani aiki ne da ake son mutum ya sa a gaba, ya yi ta yi har zuwa ranar da zai riski Ubangijinsa. Ran da ya riski Ubangijinsa Allah Ta’ala zai masa sakamako a kan abin da ya aikata, musamman ma karshen rayuwarsa. Saboda abin da ya karata a kai a kansa zai tashi. Kun ga watau kenan tunda ibada tana bukatar ka san me kake yi, ba kawai ka rinka yi ba, don an ce haka ake yi ba, tunda kana bukatar ka san hikimar da ke ciki, don me ya sa kake wadannan, ya zama lazima kenan ka yi karatu.

To na san mukan ta ce wa ‘yan uwa su yi karatu, a wannan bangaren muna da matsala babban gaske. Kullum mukan ta cewa a yi karatu, to amma sai ka ga abin da muke son a karanta din, da jama’an da ya kamata a je a yi karatun gunsu duk sun karanta, lasiman ma littattafai. Ga wanda ya iya karatu da rubutu zai iya zama ya yi karatu abin sa, wasu abubuwa ne zai nemi a yi masa bayani, in bai gane ba. To amma sai ya zama muna da karancin littatafan kwarai da gaske. Abubuwa da daman gaske, wanda yake in an fada ma mutane sai su ga kamar sabon abu ne ma aka fito musu da shi, alhali dama can yana nan shekara da shekaru, illa iyaka ba a san shi bane. Kamar yadda muka ginu a al’adu, al’adu da yawan gaske ba a litattafai ake karantawa ba. In za ka ga tsohuwa tukuf- tukuf, in a wajen ilimi ne na al’adar gargajiya to sai dai a kwatanta ta da babban Farfesa, duk al’ada ta sani. A ce kaka akan yi kaza kuwa a wajen buki? Ta ce “a’a akan yi kaza ne, ai wannan sai ya janyo kaza,” saboda duk ta san wadannan bayanan. Kuma ba karatun littafi ta yi ba, saboda ta girma a kai ne.

Wanda aka haifa a gidan da ya ginu a kan ilimi da aikata shi, to sai ka ga kawai zamansa ma a nan kawai ya sa ya girma da sanin abubuwa da daman gaske, sakamakon muhallin ilimi. To mu a nan sai ya zama ilimin an bukunce shi sosai, kuma ba mu girma da shi ba. Saboda haka kullum aka fada ma mutum, sai ya ga cewa kamar wani abu ne aka zo masa da shi sabo. To a nan gaba kam, da yake yanzun yana shiga mutane a hankali, a hankali, kamar tunanin mutane dangane da wasu abubuwa suna ta sassauyawa. Kwanakin baya ake ce min (ko a wani kauye ne ko?), kan batun ashura sai suka ce masu (su dama ana cika-ciki ne, kowanne sai an yanka masa kazarsa. A samu katuwar tukunya duk a zuba kajin. In an gama dafawa kowa ya dauko kazarsa, dama an kulla mata zare don ya gane, sai su take cikinsu. Dama an ce in ka kuskura a wannan daren ka kwana da yunwa, to shekaran ma gaba daya sai dai ka tafi a haka nan a yunwace, saboda rana ce da ake so ka take ciki. To sai ‘yan uwa suka nuna wannan ba ranar da za ka take ciki bace, a bisa gaskiya take ciki ma haramun ne, banda hakan nan kuma ko da ma ba za ka take ciki ba, ba lokacin murna bane, domin ga abin da ya faru a wannan ranar. Sai mutanen garin suka ce “Kai-kai wadannan mutanen sun zo da sabon addini. Cika-cikin a ce ba za a cika cikin ba?” To har ma rigama, kayya-kayya aka je gurin su Liman. Aka yi wa Liman bayani, sai ya ce “Kayya-kayya amma in abin nan da kuke fada gaskiya ne lallai bai kamata a yi murna ba ranar ashura, to amma mu ba mu sani ba. To amma duk da dai Liman ya goyi bayan ‘yan uwa wasu sai da suka ce ba su yarda ba. Har sun taso da nufin wai za su sassare su ne ko? Sun daddauko wasu adduna da sauransu cewa lallai wadannan kawai sun fito da sabon addini. To wannan sakamakon tunanin mutane ne, yau da kullum sun ginu ne a kan ran nan cika ciki ake yi. A wasu gurare kuma ba a taba sanin ana cika-ciki ba, misali. Yau da kullum da yake ya zama sabon abu, ba da jimawa ba zai fara zama sabon abu, har ya zama ya jikin har ma a saba, har ya zama sai dai ya zama tarihi, a rinka cewa da can mutanen da sukan rika cika ciki, amma sabuwar fikira ta riga ta canza mutane. Tunaninsu ga wannan ya sake.

Haka nan yake a abubuwa da daman gaske. Misalai na da yawa na abubuwa da daman gaske, wadanda yake wasu sun tsiro a cikin tunanin harka din nan ne, kuma sun fara intishari a gari, kuma sun fara tasiri gare su, sakamakon wasu abubuwa da muke ganin haka ya kamata a yi muke yi sai kuma mutane daga baya su rinka yi. Da can mutane ba su san cewa su ce suna neman abu, kamar ko da matsa masu aka yi, ko takura masu aka yi, sai dai su yi shiru, su yi zugum, su ce “To wannan dai ba ka da yadda za ka yi, sai dai Allah ya isa kuma. A lahira kuma in an je can, Sarkin garin nan ya cuce mu ya kwace mana kaza, in an je lahira kuma..” shi kenan. Ba a san akwai shari’a ba, ba a san kuma ka dage ka nemi hakkinka ba. Shi kenan sai ka ce, to haka nan ne abin yake.

To yau da kullum kun ga ya fara canzawa. Sai ka ga mutane sukan ce ba su yarda ba, su dage su ce ba su yarda ba, kuma har a kyale su. Sun fara gani wajen ‘yan uwa sai suka fara koyo. Wasu ma da suka rasa ruwa a Zariya sai suka ce “Ba ma so! Ba ma so!! A ba mu ruwa!” Sai suka fito suka yi ta yi. To kuma kwanan nan da aka fara batun shari’a, sai suka fito har su ma har da matansu. Da za a tambaye su wanene ya koya maku wannan? Kila su ce fa ba mu muka koya masu ba. An ce a Gombe wasu suna wai “Menene kuke so?” Sai su ce “Mu shari’a muke so?” To ga tambaya a wajen kakansu ne suka koyi wannan? Ko sun gada ne wajen kakansu suka koya?

Ko ba komai akalla sun koyi cewa idan suna son abu suna iya fitowa su ce suna so. Akwai ma inda wadansu aka bude masu wuta, wannan ya faru a Maraban Jos, sai suka ce “ahaf ai mun ga ‘yan shi’a ko ana harbin su ba sa gudu.” Sai suka ki su gudu. Aka yi harbi a iska suka ce “Ahaf ku yi ta harbin ba za mu gudu ba.” To ka ga wannan kenan. Kodayake su nasun da suke su ba ‘yan shi’a an bane, da harsashin ‘yan sandan ya kare, sai suka je suka kashe DPO din, wanda yake su ‘yan uwa duk abin da suka yi su ba su kashe kowa ba, duk da kuma kashe mutum din ba yana da wata wahala bane, musamman yadda su suke kashe ‘yan uwa, har ma a samu mutum a gida a je a kamo shi a yi ta duka har ya mutu, wanene ba za a iya mishi wannan ba? Ka gaya mani, ko Gwamna ko Shugaban kasa idan abin mu ce za mu kamo Shugaban kasa ne sassaukan abu ne, duk da masu gadin nan in muka shirya sai mu je mu dauko shi tsaf! To amma ba shi ne abin da muka sa ma gaba ba, akwai abin da muke son mu yi ne, ballantana ma Sarkin gargajiya mai kahon tsumma, wanda yanzu idan ka ce masa “kai!” Shi da kansa ma zai zo. Amma ba wannan ne muka sa ma gaba ba. Akwai abin da muka sa ma gaba ne.

Wannan muna kokarin mu ce abubuwa a hankali, a hankali kun ga sakamakon yadda tunanin mutane da fikirorinsu sai ka ga cewa sun fara ganewa. Fakam da yawa wani abin idan muka dauki matsayi sai ka ga ya yi tasiri a kan mutane, tun ba ma batun shari’ar nan da ya fito ba. Ya fara tasiri, mutane sun fara tunanin ah abubuwa fa da dama a baya in suka kunno kai, sakamakon tunanin ‘yan uwa, sai mutane su yi ta mamaki su ce yaya za ku ce kaza? Sai kuma daga baya su ce ashe haka din ne. Zan ba ku misali kamar na Kafanchan din nan, ba wani dan uwa da ya je ya fada wajen kone-konen coci, aka ce ba abin da ya kamata a yi ba kenan. Wadansu suna cewa ashe ma ku kuna cewa jihadi, jihadi, ga jihadin nan ya zo amma ba ku yi komai ba. Sai daga baya abin ya zama masu wani iri, suka gano ashe ba shi ne. Sai ya zama duk cocin da aka kona sai aka biya masu cocin nunkin ba ninkin na kudin wannan cocin da aka kona masu. Kuma ba abin da ya faru. Sai ma ya zama gaba ta kai su, a kona maka coci na miliyan dayan, a ba ka miliyan goma. Sai ya gina na miliyan goma ya bar tsohon na da din yana nuna wa sauran mutane to kun ga yadda musulmi ba sa son ku, ga ma cocinku da suka kona. Nan ko ya karbi miliyan goma ya gina sabo, amma tsohon na nan bai rusa ba yana wa’azi da shi.

To haka nan ana nan, kunnowar Saddam mutane suka ce “Yawwa yanzu suka ga jihadi, ashe ma jihadi ba sai su Ayatullahi ba, kowa ma zai iya. Ga wani ma da kafcecen gashin bakinsa ma yana yi,” ka gani. Matsayin ‘yan uwa ya ba su mamaki, “Yaya za a ce kaza,” amma daga baya ta kwaranye, wadanda suka mara masa baya ma daga baya suka dawo suna jin kunya. Wasu har sun haifi jariransu sun sa masu suna Saddam. Su ba su ma san ma’anar Saddam din ba. Yana nufin karo. Tun yana yaro in ya fita ya dinga mangare yara, sai mijin mahaifiyarsa ya sa masa suna saddam, wato mai kaure yara. Shi kenan sai mutane wai su ma Saddam, to ku su ma suna mangare su wanene? Oho!

To haka nan kuma wannan al’amarin shari’a wanda ya kunno kai. Shi ma matsayin da ‘yan uwa suka dauka na cewa ai mun san shari’a. Shari’a a wurinmu tana da fadi, ba tana nufin horon mai laifi ne kawai ba. Tana nufin ka’idoji da dokoki na rayuwa ne. ba yana nufin kawai in mutum ya yi sata sai a gutsire masa hannu, in ya yi zina a jefe shi, ba shi ne kawai ma’anar shari’a ba. Abin da shari’a take nufi ka’idoji da dokoki na rayuwa. Menene haram? Menene wajibi? Menene makaruhi? Menene mustahabbi? Wadannan sune shari’a a duk rayuwanka. Komai da komai da za ka aikata akwai ka’idoji da dokoki na shari’a. To amma akwai horo mun sani. A cikin horon nan akwai wanda aka kayyade ana ce masa haddi, akwai kuma horo wanda ko Limamin lokaci ko majibincin al’amarin musulmi ko Alkali ko Hakimi shar’i’ ko kuma shura ta musulmi na iya kayyadewa daga lokaci zuwa lokaci kan abin da ya zama maslaha ga al’umman musulmi kan bai kamata a yi kaza, ba ko kuma ya kamata a yi kaza. Kuma wanda ya saba wannan za a yi masa kaza.

To shari’a a matsayin horo, akwai matakin da ake aikata shi, akwai kuma hikimar aikatawar. Amma ba mu san cewa kowa da kowa ke iyawa ba. Inda a ce abin da ake bukata kawai a yi shari’a shi ne duk wanda ya yi iko ya yi wa mutane shari’a, in sun yi laifi ya yi masu horo, to da ba bukatar Dan Fodiyo ya yi jihadi. Sai ya roki Sarki Gobir da sauran Sarakunan Hausa su yi shari’a. Shi kenan, da sai Sarkin Gobir ya ce duk a saurari Shehu. Sai ya nada shi Shugaban kwamitin shari’a da yake Sarkin Gobir bai iya komai ba, sai zagi, yana iya tara mutane ya ce “Ku saurari abin da Shehu ke gaya muku, duk wanda ya sake fusata dan abu kazan uba,” ya buga ashar, “muna katse masa hannu!, kamar yadda shari’a ta fada,” ko ba haka ba? Tunda abin illa mai iko ne zai yi.

Har ma a wani wuri nake cewa ai da ma ba bukatar a aiko Annabi Musa ya zuwa ga Fir’auna da jama’arsa tunda Firaunan ma zai iya yin shari’a. Sai kawai Allah ya ce wa Firauna “ka yi shari’a,” ko ba haka ba? Yanzu mu an wayi gari ne Gwamnoninmu ne Fir’aunonin kasa ko Wakilan Fir’auna wai sune za su yi sharia, to in haka nan ne menene bukatar adalci? Tunda yake ko fajiri ma zai iya yin shari’a din?

To wannan ina ba ku misalai ne. Akwai abubuwa da daman gaske, ko da ma mutane ba su gane ba, sai daga baya za su gane. Sakamakon kana iya hango abu daga nesa har ka fahimce shi, wannan baiwa ce ta Allah Ta’ala. Ya zama kana da fikira sahihiya, ka san ga inda za ka can, ka san ga hanyar da ake bi ta yadda ba za ka iya kaucewa ba. Wani fa yana tunanin ga inda za a, kodayake ba yana hango shi bane, kila labarinsa ya ji. Tunda in kana hango inda za ka kila kana iya gane inda za a ko? Kamar misali ka hango dutsen Kufaina ko kuma in ce ga Madarkaci can za ka, kana tafiya kana hango dutsen, ai kila da wuyan gaske ka kama hanyar Kaduna, ka ce nan za ka. A ce ina? Ka ce Madarkaci, sai a ce to ai ka bar shi baya ko? Kila wadansu ba su ma san takamaimen inda za su ba. Suna dai jin labarinsa ne kawai.

Da suna hagen inda za su din, kila da sun gane hanya. To banda hangen inda za ka ma, akwai bukatar ka san hanya. Tunda in kana hangen abu ne ba ka san ta inda za a bi a je wajensa ba, kila ka bi ta hanya mai sarkakiya, alhali akwai hanya wadda take tiryan-tiryan. Akwai bukatar sakamakon wannan mutum ya zama yana da abin da ya dora tunaninsa a kai, shi ne ko wannan abu da na ce- ilimi da ibada. Wadannan abubuwa sune muhimman abubuwan da mutum yake bukata domin ya dora kyakkyawan tunaninsa. Ba Zai yiwu kyakkyawan tunani ya fito daga kwakwalwar jahili ba. Ba kuma zai yiwu kyakkyawan tunani ya fito daga kwakkwalwan wanda ba shi da shiriya ba, ko kuma fasiki, wa’iyazu billahi. Wannan kenan.

Yana da kyau, kamar yadda na ce a fahimci cewa wannan irin zama bai fa wadatar ga barin karatu ba! Ba fa ana nufin in ka zo irin wannan shiri sai kuma ka ce sai a sake wani shirin, sai a ce to ka bari sai bayan maulidi. Sai ka je kana jira sai lokacin wani ya zo ka zo ka karkade kunnuwa ka ji karatu. Sai kuma ranar wani taron kuma ka sake zuwa. A‘a ba haka bane. Dole mutum ya zama mutum yana da wani tsari na karatu. Lasiman idan mutum ya iya karatu da rubutu da kansa.

Na san wasu ‘yan uwa ba su iya rubutu da karatu ba, ba kowa ya iya karatu da rubutu ba, amma in za ka iya rubutu da karatu da Larabci, ka sami hanyar yin karatu sassauka. Kana bukatar ka sami littafi ne ka yi ta karatu. To ko ba ka iya rubutu da karatun ba, ba ka makara ba, lasiman littafin addini. Na san akwai wasu da daman gaske, muna dalibai lokacin kusan shekaru ashirin da suka wuce muna tare da su, nake nuna masu cewa shi fa fahimtar addini ba lallai ne sai ka yi wani zuzzurfan ilimin iya magana da Larabci ba. Mutanenmu a nan da yawa sun iya karanta addini a littafi kuma ba su iya magana da Larabci ba. Za su dauko littafin addini su karanta su kuma fahimta, amma kuma inda za ka yi magana da su da Larabci ba su iya ba. Har wani yake ce mani kai dai kawai don ka ga ka iya ne. Wai su sai sun je kasar waje sun karanta. To wasunsu kuma sun je kasashen waje din suka iya Larabcin, wasu suka zama injiniyoyi, kuma yanzu duk harkan addinin ba sa yi. Wanda yake in dai son addinin kake son ka yi, kan son ka fahimci addinin, to kai tsaye ma za ka je gare shi. Mutanenmu ma suna karanta Alkur’ani ba su san ma’anarsa ba, har su sauke, har su haddace ma, amma ba su san ma’anar abin da suke karantawa ba. Sannan kuma sai su zo su sa littafi suna karantwa ana fassara masu. Ba suna koyon Larabci bane, su suna koyon addini ne. Su fara da Kawa’idi, su yi Ahalari, su yi wannan, su yi wannan, su yi wancan, suna nan suna yi, har sai ya zama kama–kama ta wannan hanya din sai su dauki kowane littafi na addini da Larabci su karanta su fahimta, wannan shi ne hanyar da ta fi dacewa, ba lallai ne mutum ya je ya iya zuba Larabci ba, ko ko ya rubuta ya karanta ba. Kana koyon sa ma a haka nan har sai ka fahita.

Ba a makara ba da karatu. Ba shakka kam in yaro ne ya fi sauki gare shi fiye da babba. Idan ana koya wa babba sai ya dade bai fahimta ba, amma dai ba yana nufin kuma ba zai fahimta bane sam-sam, ballantana ya ce ya wuce shi. Saboda haka akwai bukatar dai lallai a nacewa karatun. Kuma kamar yadda na ce ba a gamawa. su fa wadannan tamkar misalan nan uku da na ba ku kamar abinci ga jiki ko wanka ko wanki ga sutura, ba fa ana gamawa bane, ballantana ka ce na yi na gama. In har ka tattara sabulanka da ruwanka mai yawa, ka yi wanka, ka ce to daga yanzu ba zan sake yin wanka ba, sai badi, to mutane za su fara zubawa a guje. Haka inda za ka tattara karatu ka gama ka ajiye, to kuma za ka zama jahili, saboda ba ana daina shi bane. Haka ma ibada. Ba kana gama ibada ne ka zama mutumin kirki, daga nan kuma kirkin ka daina yi ba, sai ka dawo ka zama ba mutumin kirki ba,wa’iyazu billahi.

Kuma in mutum ya rike abu ya nace, yana ta yi shi ne kariyansa daga sulmiyewa. In muka ga ana tafiya da wasu, wani lokaci sai ka ga fitina ta zo sai ka ga mutum ya ja baya, wa’iyazu billah. Da ma ya ja baya ne, ka ga wani rana zai ce to bari ma in dawo. Kodayake da wuyan gaske ya dawo, saboda in ya dawo ba zai cimma wadanda suka wuce shi ba. Da wuyan gaske ya cimma masu, ba ma zai yiwu bane. Ko ya dawo zai tsaya daga baya ne. Shi ya sa ma wasu ba su dawowa, saboda sun san in sun dawo ba za su yi kafada da wadanda suka wuce su ba, dole su tsaya a baya. Shi ya sa ma sai su ga gara ma kar su dawo su yi ta fada da abin har ya zama ma su karata ba su je ko’ina ba, wa’iyazu billahi. Saboda haka wannan dai nasihar da nake yi maku kenan. Wannan mu’utamar din ya zama kamar sobin tabi ko kuma mabudi, matashiya ga ainihin naciya ga karatu da ibada har ya zuwa wasu mu’utamarori masu zuwa insha Allah.

Wassalamu alaikum warahamatullahi Ta’ala wabarakatuhu.

   

Komawa Babban shafinmu