Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 11                                     Rabi'ul Akhir 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 11
  Rabi'ul Akhir

Kikan duba shafin

Almizan

  kuwa?
Girke-girke
Miyan waken soya

Daga Zulaiha Husain Samaru.

Abin da ake tanada

  1. tumatur
  2. atarugu
  3. tattasai
  4. albasa
  5. alayyahu
  6. waken soya
  7. man gyada ko manja
  8. nama ko kifi
  9. magi
  10. gishiri

Idan uwargida ta tanadi wadannan kayan miyan sai ta sami ruwanta mai tsafta, ta wanke kayan miyan. Sai ta aje gefe guda ta dauko waken soya awon gwangwanin alale don iyalin da ba su wuce mutum shida ba. In sun wuce haka sai ki kimanta. A jika shi sai a dauki kayan miya a niko. In an niko sai ki sami tukunyarki mai tsafta ki dora a wuta da mai. Ki sami namanki ko kifi ki wanke da kyau. Ki soya.

In ya soyu, sai ki sa kayan miya ki soya. Sai ki sami waken soyan da kika jika ki wanke. In kin wanke, ki sami turminki mai tsafta ki zuba a ciki, ki kirba. In ya kirbu sai ki kwashe. Sai ki kara wa miyan ruwa kadan. Sai ki sassaka kirbabben waken soyan kamar danwake. Sai ki rufe tukunya, ki sami alayyahu yankakku. In tukunyar ta tafasa sai ki sami ludayi ki jujjuya guda-gudan na waken soya. In ya juyu (hade) ko’ina sai ki zuba alayyahon a cikin miya. In ya tausa sai ki sauke, miya ta hadu. Sai a ci da tuwon shinkafa, teba, sakwara ko tuwon masara.

   

Komawa Babban shafinmu