Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 11                                     Rabi'ul Akhir 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 11
  Rabi'ul Akhir

Kikan duba shafin

Almizan

  kuwa?
Hira ta Musamman
A daina zaluntar mata

in ji Malama Zeenat Ibraheem

MUJAHIDA: Assalamu alaikum, Malama da farko me za ki iya cewa game da korafe-korafen da mutane suke yi cewa mata a cikin wannan karni suna cikin tasku?

MALAMA: Ba zan iya cewa mata suna cikin tasku ba, tunda ba kowace mace ne take cikin wannan ba. Da ka ce an fi zaluntar mata ne a duk lokacin da aka kauce wa hanyar Allah. Amma ta yiwu wadansu suna cikin taskun. Ba kuma kowa bane. Akwai wadanda yake sun san abin da ya kamata su yi sai dai kawai akwai zalunci ta fuskar wadanda yake ba su yarda da addini ba, ko kuma ma ba su dauka addini yana da wani muhimmanci a cikin rayuwarsu ba.

Akwai kuma zalunci ta fuskar wadanda ma suke addini din. Abin mamaki ma wani lokaci a fagen gwagwarmayar ma sai ka ga akwai wadanda suke zalunci, amma ba kowa da kowa ba. Akwai wadanda ke ganin mace bai kamata tana yin wani abu na addini ba. Ko da ma cikin gwagwarmaya ne za ka ga wadansu suna ganin mace bai kamata ta shirya ko ‘programme’ ba. In ma wani abu ne mata suka shirya, sai sun nemi hanyar dakushe wannan shirin da suke yi. Sai dai idan sune suka shirya masu, tun da su ba su da hankali a yadda su suke tsammani.

Sai dai idan ana nufin cewa tasku din ta fuskar ana kokarin a nuna wa matan (kamar wadanda ba su yarda da addini ba) cewa su zama dadai da maza a komai, suna da ‘yancinsu da dai sauransu. Da gaske ne suna da ‘yanci, Allah ya ba su. Amma ‘yancin bai mai da su maza ba. Amma akwai masu kokarin su ce da ‘yanci sai su yi abin da maza suke yi. Kamar misali sai ka ga mace ta je tana aikin da namiji ne ya kamata ya je ya yi. Ko ta je tana gini ko aikin dan sanda, tana ba da hannu a kan titi da dai sauransu. Aikin da in mutum ya duba da kyau ba ci gaba ne gare ta ba, ci baya ne gare ta a ce tana yin irin wannan. Don akwai abin da yake ya dace da mutuncinta a matsayinta na mace, amma sai suna kokarin kamar su nuna wannan daidai ne suke da maza, a Turance “they are uniform.” Wato duk daya suke ba wani bambanci, wato kamar dai mace ta zama namiji kawai.

To wannan za a iya cewa tana cikin wani irin halin kaka-nikayi, ta fuskar cewa in ma ka duba za ka ga da can su maza, kamar a Turai, suna sa gajerun wanduna ne a irin al’adarsu, to a lokacin mata suna sa dogayen kaya ne har ya rinka jan kasa, har da wani dan hula ko dan kwali wanda suke sa wa a kansu. Amma yanzu wai don sun ci gaba sai aka sa su suka daga kayansu, suka komo da shi ko gwiwa bai kai ba. Sai ya zama maza suka sa nasu har kasa. Wai kuma kokarin da suke yi suna kokarin su nuna daidai da maza suke. In daidai da maza suke, to ai sai su rufe kamar yadda mazan ma suke rufewa. Ana amfani da mata wajen cimma manufofi irin tasu.

To sai dai ta fuskar mata bayin Allah, wanda Allah ya fahimtar da su addini to suna fuskantar danniya wani lokaci ta wajen wadansu maza da suke da rikakken ra’ayi, na rashin mutunta mata. Su suna ganin mace ba ta isa ta shirya komai ba. In wani abu ne sai dai a gaya mata, alhali wannan wani guggubin abu ne da suka fito da daga jahiliyya, sai su shigo da shi, su yi amfani da shi a cikin Musulunci, alhali ba haka nan bane. To wannan zai iya sa wadannan matan da suke cikin jahiliyya ba za su yi sha’awar shigowa ba don su za su rinka ganin cewa mu nan danne mu ake yi tunda za su ga an ce ba ka da ra’ayin kanka, ba za ka iya shirya wani abu ba. Wato ina fadin wannan ne don ya zama an taba ta kowane gefe. Don a gane cewa kar a dauka wai matan da suke gwagwarmaya ba su da matsala, lallai suna da matsala don akwai maza ne masu gurbataccen ra’ayi wadanda suka dauko daga jahiliyya, kuma suna aiki da shi a kan mata din.

MUJAHIDA:Malama tunda kina da irin ra’ayin cewa mata ba daidai suke da maza ba, ba kamar yadda wasu ‘yan uwanki mata ke kirarin kan cewa da harshen Turanci “what man can do surely woman can do better” wane irin kira ko shawara za ki yi a gare su?

MALAMA:Abin da zan ce masu shi ne su gane mu dai a Musulunci Allah ya ba mu ‘yancinmu, ya nuna mana muna da mutunci. Kuma in ka duba da kyau za ka ga mace ma idan ma da wani abin da za ta yi tunani shi ne an ba ta daraja sosai mai yawa. Ba addini ne ya hana ta daraja ba, addini ya ma ba ta darajarta ne.

Wadannan masu kokarin cewa su daidai suke da maza, don haka za su rinka wulakanta kansu suna aikin da namiji ne ya kamata a ce yake yi, don aikin ko ya cika wahala, ko bai ma kamata ba. Idan namiji ne ke yi za a rika ganin sa da mutunci, amma in mace za ta je ta yi zai zama mutuncinta ya zube, to masu kokarin su fuskantar da su ga wannan suna yi ne don cimma tasu manufa din. Suna neman arhar aiki ne, ba wai da gaske suke yi ba. Su kansu ko a zuciyarsu suna ganin ba dadai suke ba. Sun san irin ginin da Allah ya yi mata na jikinta, ba ta da karfin da namiji yake da shi. Amma dai su suna son su yi amfani da ita ne don su samu isasshen kwadago watakila ma mai arha sosai. Don haka ya kamata kar su yarda da wannan.

Su kuma wadanda suke yin addinin wasu halayensu ne yake karfafa gwiwowin irin wadancan matan. Domin in sun zo a kan nuna masu wani irin hali kamar su dabbobi ne. Alhali ba addini ya ce ba. To su wadancan matan su gane ba fa addini ne ya ce haka nan ba. Wadannan suna bin son ransu ne kawai, don haka su abin da ya kamata shi ne su nemi ilimi, su karanci addini su gane wane matsayi Allah ya ba su, sai su yi aiki a matsayin da Allah ya ba su da kuma irin darajar da Allah ya ba su, ba su yi kokarin su zama maza ba.

MUJAHIDA:A cikin wadanda suke da wancan ra’ayin akwai kungiyoyin mata misali kamar WRAPA, NCWC da WIN da makamantansu da suke ganin cewa lokaci ya yi da ku mata za ku tashi ku kwatar wa kanku ‘yanci ta fuskacin siyasa, a rika dama wa da ku, yaya kike ganin irin wadannan kiraye-kirayen da suke yi?

MALAMA:Ta yiwu su abin da suka fahimta kenan, amma kamar yadda ka ce ta fuskacin ma siyasa, ka ga kamar siyasar wannan kasar ai ka ga gurbatacciyar siyasa ce da aka daura a kan ba a yarda da Allah ba. Kodayake yanzun sun fara kokarin cewa Allah a baki, amma a aikace ba su dauki Allah shi ke da iko a kan komai ba. Su suna ganin sune suka fi iko a kan yadda za su tafiyar da rayuwarsu, su alhali mu ba mu yarda da wannan ba.

Don haka idan mace tana son ta tashi ta nemi ‘yancinta, eh da gaske ne kada mata su yarda a danne su, su tashi su yi abubuwan da ya kamata su yi, amma ba ta fuskacin jahiliyya ba. Ba ta fuskacin wai su je su shiga wannan kwamacalar siyasar da ake yi ba. A’a su tashi su yi addini, don ba shakka kamar gwagwarmayar nan da muke kokarin yi, da kuma tunkude jahiliyya da kuma kafa Musulunci ba zai taba yiwuwa ba sai da mata. An ce idan al’umma ta lalace ku dubi Malamai ku dubi mata. Malamai sune suka zama makwadaita suna gwamutsan masu mulki, mata kuma ba sa tarbiyyar yaransu, kuma su kansu ba su ma san hakkin kansu ba.

To ka ga abin da ke gurbata al’umma shi ne da mata da miyagun Malamai. A nan ya kamata a ce su matan su tashi su yi gwagwarmaya amma ba ta fuskar wannan kwamacalar siyasa ba. Lallai siyasa yana daga cikin addini, amma ba irin wannan siyasar ba. Su yi na Musulunci, kuma su ba da nasu gudummawan kamar yadda mata na farko suka yi abubuwa a cikin addinin nan ba su yi shiru ba.

To haka ya kamata su tashi su yi, amma a matsayinsu na bayin Allah na gargaru, ba wadanda za su yi suna kwatan ‘yanci ta wani fuska ba a sarari, alhali a zahiri kana dada bautar da kanka ne ga wadansu, tunda kana yin abin da suke son su ga kana yi. Kamar maza. suna son su ga kin bayyana jikinki, in ma albashi kike samu ki je ki kashe shi a kan kayan shafe-shafe, ba don komai ba sai don ki burge maza. To ka ga kana nan kana bautar su ne. Kai wai kana kwatar ‘yanci, amma kuma a lokacin guda kana bautan ne. Dole ne su fahimci wannan. Musulunci ne kawai zai iya ba su ‘yancinsu na gaskiya ba wai jahiliyya ba.

MUJAHIDAH:Har ila yau Malama tun bayan da aka yi taron mata na duniya, Bejieng Conference, daya daga cikin abin da mata suka fi korafi shi ne dangane da yadda mata suke tagayyara ko kuma irin halin da mata suke shiga a yanayin yaki da kuma yara kanana, to idan muka dubi al’amuran da suka faru a ‘yan watannin da suka wuce a nan Kaduna alal hakika mata na daya daga cikin wadanda suka fi tagayyara dangane da irin rashin mazajensu da sauran abubuwan da aka yi masu, a nan laifin wa kike gani? Shin wai mazan ne ba su san darajar mata bane ko kuwa menene?

To wannan tambayar ban san yadda zan yi in bayar da amsar ta ba. Abin da za ka lura shi ne al’ummar gaba daya ta gurbace, ba mu da ingantacciyar al’umma. A nan wajen za a iya cewa irin tsarin da ake zaune a ciki duk shi ya jawo wannan. Da a ce tsari ne na addini, to abin da ma ya faru ba ma zai faru ba. Kamar misalin na Kaduna da kake magana da ma bai faru ba da a ce tsarin addini ne, ballantana ma a samu wani abu wanda zai kai ga irin wannan tagayyarar. Kuma ko da ma a wajen yaki ne, to ka ga ai akwai dokokin da aka shimfida, wadanda yake Allah ne ya shimfida su na yadda za a yi yaki din da yadda za a yi da jama’a, ko da ma matan kafirai ne, da yara da tsoffaffi da sauransu. Ka gani, to kasantuwar dai irin al’ummar da ake ciki shi ne. Kamar gini ne a kan rubabben fandisho.

Baya ga haka, mun san tarihi ya nuna mana a kowace gwagwarmaya da ake yi, akan samu mata da suke sadaukar da rayukansu dangane da ci gaban wannan gwagwarmaya, musamman ma gwagwarmaya irin ta addinin Musulunci, alal hakika mata da dama sun shiga wani irin hali ta fuskacin jami’an tsaro, cikin ikon Allah ke ma kina daya daga cikin wadanda suka shiga, kasancewar yanzu Mujahidah ta dawo, ko za ki iya bayyana wa mai karatu irin dadda kuka samu kanku a wancan lokaci?

Abin da kawai zan ce shi ne dama idan ana gwagwarmaya ta addini abin da tarihi ya nuna mata sun ma fi shan wahala, don irin halittar da Allah ya yi masu. Kuma wani abu game da su shi ne idan suka karbi gaskiya, kai ko ma karya suka karba, suna yi ne da zuciya daya. Sannan kuma kasantuwar misali su ba za su iya bad da kama ba, dole hijabin nan dai za su sa, da sauransu, ya sa dai ko da ma wani bad da kama ne zai yi masu wuya. To irin wannan ma ya sa sun shiga halin kunci. To da ma abin da muka sani ne. Shi gwagwarmaya a tafarkin ganin addinin Allah ya tabbata tun farko da ma haka yake da wahalhalu. Idan ma ba ka ga wadannan wahalhalun ba dole ka kasance cikin damuwa.

Ni na ma fi damuwa a irin halin da muke ciki, musamman idan ba abin da yake faruwa. Idan abubuwa na faruwa hankalinka ya fi kwanciya, tunda ko da ma a ce kama ka aka yi, ko kana tsare ka fi samun kwanciyar hankali ka san cewa kana kan hanyar wadanda suka gabace ka ne. Wadanda yake kana jin labarinsu, kana sha’awar abubuwan da suka yi, kai ma kana fatan ka yi koyi da abin da suka yi. Dama ba ka sanin me za ka yi sai abu ya faru. To a bin yi shi ne a yi ta yi wa mutane nasiha su rika juriya.

Mu dai mu yi ta rokon Allah ya ba mu juriya. Amma sai mutum ya shiga wani irin hali sannan zai san wane irin mataki zai dauka. Kuma a lokacin ne Allah zai taimake shi gwargwadon yadda ka dauki abin. Sai Allah ya taimake ka ya sa kila daga waje ana ganin kai kana cikin wahala ne, amma kai kana cikin kwanciyar hankali. Idan irin wannan ta faru mutum sai dai ya roki Allah ya ba shi dauriya ya jure don abin zai zo ya wuce.

Sannan akwai wani korafi da maza ke yi na cewa lalacewar tarbiyyar yara ya ta’allaka ne ga ku mata, musamman ma yadda kuke barin su suna zuwa talla da sauransu. Anya haka abin yake kuwa?

Ga wadanda ke barin yaransu suna talla ko? Ba na jin akwai sista ko burazan da suke barin yaransu? Abin da ya fi muhimmanci shi ne ka ba yaranka tarbiyya ta gari. Kuma shi ne kawai abin da za ka iya yi masu. Idan muka duba da kyau, za mu ga akwai wani abin da iyayenmu suka yi mana wanda muka fi jin dadin sa, kuma muna tare da shi, kuma za mu mutu da shi, kuma ko mun mutu ma tasirinsa zai kasance yana tare da ‘ya’yanmu da kuma wadansu shi ne ilimi. Ilimi shi ne babban abin da ya kamata a ba yara. Kuma lallai a nan ina son in yi kira ga ‘yan uwanmu, maza da mata kada su yi wasa da ilimantar da yaransu, da ilimin boko da wanda ba na boko ba, watau ilimin addini. Don mutum ma ba zai fahimci ilimin addinin sosai ba sai ya gane ilimin boko din tunda a cikin wannan zamanin muke ciki. Idan kanka yana cikin duhu kai ba ka san komai ba yaya za a yi ka iya gane addininka da irin wannan lokacin da muke ciki.

Ka ga a irin wannan ne ma kila in yaran sun tashi, in mata ne ba su san hakkinsu ba, a je ana ta zaluntar su, su kuma su yi ta cewa yaya muka iya? In ma suka samu miji dan tawaye ko kuma dan jahiliyya sai su yi ta bin sa, don suna ganin komai sai yadda ya murda su. Da a ce suna da ilimi, wannan ilimin zai taimake su su sami fahimtar kansu, ba wani zai juya su yadda ya ga dama ba. Zai zama suna da fahimtar kansu. Don haka kiran da zan yi wa ‘yan uwanmu maza da mata da kuma mutane haka gaba daya shi ne cewa lailai ilimin yara yana da muhimmanci kwarai da gaske. Sai dai wajen ilimi din yana da kyau mu tabbatar yaranmu sun tsare ka’idojin addini wajen yin ilimi din. Kar ka ce don an ce ilimi yana da kyau har da na boko din ma sai ka je da su ko da ma za a saba wa dokokin Allah din, kamar yara da suka isa sa hijabi a ce ba su sa ba. Sai ka nemi inda za su iya sa hijabi din. Ilimin nan yana da mahimmanci.

Abin da za mu lura shi ne idan ba mu ilimantar da yaranmu ba, idan ma muka takaita iliminsu a kan ilimin addini ba su san ilimin boko ba, to mu sani idan addini ya tabbata wadannan da suke sukar mu, suna cewa abin da muke yi shirme ne don su suna ilimin boko, to sune za su zo su tafiyar da Musulunci din.

Kuma tunda su ba su da sadaukar da kai ga wannan ra’ayin gwagwarmaya tun farko, zai zama kamar suna cin gajiyar an tunbuke tsarin, sun sami wasu mukamai sun rirrike. Kuma wannan zai sa cikin sauki za su iya sai da mu ga Amerika da abokan gaban Musulunci. Cikin sauki wannan gwagwarmaya din zai fadi. Amma da a ce mun ilimantar da yaranmu, in likitoci ne sune, in injiniyoyi ne sune, kowane fanni sun sani, addini ma in an tabe su ba inda ba su sani ba, ka ga wannan zai sa ba mu da bukata zuwa ga munafukai su tafiyar mana. Tunda yanzu in kana dan gwagwarmaya za a ba ka fidan mutum ka yi? Ka je ka yi aikin likita? Ko kuma in muna son a zana mana gini sai mu samu wanda ba masanin ilmin zane bane, dan gwagwarmaya ne kawai, kila shi Amir din wani gari ne, mu ce ya zana mana? Ka ga shirme zai zana mana. Idan kuma aka ba shi mutum zai kashe shi ne tunda shi ba likita bane.

Amma ka ga yaranmu idan aka yi masu tarbiyya ta gari, mu din ma a cikinmu wadanda suke ganin zai yiwu masu su kara yin karatun, to su yi ta yadda zai zama muna da kwararru a kowane fanni. Kuma kwararrun masu sanin addini, ka ga wannan na nufin za mu samu lafiyayyiyar al’umma nan gaba kenan. Saboda haka bai kamata ya zama ko da cikin ‘yan uwa mu rika sakaci da ilimin yaranmu ba, ballantana kuma su tura su talla, tunda shi ne babban abin da za ka bar ma yaranka. Idan ka mutu ma wannan abin bai mutu ba. Idan ko ka bar musu kudi a rana daya ma kudin zai iya karewa ko wata dukiya.

MUJAHIDA:Har ila yau dai akwai wadansu masu kiraye-kirayen cewa lokaci ya yi da ku mata za ku tashi ku hada kanku, kamar yadda aka sami kungiyoyin FOMWAN da MSO da sauran su domin ku sami ci gaba, yaya kina da irin wannan ra’ayin?

MALAMA:Kana nufin a cikin gwagwarmaya a kafa wata kungiya?

MUJAHIDA:A’a gaba daya al’ummar musulmi.

MALAMA:To ai akwai kungiyoyin da suka kakkafa. Kuma wadansu suna bayarwa ta inda suka fahimta. Ka ga kamar FOMWAN da ka ce su suna nasu abin da suka ga za su iya ba, a irin nasu yanayin suna kokari. Sai su ci gaba Allah ya taimaka. Ka ga kamar FOMWAN kungiya ce ta Musulunci kuma suna irin nasu kokarin. Ina kuma fatan su kansu za su ga kansu a matsayin bangaren ‘yan gwagwarmayar Musulunci, suna ba da gudummawarsu, ba wai su zama suna sukan gwagwarmaya ba, tunda su abin da za su iya yi kenan. Su yi Allah ya taimaka. Ka ga idan da za a samu irin wadannan tunda yawancinsu ‘yan boko ne, kuma su suna ganin addini dole shi ne zai tafiyar da rayuwar, sannan kuma suna ganin ga irin gudummawar da za su iya bayarwa a zuciyarsu, suna tare da ‘yan uwa, suna ma yi masu addu’a. suna kuma yi masu taimakon da za su iya yi, ka ga yana da kyau haka nan. Amma ka ga ba za a iya kwatanta su da kamar Jam’iyyar matan Arewa ba wadanda yake a ciki su za ka sami mata kala-kala ne da ba addini ne ya dame su ba. Saboda haka ya danganta da yadda kungiyoyin suke.

Amma ka ga mu ‘yan uwa mata na cikin gwagwarmaya ba ma bukatar mu shirya wata kungiya daban, tunda tuni muna da shugabanmu da tsari. Abin da ya rage kawai shi ne a ce mata, sistas musamman su gane cewa ba zama za su yi su rinka jirin maza su shirya masu abubuwa ba. Su ma su rinka shirya abubuwan da kansu. Don wannan zai nuna cewa sun gane abin da suke yi, ba wai mazajensu ne ke dankara masu ra’ayi ba. Tunda wannan ya kamata a ce ka fahimci abin da kake yi, ba wai don wani yana yi ba. Ka ga kamar waki’o’in nan da suka faru idan aka sami sistan da ba ta da fahimta, ita dai kawai tana bin mijinta ne, to idan ‘yan sandan suka zo ba za ta ce na tuba ku yafe mu, idan ta ji wahala, ko ba haka nan ba? Ko kuma ta dauka hijabi ta wurgar. Tana ganin sun zo yaya za ta yi, amma idan mutum yana da fahimtan kansa ne, to ko da mijinta an kashe shi kana nan kana kan gwagwarmaya, ko da kama shi aka yi wannan ba zai shafe ka ba. Shi ne abin da zan ce.

MUJAHIDA:Wai shin wacece musulma saliha?

MALAMA:Da ma Allah Ta’ala ya aiko da Manzo (saw) ya kuma aiko shi da addini. Addinin nan kuma ya aiko wa kowa da kowa ne, ba maza ne kawai ko mata ba. Don haka duk wanda ya bi addinin da Manzon Allah ya kawo mana, ko in ce duk wacce ta bi addinin da Manzon Allah ya zo mana da shi, ta yi kokari ta yi koyi da Manzon Allah (saw), ta yi biyayya ga Alkur’ani da misalin da Manzon Allah ya zo da mana ka gani ita ce saliha. Don haka ka ga ba wani bambanci kamar yadda za a ce salihi, to haka ma saliha din. Salihi wanda ya bi abin da Allah ya kawo da Manzonsa, haka Saliha ita ce wacce ta bi Allah da Manzon Allah a cikin komai na rayuwarta.

MUJAHIDA:Malama bincike ya nuna akwai wasu mata wadanda ba wannan harka suke yi ba, amma suna da sha’awar harkar, sai dai kasancewar mazajensu ba ‘yan gwagwarmaya ba, ba sa iya shigowa a yi da su, to a nan wace shawara za ki ba su?

MALAMA:To, ni shawarar da zan ba su ita ce ita harka, in dai mutum musulmi ne kuma ya yarda da Allah ya kuma yarda da Manzon Allah (saw), to ya kamata ya gane cewa larura ce gare shi a ce yana tafiyar da rayuwarsa kamar yadda Allah ya ce. Kuma kasantuwar muna cikin al’umma gurbatacciya wadda ba ta yarda da cewa Allah ne zai tafiyar da rayuwarmu ba shi ya maishe da harkar ta zama tilas a kanmu, maza da mata. Kuma mutum ya sani in ya je lahira, “Yauma yufirrul mar’i min akhihi wa ummihi wa abih, wa sahibatihi wabanih. Likulli imri’in yauma izin sha’anih yugnih.” To ka gani a ran nan kowa yana ta kansa ne. Idan ma aka ce za ka guje wa mamanka da babanka ka ga miji a duniyar nan ta yiwu ma ya sake ka. To amma fa babanka ko me ka yi masa, ko ya ce ba ruwansa da ke kina nan dai a ‘yarsa ko kana nan a dansa. Ba zai taba cewa ba shi ne ya haife ka ba, ko ya maishe shi ba shi ya haife ka ba. To ko su ma an ce a ranar lahira kowa yana ta kansa.

Don haka abin da ya kamata shi ne mutum ya dage, ko dama mijinki ba shi da ra’ayi, a lahira ba zai taimake ki da komai ba, kuma ko a duniyar nan yana iya rabuwa da ke. To abin da ya kamata shi ne ke ki dage ki ba da naki irin gudummawa din. Ki dage ki yi gwagwarmaya din don ita ce mafita a gare mu. Don zama a cikin irin wannan tsarin da muke ciki in muka koma ga Allah ba mu da abin da za mu ce wa Allah. Idan mutum yana zaune a irin wannan tsarin na jahiliyya, kuma ba wai kana kokarin ka yi gwagwarmaya na ganin cewa addinin Allah ya tabbatab, to ba ka da hujjar da za ka ba Allah. Kuma ki tuna wannan mijin nan naki ba zai taimake ki ba ranar lahira. Ba zai kubutar da ke ba. Kamar yadda Allah (T) yake cewa “Al akhilla’u yauma izin ba’aduhum liba’adin aduw.” Wadanda yake su aminan juna ne a duniyar nan za su zama abokan gaba da lahira, ba don komai ba sai don a duniyar nan sun yi amintakarsu ne a kan sabon Allah, shi ya sa a ran nan za su zama abokanen gaba. Wadanda kawai za su yi farin ciki da ganin juna sune wadanda suka rayu a kan bauta ga Allah da kuma biyayya ga Allah. Don haka idan mutum ya tuna da irin wadannan zai ga cewa ba abin da zai hana shi ya bi Allah a duniyar nan. Ko miji ne ko iyaye ko wani abu.

Kamar yadda in namiji yana da fahimta ba zai ce yana jiran matarsa sai ta fahimta sannan ya yi addini ba, to haka ma mace in kina da fahimta sai ki yi. Dagewarki zai sa shi ma ya fahimci gaskiya shi ma ya zo ya yi. Ba wai ka biye masa ba.

MUJAHIDA:Wane irin hobbasa kuke yi dangane da kira ko kuma tablig, musamman ga ‘yan uwa mata da suke Jami’a da kuma ma na kauye kai har da ma wadanda ba su musulunta ba irin Maguzawa.

MALAMA:Ta fuskacin kamar ‘yan uwa da suke Jami’a musulmi, akwai harkoki da ake yi, ko a Jami’a din ma akwai ‘yan uwa wadanda suke gabatar da tarurruka don jawo hankalin irin wadannan ‘yan uwa. Sannan kuma irin tarurrukan da ake shiryawa, kuma mukan gayyaci wadansu daga Jami’a din da kuma wadansu makarantu su zo irin wadannan tarurruka din. Kuma nan gaba ma za mu kara kaimi a kan haka nan. Ya zama ana yin abubuwan fiye da haka nan. Dama abin da ya sa ya zama haka shirin jahiliyya ne, tun farko ka san wannan harkar an fara ne a Jami’a, to sai da suka san hanyar da suka yi, ta kora da sauran abubuwan suna ta cire mutane daga Jami’a, amma wannan bai hana wadanda ke da fahimta ya zama sun samu fahimtar ba, amma lallai ana fuskantar matsaloli. Amma duk da haka ana kokarin yadda za a yi.

Ta kuma fuskacin matan gari akwai shirye-shirye da mata da maza suke yi don su ga cewa sakon ya kai gare su, to haka ma abin da ya shafi mutanen da suke kauye. To amma abin da ya shafi Maguzawa ban san wani kokari da muke yi ta wannan gefen ba. Ban san ko akwai ‘yan uwa da suke yi ba. Muna da sha’awar wadan da ba musulmi ba su shiga Musulunci, to amma matsalar ita ce wane Musulunci za su shiga? Wane samfuri ko misali za a nuna masu? Kana hangen abin da nake fadi? Abin da muka fi bai wa muhimmanci shi ne ‘yan uwanmu musulmi. Wato mu siffantu da addini tukuna don in mun kira wadansu su za su zo su ga abin da muke son su yi ne. Amma yanzu idan ka ce wa mutum ya musulunta kila ma in dan makaranta ne ko kuma yana da makwabci sunansa Yahaya kila zai ga ba wani bambanci. Bambancin kawai shi ne shi sunansa Yahya, wancan John, amma in neman mata ne tare suke yi, in shan giya ne tare suke yi, idan fasadi ne kala-kala duk tare suke yi. Ka ga ba wani bambanci. Ya kamata a ce in ka kira mutum ya kamata a ce ya san me kake kiran sa a kai, shi ya sa ma a hakikanin gaskiya musulman kasar nan suna yin sabo biyu ne. Sabonsu na farko shi ne ba sa bin Allah, ba sa tafiyar da rayuwarsu yadda Allah ya ce. Sannan kuma na biyu a sanadiyyar rashin gudanar da rayuwarsu a yadda Allah ya ce suna hana wadanda ba musulmi ba su yi sha’awar Musulunci, tunda su ba su ga wannan Musulunci da ake kiran su gare shi ba. Wannan babban laifi ne. To ya kamata mu kanmu mu siffantu da Musulunci sannan mu kira mutane ga Musulunci din, don idan suka zo sai su ga menene muke kiran su gare shi. Ta yiwu kila ba ma sai mun kirawo su ba, kamar yadda aka ce abin da kake aikatawa ya ma fi muhimmanci a kan abin da kake fada. Tunda aikinki ne wani lokaci zai sa wata ta yi maki tambaya ta ce ashe haka Musulunci yake? Daga nan sai ki sami damar yi mata wa’azi.

MUJAHIDA:Wane kira kike da shi ga ‘yan uwa maza?

MALAMA:A hakikanin gaskiya za mu iya samun nasara ko da ba su bayar da hadin kai ba, amma in sun bayar ya fi kyau. Wadansu suna kawo mana cikas sosai, tunda ko wata harka aka shirya in dai ba su ne suka shirya ba, su suna ganin…. Amma akwai wadanda suke ‘yan kirki ne suna ma taimaka wa a kan abubuwan da muke yi, a gaskiya wasu shirye-shiryen ma da muke yi ba wanda ba buraza a ciki suna taimaka mana da shirye-shirye. Akwai wadanda ma suna farin ciki ‘yan uwa mata suna shirya harkokinsu, don haka ma suna taimakon mu sosai.

Amma akwai wadanda suke da gurbatacciyar zuciya, ka ga irin wadannan ba za su iya kawo mana wani cikas ba, tunda ba abin da za su iya hanawa wanda Allah ya yi nufin za a yi. Ba shakka wadansunsu suna da wani tasiri a kan wasu mutane, don haka sukan yi kokari su gurbata zukatan mutane da tunaninsu, ko kuma su canza bayanai, kamar misali idan mun ce rana kaza, sai su ce an ma fasa, irin haka nan.

To, wani kila jahilcinsa ne yake damun sa, wani kuma kila ma an turo shi ne ya zo ya hargitsa harka. Ko da ma an turo mutum ya zo ya hargitsa harka, to abin tunda ba siyasa bane, ba yaudara bane, addini ne, kuma Allah ne yake da addinin kuma yana taimakon masu taimakon sa, ka ga Allah ya san ko ma wace irin yaudara mutum yake kirkirowa. Kuma shi ya san yadda zai yi ya tarwatsa shi. Don haka ko da mutum ya kawo cikas ba lallai ne ya shafe mu ba. Kamar yadda Allah yake cewa “Kada Manzon Allah da sahabbansa su yi bakin ciki kan abin da munafukai suke yi, ba za su iya cutar da su da komai ba. Ka ga wani shi jahilcinsa ne tun a jahiliyyarsa haka yake, wani kuma munafunci ne yake damun shi, shi yana ganin lallai idan mata suka samu ci gaba, addinin nan zai samu ci gaba, don haka bari ya dakushe kokarinsu, a fakaice shi yana dan uwa, amma yana dakushe kokarin mata. Wani kuma shi dai kawai yana fama da jahilcinsa ne don shi yana ganin bai kamata a ce mace ta shirya abu ba; ita ya kamata ta zauna a gida ta yi ta zuba ‘ya’ya, tana aikace-aikace kamar mai hidima a cikin gida. Shi abin da ya gane kenan.

Abin da kawai zan ce shi ne wanda yake shi gaskiya ya dauka mace bai kamata ta yi ba, to ya gane wannan Harka din kowa ya zo ne ya karbi kiran Malam don yana jin tsoron azabar Allah. Yana neman tsira daga azabar Allah, yana son Allah ya sa shi cikin rahmarsa. Kuma kada a manta mun yi wa azzalumai masu bindigogi ne tawaye, ka ga azzalumi mara bindiga ya kamata ya gane in dai har za ka tsaya ka ce mai bindiga ya zo ya harbe ka, ka ga mara bindiga idan ma ba ka ce masa komai ba, kana raga masa ne, don haka bai kamata mara bindiga ya zo ya yi maka barazana ba. Don abin da yake faruwa kenan a wasu wurare. Sai ka ga mutum ya ce shi dan uwa ne, amma sai ya rika kawo cikas a harkoki na addini. Ya rinka ganin kamar zai iya tankwara mutane. Kada ya manta wadannan taron ‘yan uwa maza da mata din nan taron mutane ne wadanda suka yi wa azzalumai masu bindiga da abin da ya wuce bindigogi tawaye. Ka ga irin wadannan bai kamata kai ka rinka ganin za ka iya murkushe su da irin naka zaluncin na rashin bindiga ba.

Wannan babbar matsala ce wadda yake in ba an magance ta ba, lallai zai iya kawo baraka, tunda abubuwa ne da ke faruwa. Ba ga sistas kawai ba ba yana faruwa ma ga maza. Za ka ga wata da’ira wanda yake da an bar ‘yan uwa da irin kokarin da Allah ya ba su akwai abubuwan da za su iya kirkirowa da zai amfani wannan harka gaba daya, amma don mutum ana ganin shi ba Amir bane, ko bai da wani mukami, ko kuma shi ba wani abu bane, sai a nemi a dakushe shi. In ya shirya abu sai a ce shi wanene da zai shirya abu? Ba kowa yake yin wannan ba, amma akwai masu yin haka nan. Kuma lallai suna kawo cikas sosai.

Don haka gara ma mutum ya gane. Idan ana raga masu ana yin haka ne saboda hadin kai ba don komai ba. Ya kamata mutum ya sani in dai za ka yi wa mai bindiga da bama-bamai da tankoki tawaye, ya fito da tankinsa ka bude kirjinka ka ce ya harba, ka ga mara bindiga ba yadda za a yi ya zo ya yi maka barazana. Da menene zai yi maka barazana? Ba shi fa da bindiga. Ko in karfi ne kai ma kana da shi misali.

To ka ga irin wadannan ya kamata su san ana dan raga masu ne, ba yana nufin za su iya ci gaba da dakushe mutane ba. Idan mutum yana yi da ikhilasi to ya sani ba wai kama-karya ake yi ba. Tunda Malam ma yana karfafa mu ne mu rinka yin abubuwa da kanmu. Na san ko shirye-shiryen taro ne idan muka ce ya ba mu shawara, sai ya ce ku je ku yi alabashi idan da wani kuskure a gyara mana. Shi ya fi so mu rika yi da kanmu ne. Haka nan yakan yi ta nuna mana, shi ya sa har muka zo muna yi da kanmu. Da a ce ko menene muka yi sai ya ce ku a su wa da kuka shirya wannan abin? Da yanzu ba mu iya shirya komai ba, kullum muna jiran ya ce mana ka ga abin da za ku yi.

Ka ga kenan idan an kama shi sai mu jira, sai ya fito. Kenan komai sai ya tsaya. Ka ga ‘yan uwa maza yanzun, ko yana nan ko an kama shi suna yin harkokinsu. Ka ga yana da kyau a ce haka nan kowa ya dauki wannan misalin. Ga shi shi wani ne da ake girmama shi, kuma mutane suna son sa, kuma idan ya fada ‘yan uwa za su ji, idan ya ce kada a yi kaza za su ji. Ka ga bai yi mana kama-karya ba. Ka ga bai kamata mu da muke cewa muna biyayya gare shi mu rika yi wa ‘yan uwanmu kama-karya ba. Idan mutum ya yi abu a dakushe masa kokarinsa. A ce shi ne wane da zai shirya wani abu? Ina son in dauki wannan dama in yi wa ‘yan uwa masu irin wannan matsala nasiha. Kuma wadanda dama suna yi ne don munafunci, to su ci gaba da yi, tunda dai Allah yana kallon su, kuma shi ya san yadda zai yi da su.

MUJAHIDA:Mujallar Mujahida mujalla ce taku ta mata, kuma ana so mata su rika ba da gudummawa mafi yawa a ciki, to menene shawararki a nan?

MALAMA:Shawarar da zan bayar ita ce yana da kyau ‘yan uwa mata su ba kyakkyawan misali, wajen ba da gudummawa ta rubuce-rubuce da sauran abubuwa. Sannan kuma idan mace za ta yi rubutu, ko wani zai yi rubuta, to kada ki yi amfani da abin da aka koya maki wanda kika dauka shi ne addini ki yi kokari ki binciki menene kike rubutawa. Don na tuna wancan karon da aka yi Mujahida, sai aka sa wata, har ma mun hadu da ita mun yi magana, kuma ta yi nadamar abin da ta aikata, sai ta rubuta abubuwa goma da wani mata za su yi wa mazajensu. Haba aka yi ta talla. Da ta zo da abubuwa goma din kawai dai ga su nan ne. Sai na ce mata ya kamata ta yi adalci. Misali a abubuwan da ta sa sai ta sa abubuwan da suke al’ada ne ba Musulunci bane. Ya kamata mu bambanta Musulunci da al’ada. Misali ta yi batun abinci, wai ta rinka tabbatar da ta gama abinci a lokaci, al’ada ne wannan, ba inda aka ce wannan, ballantana ta ce wai a tabbatar an gama abinci kan kari. Kuma abubuwan da ta rubuta, ita kanta na tabbata ba za ta iya yin su ba. Misali tana cewa ka tabbatar mijinka bai ji wani hayaniya ba. Na ce to kila ba ki da yara ne, kuma da gaske ne ba ta da yara, ba ta taba haihuwa ba, sai daga baya. Idan kina da yara kuma gidanku takurarre ne, ba dole ya ji hayaniya ba. Akwai abubuwa da ta rubuta wadanda suna dada tabbatar da al’ada, wadda a irin shi ne aka daura aure. Alhali shi Musulunci ba al’ada bane. Kuma Allah ne ya ce a yi.

Don haka yana da kyau idan wata za ta yi rubutu ta san abin da za ta rubuta. Kuma da yake lokacin tawayiyya ne, sai ya zama su a wurinsu wani adawa ne ga masu cewa mace ba baiwa bace. Domin suna nuna wai kamar mu muna bangaren ‘yancin mata ne, alhali ba haka bane mu muna fadin abin da yake gaskiya ne, kuma abin da muka ji Malam yana gaya mana. Kuma abin da ya karanta muka kuma gani a littafi cewa ga matsayin mace. Ka ga ya kamata wadanda za su ba da gudummawa da ku kuma da kuke tacewa da sauran su ku tabbatar in wata ta rubuta irin wannan, ku yi masu gyara. Kuma ya kamata a sami adalci idan an ce yaya mace za ta kyautata wa mijinta, ya kamata a fadi yadda miji zai kyautatawa matarsa. Kuma bai kamata a dauko abin da yake al’ada ne a ce abin da ya kamata ta yi ba kenan. Ko ba ka lura ba?

Ka ga yanzun aure na rabuwa ne a kan abinci ya cika zafi ko ya cika gishiri, ko bai ji gishiri ba, ko kuma ya cika sanyi ko kuma bai yi dadi ba. Alhali ba inda aka ce aikinta ne, amma a kansa abin da aka ce idan aka yi Al’arshi yana motsi, sai ka ga ana yawan yi. Ka ga ya kamata yanzu in za a yi Mujahida ya zama ta tana nuna ra’ayin Musulunci ne da gwagwarmaya, tunda mu muna so ne idan addini ya tabbata ya zama Musulunci ne zai tabbata ba jahiliyya ne ba, ko kuma ko al’ada da sunan Musulunci. Idan zai zama jahiliyya ne ko al’ada ne da sunan Musulunci, to gara ma wannan halin da ake ciki, tunda muna sa ran Musuluncin ya tabbata. Kuma kila ma idan kafiri ya ce ahaf ku ma addinin naku ai haka ake bautar da mata, za mu iya cewa gaskiya ba haka muke addini ba, wadannan dai suna bin son ransu ne.

Amma idan yau muka ce Jamhuriyar Musuluci sai sai suka ga Jahiliyyar ne dai, ka ga menene za mu ce masu? Ka ga ba mu da bakin magana. Don haka zai fi kyau a ce jahiliyyar ne sai mu ce masu, to ai wannan ba Musulunci bane. Ni dai shawaran da zan bayar kenan ga su masu rubutun da kuma ku masu gyara. Kada mutum ya ga abin ya dadada masa rai ya ji an ce matarsa ta rinka bauta masa, sai ya ce lailai wannan shi ne abin rubutu, idan wata ta rubuta irin wannan ana iya yi mata gyara a ce lallai wannan al ada ne, ki gyara rubutunki ba haka nan bane.

MUJAHIDA:Mun gode.

   

Komawa Babban shafinmu