Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 12                                     Jimada Thani 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 12
  Jimada Thani
 DAGA TEBURIN EDITA
Irin Wainar da muka toya
 SHARHIN MUJAHIDAH
A gaida 'yan uwa mata
 WASIKU
Wasiku uku daga 'yan uwa mata
 BABBAN LABARI
Taron Nasarar Hizbullah a Zariya

Hizbullah ba za ta taba daukan kaskanci ba

Dole ne Malamai su hada kansu

Wajibi ne mu zama abin koyi

 HIRA TA MUSAMMAN
Shawara ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a

 LABARI
Lalacewar mata a Nijeriya

 FADAKARWA
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata
 NASIHA
Rayuwar aure a Musulunci

Kishiya Ko Abokiyar Zama?

 YARA
Ka tausaya ma dabbobi
 LIKITA
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda
 TARIHI
Gwarzantakar Ummu Wahab(R.A)
 RAYUWA
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Shirin hana almajirai bara zai yi nasara kuwa?

Hattara 'yayan talakawa

Kikan duba shafin

Almizan
  kuwa?
The Witness
  kuma fa?
Hira ta Musamman
Shawarata ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

In ji Jami'ar Kungiyar dalibai musulmi ta Jami'ar Ahmadu Bello Zariya

Editarmu Hajiya Zainab Adamu, ita ta nemi hira da Amirah ta kungiyar dalibai musulmi da ke Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, Rahama Zakariyya da ke Tsangayar Kimiyya, sashen nazarin kananan halittu (Microbiology), amma sai hakan bai yiwu ba, ta hada ta da Mataimakiyarta, Bint Tahir Imam, wacce ke karatu a sashen kimiyyar magunguna (Pharmaceutical Sciences). Hirar cike take da sahihan bayanai. In kun karanta kwa ji. Bisimillah.

MUJAHIDAH: Yaya kuke gudanar da al'amuran kungiyarku ta MSS?

Bint Imam Muna gudanar da al'amuranmu a wannan 'campus' na Jami'ar Ahmadu Bello Zariya ta hanyar shirya tarurruka da yin azuzuwa na karatuttuka don dalibai musulmi na nan Jami'ar. Sannan kuma muna yada sakonni ko labarai na musulmin wasu wurare. Saboda wasu matsalolin suna aukuwa ne saboda rashin sanin matsayin da Musulunci yake da shi ba ma a wannan kasa tamu ba, amma a wasu wurare. Amma labaran halin da wasu musulmin suke ciki yakan kara kaimi da farfado da kishin wasu musulmin.

MUJAHIDAH: Jami'a kan taimaka muku kan tarurrukan da kuke shiryawa ne?

Bint Imam To gaskiya ya dangantaka, amma a hakikanin gaskiya ba wani taimako da muke samu. Hasali ma wurin da za mu yi tarurrukan, wato zauren taro, sai mun rubuta takardar nema, da kuma rokon a ba mu, sannan a ba mu.

MUJAHIDAH: Wane irin ci gaba kuke samu wajen wayar da kan matan Jami'a?

Bint Imam A gaskiya tunda muka zo, mun tad da matsaloli da yawa a tsakanin musulmi na Jami'a, musamman mata. Akwai jahilcin sanin addinin shi kansa, saboda akwai yara da yawa da suka zo daga wurare daban-daban. Wasu matsalolin ma daga gida suka faro, iyaye ba su ba su tarbiyya ba, ko kuma akwai tarbiyyar amma ba su san menene Musuluncin ba, kuma yaya za su rayu a matsayinsu na musulman kwarai. Tunda in sun zo ba wuri ne da kawai musulmi ne a wurin ba, akwai kiristoci da sauran masu addinai daban-daban, su ma kuma suna kokarin jan mutane gare su, saboda haka irin wadanda ba su tsaya ba sosai a addinin Musulunci za ki ga an ja su. Ko kuma ba su shiga ba, amma a Musuluncin su ba na kwarai bane sosai.

Sannan kuma mun samu matsalar rarrabuwa a tsakanin musulmi. Za ki ga su wadanda suke kokarin dabbaka addini an sami 'gap' a tsakaninsu, ana ganin su a wuraren da ba su dace ba, ko kuma wani lokaci su yi shigar da ba ta dace ba. Da an sami hadin kai duk an zo an zama daya, to da yada addinin ko koya wa sauran abubuwan da ba su sani ba, da zai zo da sauki. Amma sai ki ga muna kokarin jawo su su zo masallaci, ko wani taro, amma sai ki ga ba su zuwa, suna ganin ai wadancan masu saka hijabi ne ba su son ganin mu, saboda suna ganin sun fi mu tsoron Allah saboda suna sa hijabi.

Hatta sallama mun yi kokarin mu ga cewa mun hada kan musulmi ta hanyar yada sallama, saboda Manzo (S) ya fada cewa yada sallama tana yada soyayya tsakanin musulmi. In mun zo masallaci mukan fada cewa duk wanda ya ga wata matsala, ko muna gudanar da al'amura yadda bai kamata ba, to ya yi magana. To amma yawancin koke-koken bai wuce cewa masu hijabi suna daga mana kai, masu hijabi ba su yi mana sallama, in mun yi masu sallama ba sa amsawa, dss. Mu kuma mu ce to ai in mun gan ku ba ma iya bambancewa, musulmin ne ko ba musulmi bane. Saboda haka ana samun irin wannan matsala din.

Za ki ga kin gayyaci mutane zuwa wani shiri, amma ba za su zo ba, ko kuma koyaushe kina da abin da za ki fada wa mutane, amma sai ki ga wadanda suka saba zuwa su za su yi ta zuwa, alhali babban ci gaba shi ne a samu wadanda ba su san komai din ba su zo masallaci a koya masu, amma ba za su zo ba. A nan masallaci akwai ta'alim da muke yi kullum tsakanin magariba da isha'i. Sannan bayan isha'I muna da azuzuwa na musamman da ake koyar da wasu darussan kamar tauhidi, karatun Alkur'ani da Larabci. Da safe bayan sallar asuba akwai ajin Tarbiyyatul aulad, saboda muhimmancin tarbiyyar 'ya'ya a Musulunci, wanda yake nauyi ne na uwa. Mace kuwa wacce take cikin irin wannan muhalli in ba an koya mata yadda za ta yi tarbiyya a musulunce ba, sai ki ga hanya Bature za ta bi, alhali ba ita ce hanyar da ta dace ba.

Ganin irin wadannan matsaloli sai muka shiga yin da'awa daki-daki saboda wadanda ba sa zuwa. Muna zuwa dakuna muna tunatar da 'yan uwa musulmi, kodayake har yanzu ba mu fadada zuwa ga wadanda ba musulmin ba, mun fi mai da hankali a kan musulmi, musamman a lokacin da ba a ba da karfi ba sosai ga karatu.

Mukan kuma shirya walimomi, saboda in ka ce a zo laccar addinin Musulunci ba za su zo ba, amma da kin ce wani dan buki, sai su zo a hadu. To muna bin da'awa din da hikimah. A walimar sai mu nuna masu duk daya ake ba warewa aka yi ba. Mukan shirya gasar karatun Alkur'ani tsakanin Tsangayoyin ilimi na jami'ar ko dakunan kwana. Kuma wannan ya kara kaimin dalibai da dama, saboda yanzu ana samun da yawa suna zuwa koyon karatun Alkur'anin.

Muna kuma koyar da girke-girke da yadda ake tattalin gida, wannan shi ma yana janyo wadanda ba sa son zuwa masallaci. Mace ko ba ta so ta zo ta ji wa'azi, to in ta zo irin wadannan darussa, sai a hadu a dan tattauna.

Sannan 'yan uwanmu mata da suka yi aure mukan yi masu walima, don dai mu dan dada kaimi ga sauran sistas don a yi aure, don shi ma hanya ce ta cikan addini da kare mutunci.

MUJAHIDAH: In za ku yi wadannan shirye-shirye kukan sa wa junanku haraji ne ko kukan nemi taimako daga wasu wurare ne?

Bint Imam Mukan nemi taimako ne kowa ya ba da fisabilillahi. Kowane bene mukan sa mai karbar taimako.

MUJAHIDAH: Kukan nuna masu muhimmancin sa hijabi in an zo tarurruka?

Bint Imam Wannan abin da ake tunatar da su ne a kullum. Da muka zo ma mun samu wannan matsala din, da yake ni ma ban dade da zuwa Jami'ar ba. A gaskiya a san da na zo na tarar da muhallin sai dai mutum ya ce subahanallah. A lokacin mu sabbin zuwa matsalar ta fi shafar mu, saboda wadanda suka zo daga Sakandare suna so su zo ne su yi abin da suka ga dama, su yi sharholiy, hatta masu saka hijabin ma za ki ga sun aje, sun fara irin wadannan abubuwan. Kodayake su ma Jami'an MSS din na baya sun yi kokari wajen jawo hankalin dalibai kan suturar Musulunci da ta dace. Kuma alhamdulillahi mun ga ci gaba sosai, saboda yadda ake samun masu saka suturar da ba ta rufe jiki sun ragu sosai, yanzu ma da kyar za ki samu musulma da za ta fita ba ta rufe jiki ba, amma a da ba ki gane musulma sai dai a suna.

MUJAHIDAH: To yaya rayuwar mace musulma yake a Jami'a?

Bint Imam To a gaskiya saboda tsarin gudanar da jami'ar, wuri ne mai wuyar rayuwa. Saboda ita mace da Allah ya yi ta ya tsara mata yadda za ta yi rayuwarta, inda za ta zauna, wuraren da za ta je, yadda za ta fita, wadanda za ta yi hulda da su, to za ki ga cewa yadda al'amuran suke a Jami'a ya saba wa haka. Saboda za ki je aji, watakila a hada ki da maza ku yi aiki a kan kaza, za a samu wannan cudanya da maza, wanda addinin Musulunci kuma ya hana haka.

Ko kuma in za ku je dakin bincike ba za a bar ki ki sa cikakken hijabi ba, za ki saka rigar dakin bincike, kodayake yanzu muna shiga da hijabin, amma sai kin dage shi yadda ba zai rufe rigar dakin binciken ba. Masu saka 'Nikab', wasu malaman ba su bari, sai kin cire, su ce yaya za a yi a gane ki? Wajen shiga ajin ma ga turereniya a cakudu da maza, haka ma inda za ki zauna, duk ya saba da tsarin addinin Musulunci.

Wannan cakuduwa din da maza ita ce babbar matsalar, ba yadda za ki yi ki yi rayuwarki yadda Musulunci ya tsara sai kin sami matsala. To dama wacce ta san haka sai ta shirya ga yadda wannan wuri yake, bari in shirya wa tafiyar. Saboda haka tun daga gida ya kamata kin zo da niyyar ga yadda za ki zauna.

Da farko dai ya zamana kin zo da ikhlasin neman ilimi, saboda Allah kika zo neman ilimi. To da haka za ki yi kokari a komai naki za ki yi shi yadda Allah ya ce a yi. saboda ba za ki ce za ki yi abu saboda Allah, sannan ki saba wa Allah ba. In kika yi haka ta yaya kike so Allah ya albarkaci wannan abu?

Akwai wadanda suke ganin barin gida wata dama ce suka samu na su kauce wa iyayensu. Wasu suna ganin in a gida suke ba za su yi abin da suka ga dama ba. Don haka da sun zo Jami'a shi ne suke ganin za su saka abin da suke so, su je inda suke so, su rayu yadda suke so su rayu. Saboda haka ba su da wata niyya ta kwarai ta zuwa Jami'ar don haka rayuwar ma ba ta da wani tsari. Amma wacce ta zo da niyya ta kwarai ta riga ta tsara insha Allah za ta hadu da mutanen kirki, wadanda suke da irin tawa niyyar ba mutanen banza ba, za ki yi kokari ki ga cewa ba ki kauce daga hanya ba.

MUJAHIDAH: Wane kira za ki yi wa iyaye wadanda 'ya'yansu ke Jami'a?

Bint Imam Da ma abin ya tattaru a kan yadda yaran suka taso da tarbiyya. Matsalar da aka samu ita ce ta rashin tarbiyya. Su dai sun san mahaifinsu musulmi ne mahaifiyarta musulma ce, kuma an haife ta a gidan Musulunci, shi kenan ita ma musulma ce, an sa mata sunan Musulunci shi kenan. Amma ba za ki iya bambance ta da wadda ba musulma ba. Ita ba ta san cewa wannan laifi ne ba. kai duk wata lalata da za ki sami mace tana yi a Jami'a to a dalilin rashin tarbiyya ne. nauyin yana kan iyaye. Allah (T) ya ba su 'ya'ya amana, to tarbiyyarsu yana wuyansu su ga cewa wadannan 'ya'ya sun taso da su a musulmin kwarai. Shawarar da zan ba iyaye ita ce kafin su turo 'ya'yansu makaranta su san cewa sun ba su tarbiyya ta addinin Musulunci. Yaro ya san cewa ni musulmi ne ba don iyayena musulmi ne ba, a kan kansa ya san dalilin da ya sa yake Musulunci. Ya kamata iyaye su ga cewa suna ba wa 'ya'yansu ilimin, suna kuma ganin cewa 'ya'yan suna dabbakawa, to duk yaron da ya samu wannan fa shi ne zan ce yana da garantin zuwa Jami'a. wato zai iya kiyaye kansa daga dukkan matsalolin da ke tattare da jami'ar.

MUJAHIDAH: Mun gode.

Bint Imam Ni ma na gode.

   

Komawa Babban shafinmu