Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 12                                     Jimada Thani 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 12
  Jimada Thani
 DAGA TEBURIN EDITA
Irin Wainar da muka toya
 SHARHIN MUJAHIDAH
A gaida 'yan uwa mata
 WASIKU
Wasiku uku daga 'yan uwa mata
 BABBAN LABARI
Taron Nasarar Hizbullah a Zariya

Hizbullah ba za ta taba daukan kaskanci ba

Dole ne Malamai su hada kansu

Wajibi ne mu zama abin koyi

 HIRA TA MUSAMMAN
Shawara ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a

 LABARI
Lalacewar mata a Nijeriya

 FADAKARWA
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata
 NASIHA
Rayuwar aure a Musulunci

Kishiya Ko Abokiyar Zama?

 YARA
Ka tausaya ma dabbobi
 LIKITA
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda
 TARIHI
Gwarzantakar Ummu Wahab(R.A)
 RAYUWA
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Shirin hana almajirai bara zai yi nasara kuwa?

Hattara 'yayan talakawa

Kikan duba shafin

Almizan
  kuwa?
The Witness
  kuma fa?
Hira ta Musamman
Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

In ji Amirah ta MSS, Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Kaduna (Kadpoly)

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna shahararriyar makaranta ce, kodayake ba jami'a bace, amma marabarta da jami'ar kadan ce. Shi ya sa Wakiliyarmu da ke kwalejin ta tattauna da Amirah ta MSS, Malama Maryam Abdullahi don jin ta bakinta kan halin da 'yan uwa mata suke ciki a kwalejin.

MUJAHIDAH: Malam yaya sunanki?

Amirah MSS Kadpoly: Yana da muhimmanci?

MUJAHIDAH: Kwarai kuwa!

Amirah MSS Kadpoly: To sunana Maryam Abdullahi.

MUJAHIDAH: A wane aji kike a wannan kwalejin ta kimiyya da fasaha?

Amirah MSS Kadpoly: Ina yin babbar difloma ne a kan kididdigan kudi (accounting).

MUJAHIDAH: Wane matsayi kike da shi a kungiyar MSS ta wannan kwalejin?

Amirah MSS Kadpoly: Matsayin da Allah ya ba ni shi ne na Amirah.

MUJAHIDAH: Ko za ki iya gaya mana irin matsalolin da sistas kan yi fama da shi a wannan Kwalejin?

Amirah MSS Kadpoly: Sistas sukan yi kuka da abokan zamansu a dakuna, saboda wasu sukan yi wanka tsirara a barandar dakunan, musamman wadanda ba musulmi ba, alhali haram ne ga musulmi ya ga tsiraici wani. Wasu kuma abokan zaman da ba musulmi ba sukan dami musulmi in suna yin salloli a daki, suna ganin kamar suna yi masu addu'ar mutuwa ne, musamman sallar dare. Amma alhamdulillahi irin wadannan matsalolin ana shawo kansu. Wata matsalar kuma ita ce wasu musulman saboda karancin iliminsu kiristoci na sa su ridda ko su rinjaye su.

MUJAHIDAH: To wadanne matakai kuke dauka don shawo kan wadannan matsaloli?

Amirah MSS Kadpoly: To da farko dai muna kokarin fadakar da 'yan uwa mata su rika dawowa kwalejin da wuri saboda su sami daki. Domin ta rashin daki ne ake cutar mu. Su kiristoci sukan zo da wuri saboda sun san cewa samun daki a makaranta na da wuya a nan Kadpoly. Kuma mukan shirya da'awa ta daki-daki da kuma kiran su zuwa masallaci su ji wa'azi da dai sauran karantarwa.

MUJAHIDAH: Kun ga alamun nasarorin wadannan kokari da kuke yi kuwa?

Amirah MSS Kadpoly: Alhamdulillahi, haka Allah ya so, don kuwa muna samun nasara, wasu sistas din suna canzawa, kodayake wasu suna ba mu matsalar rashin amsar da'awar. Duk da haka ba mu yi sake ba, muna ta kokari, kuma in Allah ya yarda komai zai yi kyau.

MUJAHIDAH: To ya kika ga dabi'ar 'yan uwa mata a Kwalejin?

Amirah MSS Kadpoly: To wasu dabi'unsu lallai ba kyau saboda tun daga gida ba su zo da tarbiyya mai kyau ba. Dama kuma an ce tarbiyya daga gida take farawa. Kodayake kuma akwai sistas na kwarai.

MUJAHIDAH: Yaya su kuma malamai suke daukar sistas?

Amirah MSS Kadpoly: Wasu malaman sukan tursasawa sistas, musamman wadanda ba musulmi ba. Idan suka nemi sista ta ki, sai su nemi kada su a jarabawa, in ba a yi hankali ba ma su ba su 'carry over', wato su maimaita jarabawar. Amma a lura ba dukkansu bane, wasu ne.

MUJAHIDAH: Shin kuna da wata kwakkwarar hujja ce ko kuwa?

Amirah MSS Kadpoly: Kwarai kuwa, akwai. Akwai rahoton da wata sista ta ba ni, tana ma da aure. Kuma bayan ya yi masu jarabawa, sai ya ce ta zo ofis dinsa ta karbi nata takardar, ita kuma ta ki zuwa. A sabili da haka sai ya ba ta 'carry over', saboda ya neme ta ta ki. Sai da Rijistarar darussan dalibai na Kwalejin ya sa baki, a karshe sista din ta ci jarabawarta.

MUJAHIDAH: Za ki iya gaya min sunanta ko sashenta?

Amirah MSS Kadpoly: Ina ga ba bukata.

MUJAHIDAH: Me za ki ce kan ra'ayin wasu mazaje na kin auren 'yan jami'a ko manyan kwalejoji irin namu?

Amirah MSS Kadpoly: Hakika akwai wasu mazaje masu irin wadannan ra'ayoyin. Wasu suna da wadannan ra'ayoyin ne saboda suna ganin su wadannan 'yan jami'a din sun fiye son abin duniya, su kuma ba za su iya biya masu bukatunsu ba.

MUJAHIDAH: Akwai matakan da kuke dauka don kau da irin wadannan matsalolin?

Amirah MSS Kadpoly: Alhamdulillah babu wata matsala da ba ta da mafita. Don haka da muka ga wannan matsala ba kawai ta tsaya a wannan kwalejin bane, ta shafi kasa baki daya, ta yadda sai ka ga sista ta gama jami'a ko Kwaleji ta shekara uku ba aure sai MSS ta bullo da wani shiri mai suna MEGACO (Marriage Guidance Consel). Manufar wannan ita ce kau da gwagware wadanda ba su yi aure ba. Wato in kana da wata matsala da ta shafi aure, to in ka sami MEGACO to za ta ba da shawara. Kamar idan 'yar uwa ta ga wani tana so, ko kuma dan uwa ya ga wata yana so, amma ya rasa yadda zai yi ko za ta yi, in sun zo gun MEGACO sai ta shiga tsakani.

MUJAHIDAH: Shin za a sami natsattsiyar yarinya a kwalejin nan kuwa?

Amirah MSS Kadpoly: Me kike nufi? Me zai hana? Akwai natsattsu mana. Duk kuwa da cewa Kwalejin a gurbace take, amma akwai sistas da suke da tarbiyya tun daga gida, don haka ko da suka zo nan ba wanda ya iya canza su. Akalla za su haura kashi biyu cikin dari.

MUJAHIDAH: Wace shawara za ki ba sabbin shiga kwalejin nan?

Amirah MSS Kadpoly: Shawarata gare su ita ce a matsayinsu na sabbin dalibai za su ga sabbin canje-canje a sabon muhallinsu, amma duk da haka kar su ji cewa don ba su tare da iyayensu za su iya yin abin da suka ga dama. Su sani cewa Allah (T) yana tare da su a ko'ina. Kamar yadda ya fada a Alkur'ani "Ina tare da ku a duk inda kuke." Manzon Allah ma ya fada cewa "Ka bauta wa Allah kamar kana ganin sa, idan kai ba ka ganin sa to shi yana ganin ka."

MUJAHIDAH: To wace shawara za ki ba sistas din da za su gama kwalejin nan?

Amirah MSS Kadpoly: Shawarata ita ce su sani cewa za su shiga katuwar al'umma ce, don haka akwai jan aiki a gabansu. Saboda haka ilimin da suka samu su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace. In sun je gida su bi iyayensu da mazajensu ga wadanda suka yi aure. Wadanda kuma ba su yi aure ba su yi kokari su yi aure, saboda Manzo (S) ya ce aure cikon addini ne. Kuma su watsa ilimin da suka samu ga wadanda ba su da shi.

MUJAHIDAH: Sista wace shawara za ki ba iyaye?

Amirah MSS Kadpoly: Shawarata gare su ita ce su yi kokari su rika tarbiyyantar da 'ya'yansu kamar yadda shari'a ta tanada. Su sani cewa a ranar lahira Allah zai tambaye su kan yadda suka ba da wannan tarbiyyar. Manzon Allah ya ce "Kowannenku mai kiwo ne, kuma za a tambaye shi kan abin da yake kiwo." Don haka a sanar da 'ya'ya abin da Allah ya wajabta musu, da abin da ya haramta masu. Su kuma sani cewa Manzon Allah ya ce tarbiyyantar da yaro guda ya fi sadaka da sa'i guda. Kuma Manzon Allah ya ce babu talaucin da ya fi mutum ya zama ba shi da tarbiyya, kuma babu arzikin da ya fi mutum ya zama yana da tarbiyya. Kuma ya ce kyakkyawar tarbiyya gaba take da ilimi, kuma ilimi shi ne tushen hikima.

MUJAHIDAH: To wace shawara za ki ba mazajen da suke son matansu su ci gaba da karatu a manyan makarantu?

Amirah MSS Kadpoly: Shawarata gare su ita ce wannan yana da kyau. Saboda Allah ya wajabta mana neman ilimi. Kuma Manzon Allah ya ce neman ilmi farilla ne a kan mace da namiji. A nan Allah bai ambaci maza kawai ba. a wani hadisin ma ya ce duk wanda ya ilmantar da namiji to ya ilmantar da mutum guda ne, kuma duk wanda ya ilmantar da mace, to kamar ya ilmantar da al'umma ne. Ka ga wannan yana nuna muhimmancin neman ilimi. Wasu na ganin tura matansu manyan makarantu zai kawo lalacewarsu, wannan ba haka bane, in ka ga haka ta auku to dama can irin ta ko a gidanka ne za ta lalace, amma in dai tana da tsoron Allah ba abin da zai sa ta karkace.

MUJAHIDAH: Mun gode kwarai.

Amirah MSS Kadpoly: Ni ma na gode.

   

Komawa Babban shafinmu