| Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a
In ji Mataimakiyar Amirah ta Jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato
Kai aikin jarida wani lokaci yana da matsala 'yar karama kuma babba. Ba matsalar da ta fi ka je yin hira da mutum, rikodarki ta ba ki kunya. Abin da ya faru ga Wakiliyarmu Malama Lubabah Ibrahim Gusau kenan da ta je yin hira da Mataimakiyar Amirah ta Jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato, Malama A'isha Laraba Yusuf. Don haka sai ta ba ta tambayoyin a rubuce ita kuma ta amsa mata su a rubuce, a takaice cikin Turanci. Don haka wannan hirar ta zama a takaicen takaice.
MUJAHIDAH: Malama yaya sunanki?
Malama A'isha Laraba Yusuf : Sunana A'isha Laraba Yusuf. An haife ni ranar 17-72 a Gusau, jihar Zamfara. na yi makarantar firamare ta Ja'afaru da ke Sabon gari Zariya daga 1979-1984. Daga nan na wuce Sakandaren gwamnati da ke Samaru Zariya. Daga nan na tafi Kwalejin ilimi ta Tarayya da ke Gusau 1991-1994. Sannan a 1997 na sami shiga Jami'ar Usman Danfodiyo da ke nan Sakkwato ina karanta fannin noma, kuma insha Allah zan gama a shekarar 2001.
MUJAHIDAH: Shin me ya karfafa ki har kika kai Jami'a kina karatu?
Malama A'isha Laraba Yusuf : Kakana shi ya karfafa min gwiwa, sannan kuma ina ganin a matsayina na mace musulma wannan wani kalubale ne da ya kamata in fuskanta, domin ni ma in ba da gudummawata ga 'yan uwana mata, ganin yadda wasu mata da ba musulmi ba duk sun mamaye ko'ina sun cin zarafin mu musulmi a gwamnatocin jihohi da na Tarayya.
MUJAHIDAH: Shin ko kina ganin mata musulmi sun kai nawa a Jami'ar nan/
Malama A'isha Laraba Yusuf : A gaskiya ina ganin kashi uku cikin hudu na mata da ke Jami'ar nan musulmi ne
MUJAHIDAH: Nawa ne suke cikin MSS har ana harkoki da su?
Malama A'isha Laraba Yusuf : Ina ga ba za su wuce kashi daya bisa uku ba.
MUJAHIDAH: Wadanne matsaloli kuke fuskanta a Jami'a a kokarinku na bin Musulunci?
Malama A'isha Laraba Yusuf : To tunda nan ne Cibiyar daular Usmaniyya, don haka tun daga Mataimakin Shugaban Jami'ar har zuwa shugabannin sassan karatu na Jami'ar akasari musulmi ne. don haka ba mu da wata matsala ta fuskacin hukumar Jami'ar. In ma kika kalli dokokin Jami'ar kusan duk sun dace da al'adunmu. Kuma Hukumar Jami'ar na da sha'awar ayyukan MSS.
MUJAHIDAH: Ba mu misalin yadda rayuwar 'yar Jami'a take.
Malama A'isha Laraba Yusuf : 'Yar Jami'a tana ganin ita ta mallaki kanta, don haka tana yin duk shigar da ta ga dama, kuma ta je duk inda ta ga dama. Amma yayin da ta fara gane kann lamarin Jami'ar, sai ta ga cewa lalle ya kamata ta canza yanayin rayuwarta, a lokacin ne za ta gane ashe duniyar nan kurkuku ce ga mumini, kuma aljanna ga wanda ba mai imani ba. A lokacin ne za ta saduda.
MUJAHIDAH: Shin akwai matsalar sa hijabi a Jami'ar nan?
Malama A'isha Laraba Yusuf : Kamar yadda kika sani a kowace al'umma ta musulmi maganar sa hijabi yana kan gaba. To mu a nan wasu tun daga gida ba su soma sa hijabin ba, don haka in sun zo nan sai ya zame masu matsala. Wasu kuma a gaskiya ba su fahimci menene ma'anar hijabin ba ma kansa. Amma dai ina ganin akwai ci gaba ta fuskacin sa hijabi a Jami'ar nan, a lokaci guda kuma ba zan ce ba matsala ba.
MUJAHIDAH: Wane kira kike da shi ga iyaye kan karatun 'ya'yansu?
Malama A'isha Laraba Yusuf : Ni kiran da zan yi masu shi ne su sani fa an ce tarbiyya daga gida take somawa, kodayake ba a gida take karewa ba. don haka wajibi ne iyaye su ba 'ya'yansu, musamman mata ilimin addinin Musulunci, ta yadda da zaran sun zo Jami'a ba za su sha wahalar bin ka'idojin addinin ba. Kodayake Allah shi ke shiryar da wanda ya so.
MUJAHIDAH: Wace shawara kike da ita ga wacce take shirin shiga Jami'a?
Malama A'isha Laraba Yusuf : To wasu kan ce wai sai mace ta yi aure tukuna ya kamata ta zo Jami'a, amma ni ina ganin ba haka bane. Abin da yake da muhimmanci shi ne mace ya zamanto tana da tsoron Allah, ta yadda za ta rika kame kanta, ta rika yin shiga ta mutunci, ta rika magana yadda ya dace. In tana haka za a rika ganin girmanta. Kuma dama in dai tana jin tsoron Allah, Allah ya ce zai shiryar da ita. Ina ga wannan shi ne. Allah ya taimaki masu kokari a tafarkinsa ya kuma kiyaye su.
|