| Tsarabar taron mu’utamar na ‘yan uwa mata
Daga Zainab Adamu
A cikin watan Safar ne ‘yan uwa mata musulmi na da’irar Zariya suka shirya mu’utamar, wanda aka shafe kwanaki biyu ana yi a Madrasatul Fodiyya Babban Dodo Zariya. A karshensa ne ma suka gayyaci Malam Zakzaky ya rufe masu taron da jawabi. Amma tun farko Malama Fatimah Ahmad, wadda ta jagoranci shirya mu’utamar din, ta yi gabatarwa, sannan Malama A’isha Dinya ta bude taron da addu’a. A yayin da Malama Maryam Usman ta yi karatu daga Alkur’ani. Wannan fa duk a ranar da Malam Zakzaky ya rufe taron ne.
Taron mu’utamar din, wanda aka fara tun ranar wata Juma’a ya sami halartar ‘yan uwa mata sama da hamsin, wadanda suka fito daga unguwanni da kauyuka daban-daban na Zariya da kewaye.
Abin ban sha’awa shi ne su ‘yan uwa matan ne suka shirya abin su suka kuma tafiyar da shi. Kafin ranar rufewa an gabatar da jawabai daban-daban kamar muhimmancin ilimi, wanda Malam Abubakar Abdullahi Almizan ya gabatar, da wajibcin gwagwarmaya, wanda Malam Abdulhamid Bello ya gabatar, da son Iyalan gidan Manzo (Ahlul bait), wanda Malam Ibrahim Muhammad Potiskum ya gabatar. Sai kuma ‘yan uwantaka wanda Malama Zeenat Ibrahim ta gabatar.
A jawabinsa kan wajibcin neman ilimi, Malam Abubakar Abdullahi ya nuna cewa sharadi ne na shiga Aljannah ilimin sanin Allah. Game da wannan shi ne ya nuna cewa babu yadda mutum zai yi ya bautawa Allah Ta’ala da jahilci. Hujjarsa na fadin wannan shi ne inda Allah Ta’ala yake cewa “Ka san ni kafin ka bauta min.”
Ya nuna cewa Imam Khomain ® ya kasa mutane har kaso uku. Na dayansu shi ne Malami, akwai jahili wanda ya takaita kansa wajen neman ilimi. Sannan na ukunsu shi ne jahili wanda shi bai ma san ana neman ilimi ba, wannan ta fannin lahira kenan.
Sannan ya ci gaba da cewa “Imam Ali (AS) yana cewa idan kana neman arzikin duniya sai ka nemi ilimi. Idan arzikin lahira kake nema, to ka nemi ilimi. Kuma idan kana neman duk sai ka nemi ilimi.”
Malam Abubakar ya ci gaba da cewa babu abin da ake amfana da shi daga jahilci. Babu wani uzuri da mutum zai bayar na kin neman ilimi a wannan zamanin. Kamar mace ta ce iyayenta, ko mijinta sun hana ta ta je ta nemi ilimi. Ya ce “Idan ba mu tashi tsaye mun nema da kanmu ba, ‘ya’yanmu ne za su koya mana nan gaba? Ko kuma wadanda muke ce masu jahiliyya ko amawan gari sune za su zama Malamanmu nan gaba idan daula ta kafu? Sai mu yi ta zama daula muke jira?”
Sannan ya karkare bayaninsa da cewa dole ne mu tashi mu nemi ilimi idan dai ba ma son haka ya kasance a kanmu. Domin idan har muka tsaya daula ta kafu, to wasu ba mu ba sune za su mamaye ko’ina kamar wajen aikin likita, injiniya da sauransu.
Shi kuwa Malam Ibrahim Potiskum a jawabinsa kan wajibcin biyayya ga Ahlulbait, ya raba maudu’in gidan uku ne. Na farko shi ne wajibci, na biyu biyayya, na uku Ahlul bait.
Ya ce idan aka ce wajibi menene ake nufi da wajibi? Sannan ya amsa da cewa wajibi wani abu ne wanda ya zama tilas a kan mutum ya aikata. Wanda da mutum zai bar shi da ukuba za a yi masa. Idan kuma ya aikata shi zai samu lada mai yawa, tare da fatan neman kusanci ga Allah.
Malamin ya ce biyayya kuwa wani abu ne da yake kamar wajibi saboda umurnin Allah ne da Manzonsa. Yadda ya zama wajibi ga musulmi ya yi biyayya ga Manzon Allah haka ya zama wajibi ga mutum ya yi biyayya ga Iyalan gidan Manzo. Saboda Allah Ta’ala shi ne ya wajabta mana biyayya ga Manzonsa, haka kuma ya wajabta mana biyayya ga Ahlul bait ta bakin Manzonsa. Saboda Manzon Allah ba ya fadar son ransa sai abin da Allah Ta’ala ya umurce shi da ya fada.
Daga nan Malam Ibrahim Potiskum ya yi bayanin su wanene Ahlul bait. Ya ce su biyar ne. Manzo (SAWA), Fatima (AS), Ali (AS), Hasan (AS), da kuma Imam Husain (AS). Ya ce da Mala’ika Jibril ya zo wa da Manzon Allah da wahayi na tsarkake iyalan gidansa cikin suratul Ahzab, inda Allah Ta’ala yake cewa “Lallai Allah yana nufin ya tsarkake ku tsarkakewa,” wasu suna ganin kamar Ahlul bait sune matan Manzo, to sai Manzon Allah ya nuna su wanene Ahlul bait nasa, lokacin da ya shigar da su cikin ‘kisa’a, har Ummi Salma ta nuna tana son ta shiga ciki, sai Manzon Allah ya ce mata ta yi hakuri, wadannan na ciki sune Ahlul bait nasa.
Malam Ibrahim ya kara da cewa bayyana su wanene Ahlul bait ya sake aukuwa a ranar mubahala, inda Manzo inda Manzon yake cewa “Mu zo da ‘ya’yanmu, ku ma ku zo da ‘ya’yanku, mu zo da matayenmu ku ma ku zo da matayenku, mu zo da kawunanmu ku zo da kawunanku, sannan mu roki Allah ya tsine wa makaryaci.”
Malamin ya yi bayanin cewa wajen “‘ya’yanmu” da Manzo ya fadi, sai ya zo da Hasan da Husain. Wato wannan aya tana nuna mana cewa wadannan ‘ya’yan Manzo ne. “Matayenmu” kuma sai ya zo da Fatima (AS), “kawunanmu” kuma sai ya zo da kansa da kuma Imam Ali (AS). Da Yahudawan suka ga haka sai suka gudu, tunda sun san cewa idan suka yarda suka yi tsineneniya za ta fada kansu. Sai da babban Yahudawan ya aika ya ce a ga da su wa Manzo zai fito. Da dan aiken ya koma sai ya lissafo masa wadanda suka fito tare da Manzon Allah (SAWA), sai ya ce to kar su yarda su yi tsineneniyar, domin ba za su ci nasara ba. Domin dukkansu makusantan Manzo ne, bai dauko wani bare ba.”
Mai karatu sai a yi min afuwa dangane da abin da sauran malamai biyun suka fada a wajen mu’utamar, domin abin da na iya riska kenan. Amma alhamdulillahi tunda ga cikakken jawabin da Malam ya yi a wajen rufe mu’utamar din nan an rubuta a wannan Mujahidah.
|