| Juyayin waki’ar kama Malama Zeenat
Daga Nuruddin Usman Danja
Kamar yadda kowa ya sani la’ananne dan ta’adda wato Janar Tazarce ya yi mushe ne a ranar 8 ga watan Yunin 1998. Daga cikin irin jerin ta’addancin da ya dinga tafkawa, musamman a kan harkar Musulunci, ya rage saura kimanin wata biyu ya zarce ne ya aikata mafi munin ta’addancin da ya yi a baya.
Domin a ranar wata Juma’a 17 ga watan Afrilu shekarar 1998 ‘yan sanda suka auka wa wasu ba’adin masallata a masallacin Juma’an cikin garin Zariya. Sun yi hakan ne don neman tonon fada da kuma neman dalilin auka wa ‘yan uwa musulmi masu gwagwarmayar tabbatar da addinin Allah a bayan kasa. Duk da cewa hakarsu na neman kawo hargitsi bai cinma ruwa ba, sai kawai suka nufi gidan Jagoran Harkar gwagwarmayar tabbatar da Musulunci, Malam Ibrahim Zakzaky, wanda a lokacin yana tsare, suka keta alfarmar gidan, suka kama iyalan gidansa duka da suka hada da mata da yara, ciki har da wani dan jinjiri mai kimanin shekara daya da aka haifa bayan kama Shehin Malamin.
Har wa yau ‘yan sanda sun je gidan Alhaji Hamidu Danlami, Manajin-Daraktan I.M. Publications, inda nan ma suka kama duk mata da yara da ke gidan ciki, har da wata mata mai tsohon ciki, suka wuce da su ofishinsu, inda suka cunkusa su duk a wani karamin daki, duk da tsananin zafin da ake yi a wancan lokacin. Ita matar Malam Zakzaky wato Malama Zinat an yi mata duka har aka ji mata ciwo. Kuma suka hana su abinci da ruwa har na tsawon kwana biyu.
Daya daga cikin yaran Malam ma da yake fama da ciwon kunne aka hana shi ya sha magani. Baya ga haka ‘yan sanda sun kwashe kayayyakin Malam kamar su rediyo da talabijin da sauran tarkacen gidan. A ranar Talata da ta biyo baya kuma sai aka kai su wata kotun yanki da ke Palladan, inda Alkali Ibrahim Ahmad ke alkalanci, ana tuhumar su da laifin ta da hankalin jama’a da cin zarafin ‘yan sanda. Abin mamaki! A wani bangare kuwa sai ‘yan sanda suka shiga tursasa wa mabiyan Malam Zakzaky a cikin Zariya. Suna bi gida-gida suna kama su da gallaza masu nau’o’i na azaba iri-iri, har wata mata da take nakuda suka kama.
Muzaharar Kaduna
A Kaduna kuwa, kwanaki uku bayan cin zarafin iyalan Malam sai wasu ‘yan uwa musulmi suka fito suna muzahara ta lumana don nuna rashin jin dadinsu da irin aika-aikan da ke faruwa a Zariya, da kuma kiran a saki iyalan Malam Zakzaky. Sai kawai ‘yan sanda suka bude masu wuta da albarushi, inda nan take mutane takwas suka yi shahada. Sune Jibrin Maitakarda, Muhammadu Sani, Muhammadu Tukur, Abdullahi Mai tumatir Rigasa, Ahmad Katsina, Sani Umar Dogo. Sauran sune Umar Faruk Jauro Gutel ta jihar Gombe, da Dauda Adamu Unguwar Mu’azu.
Bayan haka an ji ma mutane da dama raunuka a wannan rana. Bayan haka washe gari ne kuma an taru a Asibitin musulmi da safe domin a yi wa shahidan jana’iza, kawai sai ga ‘yan sanda suka bi ‘yan uwa har makabartar Tudun wada suka bude wuta. A ranar ‘yan uwa uku suka kashe, ciki har da Muhammadu Bakir, dan watanni hudu da haihuwa. Mahaifiyarsa ma sai da ta sami nata rabon na harsashi. Sauran sune Sulaiman Hasan da Salisu Gwaza road.
Ba ‘yan uwa kadai wannan ta’adancin ya shafa ba ‘yan sanda sun kashe wasu mutane hudu da ba su ji ba ba su gani ba. Uku daga ciki iyalan wani ne mai suna Malam Danladi da ke ‘yan lilo a T/wada. Matarsa A’ishatu da ‘yarsa mai suna Dukwai da dansa Hasan ‘yan sandan suka kashe. Cikon na hudun shi ne Rabi’u Aliyu da ke zaune a Zango road T/wada. Akwai kuma wani dan kasar Cana da ke aiki a hukumar sufurin jiragen kasa da ‘yan sanda suka harba kuma ya yi jinya a asibitin St-Gerad Kaduna.
A Zariya kuwa ‘yan sanda sun ci gaba da tsare wadannan ‘yan uwa mata a ofishin ‘yan sanda daban-daban da ke Zariya har kimanin wata biyu, inda daga baya kotu ta ba da belinsu. Hakika wannan waki’a tana dauke da tarihin da ba za a taba mancewa da shi ba. Domin ta alamta karin maganar da Hausawa ke cewa “In aski ya zo gaban goshi ya fi zafi.” Ko kuma inda suke cewa “In ka ji ganga ta cika zaki, to ta kusa fashewa,” domin kuwa duk abin nan da ake ashe Allah Ta’ala yana gab ne da yi ma tukka hanci. Haka kuwa aka yi domin bayan fitowar su Malama Zinat ne da wasu ‘yan kwanaki kawai, sai ga labari mai dadin ji ga duk muminan da aka zalunta, ranar wata Litinin ce mai tarihi da farin ciki, ta bakin Malam “dolon ya mutu.”
Allah Ta’ala ya amsa addu’ar Malam da sauran ‘yan uwa, ya halaka Abacha a kan idonmu kamar yadda ya halaka Fir’auna a kan idon Annabi Musa da jama’arsa. Daga karshe ina rokon Allah ya kara tsine ma Abacha da duk wadanda suka goya masa baya wajen yakar musulmi. Kuma ina rokon Allah ya tabbatar da mu a kan gwagwarmayar tabbatar da Musulunci karkashin jagorancin Malam Ibrahim Zakzaky. Allah ya ruguza kafirai da azzalumai da duk masu goya masu baya.
|