Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 12                                     Jimada Thani 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 12
  Jimada Thani
 DAGA TEBURIN EDITA
Irin Wainar da muka toya
 SHARHIN MUJAHIDAH
A gaida 'yan uwa mata
 WASIKU
Wasiku uku daga 'yan uwa mata
 BABBAN LABARI
Taron Nasarar Hizbullah a Zariya

Hizbullah ba za ta taba daukan kaskanci ba

Dole ne Malamai su hada kansu

Wajibi ne mu zama abin koyi

 HIRA TA MUSAMMAN
Shawara ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a

 LABARI
Lalacewar mata a Nijeriya

 FADAKARWA
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata
 NASIHA
Rayuwar aure a Musulunci

Kishiya Ko Abokiyar Zama?

 YARA
Ka tausaya ma dabbobi
 LIKITA
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda
 TARIHI
Gwarzantakar Ummu Wahab(R.A)
 RAYUWA
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Shirin hana almajirai bara zai yi nasara kuwa?

Hattara 'yayan talakawa

Kikan duba shafin

Almizan
  kuwa?
The Witness
  kuma fa?
Likita
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda

Daga Dr. Shu'aibu Musa

GABATARWA

Toshewar fitowar jariri lokacin nakuda da kuma tsawaitar nakudan da kan biyo baya suna daga cikin mafi munin hadurra da ke tattare da al'amarin da ya shafi ciki da haihuwa.

Wadannan abubuwa biyu tare suke gudana, kuma suna daga cikin abubuwan da ke kan gaba wurin sanadiyyar salwantar rayukan masu nakuda da ma jariran da ke cikin masu nakudan, musamman ma a wuraren da babu kular da ta kamata masu nakudar su samu.

Duk kuwa da cewa a 'yan shekarun nan an dan sami ci gaba ta fannin kiwon lafiya, musamman ta bangaren wayewar kai da karin sanin makamar aiki da ungozomomi da ake samun yawaitar su ke samu, har yanzu ana cin karo da munanan hadurra wurin nakuda da hahihuwa, kuma matsalolin ciki da haihuwa su suka fi kasancewa kan gaba nesa ba kusa ba wurin sanadiyyar mutuwar mafi yawan mata a kasashenmu.

Ashe kenan akwai karin muhimmancin kara wayar wa 'yan uwa mata kai kan ire-iren matsalolin da akan fuskanta yayin ciki da haihuwa da yadda za a kauce masu ko a magance su in har sun faru. Allah ya sa mu amfana amin.

Menene nakuda?

Masana ilimin kiwon lafiya sun rarraba nakuda a kan matakai uku. Wato matakai uku ne suka tattaru suka yi abin da ake kira nakuda, wanda bayan mai ciki ta bi wadannan matakai uku za ta haifi jariri.

Matakin farko shi ne yayin da mai ciki ta fara jin ciwon ciki, wanda kan zo ya dauke akai-akai kuma lokaci-lokaci. Yawancin mutane ma a hakikanin gaskiya sun dauka cewa wannan matakin farko na zafin ciwon cikin ne kawai ake nufi da nakuda. To ba haka bane. Wannan matakin farko ne kawai. Yakan fara ne tun daga lokacin da mai ciki ta kai matakin haihuwa ta dan fara jin ciwon ciki kuma ta ga wani abu da ake kira zaki-wani abu mai kama da majina gauraye da jini- ya fito daga farjinta. Makasudin ciwon cikin shi ne kokarin da mahaifa mai dauke da jariri ke yi na kara turojaririn kasa, kuma a lokaci guda bakin mahaifar na kara budewa don jaririn ya fito waje. Wannan matakin farko na nakuda na karewa ne a lokacin da bakin mahaifar ya gama budewa gaba daya, wato jaririn na iya fitowa kenan ba tare da matsala ba.

Sanin lokacin da aka kai karshen wannan matakin farko na da muhimmancin gaske, don kuwa duk wani yunkurin fitar da jaririn gabanin wannan na da matukar hadari.

Mataki na biyu a nakuda kuwa na farawa ne daga karshen matakin farko, wato lokacin da bakin jakar mahaifa da ke dauke da jaririn ya gama budewa. Wannan mataki na biyu shi ne na fitowar jaririn wannan duniya tamu. Kuma yana karewa ne lokacin da gaba dayan jaririn ya bullo waje daga jakar mahaifa. Shi ma wannan matakin na da muhimmancin gaske ga jaririn da ma mai nakudar don dai akwai hadurran gaske tattare da wannan matakin.

Sai matakin karshe, na uku, wanda ke fara wa daga inda mataki na biyu ya kare, wato tun lokacin da jariri ya fito duniya har zuwa lokacin da mahaifa ko uwa ta fito gaba daya. Wannan matakin ya hada da yanke cibi da haifar bangaren cibi da kan biyo baya, wato abin da ya hada jariri da mahaifar uwa, inda yake ci ya sha a sa'ilin da yake ciki-abin da a Hausa ake kira mahaifa ko uwa. Sai dai a kula cewa ba wannan jakar mahaifar da ya dauki jaririn ne ke fitowa ba, amma wani nau'in tsoka da ya hada jaririn da uwar ta cibi a lokacin zaman jaririn a cikin uwar.

Wannan mataki na uku shi ma dai yana da matukar muhimmanci don in ba an bi a hankali da lura ba, sai ya yi sanadiyyar rasuwar mai nakudar.

ME KE JANYO TOSHEWAR FITOWAR JARIRI?

Abin da ake nufi da toshewar fitowar jariri a yayin nakuda shi ne wani yanayi da kan iya faruwa bisa wasu dalilai ta yadda babu ci gaban nakuda a mataki biyu na farko na nakudar, wato rashin ci gaba da matakan fitowar jariri a kan kansa yadda aka saba. Abin nufi a nan shi ne cewa jariri ba zai fito ba, ba tare da wani agaji ba saboda toshewar hanya.

Dalilan da ka iya janyo toshewar fitowar jariri a lokacin nakuda suna da yawa, amma muhimmai daga ciki sun hada da:

1. Rashin daidaiton girman kan jariri da kasusuwan kwankwason uwa. Wannan kuwa na iya faruwa idan kan jaririn ya cika girma fiye da kima ko don tsananin girman jaririn gaba daya kamar yadda akan gani a uwaye mata masu ciwon sukari, ko kuma dai katon kan jaririn sanadiyyar wata ta jaririn da ta shafi kansa.

Haka kuma wannan rashin daidaiton kan jaririn da kasusuwan kwankwason uwa na iya karuwa saboda tsananin matsi da karantar fili tsakanin kasusuwan kamar yadda akan gani a wasu mata da suka cika gajarta fiye da wani mikdari. A irin wadannan, kan jariri daidai yake yadda ya kamata, amma kuma babu fili tsakanin kasusuwan uwa ta yadda zai bi ya fito.

2. Nakasar kasusuwan kwankwason uwa na iya toshe hanyar fitowar jariri a lokacin nakuda. Irin wannan nakasu kuwa na iya kasancewa saboda rashin isasshen abinci mai gina jiki (musamman kasusuwa) tun lokacin da uwa take yarinya. Haka kuma nakasun na iya biyo bayan wani rauni ko ciwo.

3. Rashin daidaiton kwanciyar jariri a mahaifa na iya hana fitowar jariri. Alal misali kamar jarirai da sukan kasance a gicciye babu yadda za a yi su fito da kansu ba tare da agaji ba.

4. Sarkafaffun 'yan biyu na iya toshe fitowarsu daga mahaifa. Wato idan 'yan biyu sun sarkafe da juna a mahaifa ta yadda daya ya hana dayan fitowa, kenan babu wanda zai fito a tsakaninsu.

5. Sauran wasu cututtuka da suka shafi mahaifa kamar irin su ciwon da ake kira dutsen ciki, wanda kan tsiro a mahaifa kuma idan ya yi girma sosai kuma an sami ciki, dutsen na iya toshe hanyar fitowar jaririn.

YADDA AKE GANE MAI FAMA DA MATSALAR TOSHEWAR FITOWAR JARIRI

Da farko daga jin yadda nakudar ta kasance tun daga farkon matakin farko zuwa lokacin da ake duba mai nakudar, ana iya gane mai fama da matsalar toshewar fitowar jariri. Kamar yadda wakakila ake tsammani. Farkon abin da kan biyo bayan toshewar fitowar jariri shi ne tsawaitar nakuda a matakai biyu na farko.

A saboda haka, muddin an ga nakuda ta tsawaita fiye da yadda ake zato, to dole ne a dauka cewa watakila toshewar nakudan ce ya janyo haka. Da yake tsawon lokutan da mace ke dauka a kowane matakan uku na nakuda kan bambanta daga mace zuwa mace, yana da wuya a ce tsawon lokaci kaza ne, in an wuce ana iya cewa nakuda ta tsawaita. To amma galibi idan an lura da cewa matakin farko na nakuda ya wuce sa'a goma sha takwas, musamman in har ta ga ruwa, to ana iya cewa nakuda ta tsawaita kuma wannan alamar cewa akwai toshewar nakudar ne. Haka kuma idan matakin nakudan na biyu ya wuce sa'a daya, to alamar cewa akwai toshewar fitowar jariri ne, kuma dole a dauki matakin agazawa nan take.

Wadanda akan kawo asibiti da wannan matsalar toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda an lura sukan kasance sun galabaita matuka don wuya da zafin ciwon ciki da suka dade suna sha na tsawon lokaci, ga kuma rashin barci da samun damar cin abinci ko sukunin shan isasshen ruwa. Sukan kasance cikin matukar damuwa ainun. Yawanci kuma za a ga har sun ma kwashi cututtuka iri-iri daga kokarin da aka yi ta yi a gida don ganin ta haihu da kanta ba tare da la'akari da daukar kwararrun matakan kare ta da jaririn daga kwayoyin cuta ba.

A wasu lokuta ma, kafin su kawo Asibiti, har tuni mahifar ta fashe! In ma an yi sa'a mahaifar ba ta fashe ba, to hatta jaririn ma dai ya galabaita kuma dole a dauki matakin fito da shi cikin gaggawa.

YADDA AKE MAGANCE MATSALAR

Kamar yadda Hausawa ke cewa "Rigakafi ya fi magan," haka al'amarin yake a nan. Da yake kusan yawancin abubuwan da ke janyo toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda ana iya gane su ga mace ko tun kafin ta ma sami cikin ko kuma bayan ta sami ciki, amma kafin ta fara nakuda, ashe kenan ana iya magance su in har haka mai yiwuwa ne, ko kuma a dauki matakin agaza mata tun kafin ma ta fuskanci matsalar.

Wannan shi ya sa zuwa awon ciki na da amfani. Don kuwa a lokacin awon ana iya gane ko wacece za ta iya fuskantar matsalar nakuda kuma a dau matakin da ya fi dacewa.

Sannan muddin mai ciki ta shiga nakuda, akwai bukatar a sa ido a kanta sosai har sai ta gama wadannan matakai uku na nakuda (ta haihu lafiya). Da zarar an soma ganin alamun toshewar fitowar jariri sai a dau matakin agaji da gaggawa. In a gida ne sai a nufi Asibiti nan take. Yin nakuda ba tare da sa idon kwararriyar ungozoma ba babban hadari ne ga rayuwar mai yin haka da jaririn da take dauke da shi.

Allah ya sawwaka, amin.

   

Komawa Babban shafinmu