| Dalilan halascin maulidin Nabiyyi
Daga Abdulhamid Bello
Watan Rabi’ul Awwal wata ne mai tarin albarka wanda a cikinsa aka haifi fiyayyen talikai, Muhammad dan Abdullah a birnin Makka a shekarar da ake kira shekarar giwaye-wato shekaru dubu daya da dari hudu da saba’in da hudu da suka wuce. Babu wani wata a cikin watannin shekara wanda ake yawan taruka da bukukuwa a cikinsa tun farkonsa har zuwa karshe, musamman ma a wannan nahiya tamu kamar watan Rabi’ul Awwal.
Duk da cewa an sami wasu ‘yan kungiya a cikin musulmi masu tsananin suka har da haramta ko kafirta irin wadannan taruka ko bukukuwan maulid da sunan wai bidi’a ne, an sha yi masu raddi a wurare daban-daban na irin wadannan tarurruka ta kafa hujjoji na hankali da ilimi.
A nan na kawo wasu daga cikin dalilan halascin taron maulidin Annabi:
1. Taron maulidin Annabi (SAW) yana nuni ga jin dadi da farin ciki da haihuwar Manzo (SAW). Hakika kafiri ma zai amfana saboda nuna farin ciki da haihuwar Manzo (SAW). Ya zo a cikin Sahihul Buhari cewa ana saukake wa Abu Lahabi azaba duk ranar Litinin saboda ‘yantar da Suwaiba, kuyangarsa, yayin da aka yi masa bushara da haihuwar Manzo (SAW). Dangane da wannan ne Muhammad Nasiruddin ke cewa: Idan ya kasance kafirin da zargin sa ya zo da “Tabbat yada,” kuma madawwami a cikin jahannama, cewa duk ranar Litinin ana saukake masa azaba saboda farin cikinsa da haihuwar Muhammad (SAW), menene zatonka dangane da bawan da ya kasance duk rayuwarsa mai farin ciki da (haihuwar) Muhammad (SAW) ne kuma ya mutu yana mai kadaita Allah?
2. Manzo (SAW) ya kasance da kansa yana girmama ranar haihuwarsa; yana godiya ga Allah Ta’ala a cikinsa bisa ga ni’imomi masu girma da ya yi masa, da kuma falalarsa a gare shi da samuwarsa a wannan duniya. Domin dukkan samammu sun sami sa’ada albarkacinsa. Ya kasance yana bayyanar da girman wannan rana ta yin azumi-kamar yadda ya zo a hadisi daga Abi Katada cewa an tambayi Manzo (SAW) dangane da azumin ranar Litinin, sai ya ce “A ranar ne aka haife ni kuma a ranar ne aka yi wahayi gare ni.” Wannan yana daidai da ma’anar ranar maulid, sai dai salon ne ya bambanta. Amma ma’anar samamme ne, daidai ne ya kasance da yin azumi ko ciyar da abinci ko taron zikiri ko salatin Annabi (SAW) ko sauraron falalolinsa masu daraja.
3. Farin ciki da samuwar Manzon Allah (SAW), umurni ne na Alkur’ani. Kamar yadda Allah ya ce: “Ka ce da falalar Allah da rahamarsa, to da wannan ne za ku yi alfahari.” Allah Ta’ala ya umurce mu da yin alfahari da rahamarsa, kuma Annabi (SAW) shi ne mafi girman rahma. Allah ya ce: “Ba mu aike ka ba face rahma ga talikai.”
4. Manzo (SAW) ya kasance yana lura da sake gewayowar lokacin faruwar babban al’amari na addini. Idan wannan lokaci ya gewayo sai ya kasance wata dama ce ta tuna ko raya waki’ar da ta faru da kuma girmama ranar saboda waki’ar.
5. Hakika maulid yana kai ga raya salati da salami wanda yake abin nema ne ko wajibi da fadin Allah Ta’ala “Haka Allah da Mala’iku suna salati ga Annabi, ya ku wadanda kuka yi imani ku yi salati ga Annabi, ya ku wadanda kuka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama matukar sallama.” Kuma duk wanda yake kai wa ga abin nema ko wajibi a shari’a, shi ma ya zama abin nema ko wajibi a shari’ance. Kuma alkalami ya gajiya wajen bayyanar da yawan tasiri da hasken salati ga Manzo (SAW).
6. Maulidi ya hada ambaton haihuwar Manzo (SAW) da mu’ujizozinsa da tarihinsa. Ko ba a umurce mu bane da sanin sa da yin koyi da shi da debe kewa da ayyukansa da imani da mu’ujizozinsa da yarda da ayoyinsa? Lallai littafan maulidi suna tabbatar da wannan ma’ana.
7. Har wala yau yana daga cikin dalilan yin maulidi shi ne bijiro da hakkokinsa da suka wajaba a gare mu ta bayanin siffofinsa kammalallu da dabi’unsa managarta. Masu wake sun kasance suna gabatar da kasidu a gare shi. Kuma yana nuna yardarsa da ayyukansu har ma ya sakanta masu da kyautar dadaddan abubuwa da salati. Idan Manzo (SAW) ya nuna yardarsa ga wanda ya yi yabo a gare shi, to yaya yardarsa za ta kasance ga wanda ya tattara bayani kan duk darajojinsa? Lallai a taron maulid akwai hakan, kuma ta hakan kusanci ne gare shi wanda ke jawo sanin sa da yardarsa.
8. Kuma an shar’anta girmama Manzo (SAW). Alfahari da ranar haihuwarsa da bayyanar da farin ciki ta yin walima, da taro don zikiri da kyautatawa fakirai na daga cikin mafi bayyanar girmamawa da alfahari da godiya ga Allah, saboda shiryar da mu zuwa ga addininsa da tagomashi da ya yi mana na aiko shi (Manzo) a gare mu.
9. Allah Ta’ala ya ce “Muna kissa a gare ka na labarin dukkan Annabawa, da abin da za mu karfafi zuciyarka da shi.” A nan hikimar kawo kissar Manzanni (AS) ita ce karfafa zuciyar Manzo (SAW) da shi. Babu shakka mu a yau mabukata ne zuwa ga abin da zai karfafi zukatanmu ta sanin tarihin rayuwarsa da halayensa.
10. Taro saboda maulid, raya ambaton Manzo ne Almusdafa (SAW), kuma yin wanann umurni ne na Musulunci. Kamar yadda kana iya ganin mafi yawan ayyukan hajji shi ma raya ambaton –mashhud- da matsaya abin yabo, kamar sa’ayi tsakanin Safa da Marwa, da ramyu jumar (jifan shaidan), da yanka a Minna, dukkaninsu raya abubuwa ne da suka faru a a da. Musulmi suna raya ambatonsu ta hanyar sabunta surorinsu (yadda abin ya faru a da) a yau. Dalilin yin haka fadin Allah Ta’ala “Ka yi shela cikin mutane da (yin) aikin hajji…” da kuma fadin Allah Ta’ala hikaya daga Annabi Ibrahim (AS) da dansa Isma’il (AS). “…Ka nuna mana ibadojinmu… (wato tsarin aikin hajji)…”
Dukkan abubuwan da muka ambata din nan na halascin taron maulid, muna nufin irin taron maulidin da ya wofintu daga munkarai ko abin zargi, wanda wajibi ne a yi inkarinsa.
|