Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 12                                     Jimada Thani 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 12
  Jimada Thani
 DAGA TEBURIN EDITA
Irin Wainar da muka toya
 SHARHIN MUJAHIDAH
A gaida 'yan uwa mata
 WASIKU
Wasiku uku daga 'yan uwa mata
 BABBAN LABARI
Taron Nasarar Hizbullah a Zariya

Hizbullah ba za ta taba daukan kaskanci ba

Dole ne Malamai su hada kansu

Wajibi ne mu zama abin koyi

 HIRA TA MUSAMMAN
Shawara ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a

 LABARI
Lalacewar mata a Nijeriya

 FADAKARWA
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata
 NASIHA
Rayuwar aure a Musulunci

Kishiya Ko Abokiyar Zama?

 YARA
Ka tausaya ma dabbobi
 LIKITA
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda
 TARIHI
Gwarzantakar Ummu Wahab(R.A)
 RAYUWA
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Shirin hana almajirai bara zai yi nasara kuwa?

Hattara 'yayan talakawa

Kikan duba shafin

Almizan
  kuwa?
The Witness
  kuma fa?
Nasiha
Rayuwar aure a Musulunci

Daga Abdulhamid Bello

KAFA GIDA MUSULMA

Gyaran kai a matakin farko da kiran wani zuwa ga Musulunci wajibai ne guda biyu na asasi a kan tafarkin da'awah a kan kowane musulmi da musulma. Tare da tsai da wadannan wajibai guda biyu, wajibi na uku mai matukar muhimmanci zai bayyana, shi ne kafa gida musulma. Kamar yadda ake son daidaikun musulmi ya zama mai tsayayyen akida, mai bin tsarin Musulunci ingantacce kuma abin koyi, haka ma ake da tsananin bukatar gida musulma ya zama ginshiki mai karfi kuma abin koyi wajen gina al'umma musulma. Iyali ko gida na da muhimmin rawa wajen canza tsarin al'umma, tabbatar da shi ko kuma rusa shi. Domin gida shi ne asasi ko tushe wanda daga nan ne ake renon dukkan sauyi. Gida ne ke gina yara a bisa wata tarbiyya da za ta lizimce su tsawon rayuwarsu.

Manzo (sawa) ya yi gaskiya yayin da ya ce "Dukkan abin haihua (yaro) ana haihuwarsa bisa dabi'a (Musulunci). Iyayensa ne suke yahudantar da shi, ko su nasarantar da shi ko kuma su majusantar da shi." Zance a kan kafa gida musulma, kalma daya ko biyu ba ya gamsarwa. Ba makawa a koma cikin littafan da aka rubuta da ma wadanda za a rubuta dangane da wannan darasi. Sai dai a nan za mu yi ishara don haskakawa ga muhimman abubuwan da ake bukata wajen kafa gida musulma.

ZABE: Lallai dan uwa musulmi da 'yar uwa musulma wadanda suka amsa kiran gwagwarmaya don gyara kansu da kiran wanninsu don tabbatar da Musulunci, wajibi ne a gare su su binciki junansu kafin aure. Kada su yarda da zaben tumun dare!

Lallai tun farko wajen gina iyali ko gida musulma bisa takawa, wajibi ne dan uwa musulmi ya zabi ma'abuciyar addini, wadda ta fahimci sakon da ya kawo ta wannan rayuwa, sai ta zama mai kyakkyawan taimako a gare shi a tafarkin gwagwarmya. Ta taimake shi, ba za ta raunana shi ba. Ta kare shi, ta tarbiyyantar da yaransa irin tarbiyyar Musulunci.

Haka ma wajibi ne ga 'yar uwa musulma kada ta yarda ta auri wani miji face mutumin kirki ma'abucin addini wanda zai kiyaye dokokin Allah wajen zama da ita. Kuma ya taimake ta wajen da'a ga Allah da neman yardarsa. Kuma ma sannar Manzo (sawa) ya shiryatar da mu zuwa ga yin haka yayin da ya ce: "Ana auren mata saboda dalilai hudu: Dukiyarta, danganenta, kyawunta da kuma addininta. Ka zabi ma'abuciyar addini, sai ka rabauta." Kuma tunda Manzo (sawa) bai tabbatar ma waliyyin yarinya aurar da ita ga wanda ba ta so ba bisa tilasci, wannan kenan ya ba 'yar uwa damar ta zabi miji salihi.

LIZIMTAR IYAKOKIN MUSULUNCI

Muna son iyakokin Musulunci da ladubban Musulunci su dawo su zama kan gaba cikin dukkan marhalolin kafa gida musulma. Wajen neman auren da daura shi da shirya dakin amarya da tarewa, da sauransu ya nisantar da al'adu da takalidai batattu na da da na yanzu wadanda a ciki akwai saba ma shari'ar Allah. Lallai mu tasaya kan iyakokin Musulunci a dukkan matakan auren, kuma mu saba wa al'adun da suke tattare matakan auren wadanda suka saba ma shari'a. Da yawa za su ki yarda da wannan a yau kamar yadda a da sukan ki yarda da shiga irin ta Musulunci wato hijabi, amma tare da cijewarmu a cikin wadannan matakan shari'a na aure za a wayi gari an saba da shi ba kuma bakon abu ba. Kamar yadda aka wayi gari yanzu an saba da ganin shiga irin ta Musulunci. Lallai wannan kokawa ne tsakanin daukaka da kaskanci. Idan muka yi riko kam-kam da daukaka da ladubban Musulunci muna iya tabbatar da mutuntakarmu ta Musulunci.

DAUKAKAN MA'AURA

Idan zabi ya kammala bisa asasin addini, kuma matakan auren suka kammala bisa dacewa da koyarwar Musulunci za mu kasance mun fara assasa gida musulma bisa ginshiki mai karfi wanda zai haifar da tabbata da kuma daukaka na gaske wadda da yawan gidajen ko iyalai suka rasa a yau. Daukaka fa ba daga wajen rai yake ba. Kuma ba yana tabbata da dukiya, da gidaje da tufafi da tarkace bane, a'a daga cikin rai ne daga takawar Allah Mai ba da daukaka, Mai ba da soyayya da tausayi. Allah ya yi gaskiya da ya ce "Daga cikin ayoyinsa ya halitta maku daga gare ku mata don ku natsu zuwa gare ta. Kuma ya sanya tsakaninku soyayya da tausayi." Kuma wani mai wake na cewa: Ba na ganin daukaka shi ne tara dukiya

Sai dai tsoron Allah (takawa) shi ne daukaka.

AURE IBADA NEW

Makasudin zuwanmu wannan rayuwa ta duniya shi ne bautar Allah. Don haka wajibi ne a gare mu mu mai da dukkan al'amuran rayuwarmu bauta ne wanda zai kusanta mu da Allah. Kuma mu nemi taimako da shi wajen bautar Allah da da'a gare shi da ci da sha da motsa jiki da ilmi da aiki da aure da tarbiyyan yara, dukkansu ibadu ne da kusanci da Allah. Mu zabi cikin kowanensu abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi. Mu nisanci abin da Allah ba ya so kuma yake fushi da shi.

Lalle wajibi ne ga dukkan dan uwa musulmi da 'yar uwa musulma su dauki aurensu a matsayin ibada ne wanda suke fatan samun ladar Allah da yardarsa. Saboda haka ya zama tilas ga kowanensu sanin abin da yake tattare da aure, na ladubba, ilmantarwa da hakkoki da wajibai da kwadaitarwa a kan tsayuwa da wadannan wajibai, da laziman wadannan ladubba, da kuma taimakon juna a kan nagarta, da tsoran Allah (takawa) da da'a ko biyayya ga Allah a cikin zamantakewar aurensu. Manzo (sawa) ya yi gaskiya- "Allah ya jikan mutumin da ya mike cikin dare ya yi sAllah ya kuma ta da matarsa idan ta ki ta tashi ya yayyafa mata ruwa a fuskarta. Allah ya jikan macen da ta mike cikin dare ta yi sAllah kuma ta ta da mijinta, idan ya ki ta yayyafa mashi ruwa a fuskarsa."

AURE AMINCEWA JUNA NE

Duk lokacin da aka sami cikakken soyayya da amince wa juna tsakanin ma'aurata- miji da mace, an sami tabbatar da daukaka wato sa'ada da kwanciyar hankali. Sai ya zama babu zace-zace, babu kokwanto ko shakku, babu sauran zantuka na gulma ko kiran karya a tsakaninsu. Ba a samun irin wannan aure sai a karkashin inuwar tsoron Allah (takawa) da kyakkyawan kusantar Allah (murakaba ) a boye da a bayyane, a fake da a halarce. Sai shi miji ya sami natsuwa da amincewa da jin cewa matarsa tasa ce shi kadai. Za ta kiyaye kanta, ta kare shi idan ba ya nan. Ta kuma jira shi komen dadewa. Kazalika, ita ma sai ta ji cewa mijinta nata ne ita kadai. A irin wannan soyayya da amincewa juna suna iya hana dukkan shaidanin mutum da na aljan samun hanyar shiga tsakaninsu, har ya kawo masu sabani. Sannan kuma za su iya yi wa 'ya'yansu kyakkyawar tarbiyya su taso da shi.

Za mu ci gaba insha Allah.

   

Komawa Babban shafinmu