Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 12                                     Jimada Thani 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 12
  Jimada Thani
 DAGA TEBURIN EDITA
Irin Wainar da muka toya
 SHARHIN MUJAHIDAH
A gaida 'yan uwa mata
 WASIKU
Wasiku uku daga 'yan uwa mata
 BABBAN LABARI
Taron Nasarar Hizbullah a Zariya

Hizbullah ba za ta taba daukan kaskanci ba

Dole ne Malamai su hada kansu

Wajibi ne mu zama abin koyi

 HIRA TA MUSAMMAN
Shawara ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a

 LABARI
Lalacewar mata a Nijeriya

 FADAKARWA
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata
 NASIHA
Rayuwar aure a Musulunci

Kishiya Ko Abokiyar Zama?

 YARA
Ka tausaya ma dabbobi
 LIKITA
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda
 TARIHI
Gwarzantakar Ummu Wahab(R.A)
 RAYUWA
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Shirin hana almajirai bara zai yi nasara kuwa?

Hattara 'yayan talakawa

Kikan duba shafin

Almizan
  kuwa?
The Witness
  kuma fa?
Nasiha
Kishiya ko abokiyar zama ?

Daga Isa Sulaiman Kabba rd, Kaduna.

Kishi kumallon mata. Kishi adon mata. Idan mace tana zaune tare da mijinta sai ya kara wani auren, to wane matsayi mace za ta dauki ita wannan matar? Abokiyar zamanta ko kishiyarta? Me zai hana mace ta rike matar mijinta a matsayin abokiyar zama maimakon kishiya? Ya ke 'yar uwata! Ko kin san illar kishi a rayuwarki ta duniya da gobe kiyama? Zafin kishi zai iya tunkuda ki zuwa ga kisan kai, sata, kazafi, lalata dukiya da kona gida.

An sha samun a lokaci daban-daban, inda zafin kishi ke sanya mace ta kashe mijinta ko kishiyarta ta hanyar guba ko ta wata hanyar daban. Ko ta yi wa kishiyarta kurciya, ta bar gidan, ko ta haukata mijinta. Wani sa'ilin ko kishiya ta bar gidan, sai mace ta mayar da huzamin kishinta ga dan kishiyar ko diyarta ta hanyoyi daban-daban kamar azabta su da yunwa ko yawan zagi da duka ba gaira ba dalili.

Kishi ya jefa wata mace ta yanka dan jaririn kishiyarta. Saboda Allah wannan jahilcin da hauka har ina? Menene laifin wannan jaririn? Anya mace za ta iya daukar kayan nauyin wadannan zunubban a kanta? Ko kin yi wa kanki wani shiri ne na kundumbala tare da jurewa ko rungumar bala'o'in da ke cikin wutar jahannama ne? Ya ke 'yar uwata! Har yaushe ne za ki ci gaba da zama shaidan yana miki kida,ke kuma kina faman tika rawa babu ko kunya ballantana gajiya? Ashe lokaci bai yi ba da za ki kubutar da kanki daga wannan raunin da Shaidan ya jefa ki ciki na mugun kishi da kyashi? Hausawa na cewa dabara ta ragewa mai shiga rijiya.

Menene ma'anar kishi?

Kalmar kishi tana daga cikin kalmomin da masana ilimin falsafa har yau din nan suka kasa fassara ta. Kamar kalmar "pleasure" wato nishadi, wacce ita ma masana falsafa suka kasa fassara ta. Abin da yake nishadi a wajena yana iya zama rashin nishadi a wajen wani. Haka ya sa suka fassara nishadi kishiyar aiki, ko duk wani abu koma bayan aiki. Duk wanda ya fassara kishi da sunan soyayya tsagwaron ta ya yi kuskure, kazalika shi ma wanda ya fassarea kiyayya zallanta da sunan kishi. To menene kishi? "Kishi wani kulli ne da ke cikin zuciya, wanda kuma ya fi kusa da kiyayya, amma a lokaci guda ba ya da nisa sosai a tsakanin sa da soyayya." Wani masanin falsafa ya ce: "Kishin wani abu ne da ke tsakanin soyayya da kiyayya. Wanda in ya yi kasa yana karkashin kiyayya, amma in ya yi sama yana zarce soyayya."

Kamar labarin da muka gabatar na matar da ta yanka dan kishiyarta, to a dabi'a, kiyayya ba ta bazuwa ko yaduwa ko yin naso ko yin tartsatsi ga abokin gaba, sai dai ta tsaya kansa kawai banda wani nasa. Fi ma labudda sai in kiyayya ta hadu da kishi haka ke faruwa.

An ce lokacin da Allahmah Tabataba'i ya yi raddi 'yan kwaminis a wani littafi nasa, sai da ya kai wani babban dan Kwaminis ya da duba littafin ya ga yadda Allamah din ya yi kaca-kaca da tsarin gurguzu, nan take ya fadi matacce! Me wannan Kwamared ya yi? Tabbas ya nuna kishinsa ga kwamishisanci ne! Kishi wani makami ne mai karfin gaske da ke jefa kiyayya karkashin kasa kuma ya harba soyayya can sama. kishi abu ne da zamani ko lokaci ne zai iya fayyace muninsa ko kyawunsa, alherinsa ko sharrinsa.

Idan misali an kama wani mutum an tsare a caji ofis, sai matarsa ta je domin ta yi belinsa, amma 'yan sanda suka hana har ma suka ce mata sai dai in kin yarda a saki mijinki ke kuma a tsare ki maimakon sa, ta ce ta yarda da hakan. Aka saki mijinta ita kuma aka tsare ta a wurin 'yan sanda har tsawon sati biyu. Me ta yi kenan? Hakika ta nuna tsananin kishinta ga wannan mijin nata! Ta fifita mijinta a kanta.

Kuma ma'anar kishi a nan yana nufin tsananin soyayya. Wani daki ne ya kama da gobara, kana akwai karamin yaro a cikinsa. uwar yaron ta je kasuwa tana dawowa ta ga wuta balbal na ci, amma ta yi karfin hali ta fada cikin dakin nan ta dauko danta, kuma da ita da yaron duk sun kone kurmus, babu wanda ya yi rai daga baya. me matar nan ta nuna? Tabbas ta nuna kishinta ga wannan yaron. Sannan kishin a nan yana nufin tsananin tausayi. Idan wata budurwa ana gobe za a daura mata aure tare da wani saurayinta, sai Ubanta ya ce an fasa auren! Sai kawai ta je dakinta tana faman rusa kuka, da dare ya yi ta daura igiya a sama ta rataye kanta!! Da safe aka leko aka same ta matacciya kuma sagalalliya, me ta yi kenan? E, ta nuna kishinta ga wannan saurayi nata. Kuma a nan kishi yana nufin tsananin bakin ciki da takaici.

Idan wani mutum ya hango wani abokin gabansa a cikin wata mota na miliyan biyu da rabi, sai ya zamana nan take ya fadi kasa sumamme. Me ya yi kenan? Tabbas ya nuna kishinsa da gabarsa ga wannan makiyan nasa. Kuma kishi a nan yana nufin tsanananin kiyayya.

ME KE SANYA MATA KISHI ?

Kamar yadda kalmar kishi take daukar ma`anoni daban-daban haka su ma matan suka bambanta game da dalilai da abubuwan da ke sanya su kishi. Saboda abin da zai sa waccan matar kishi ba shi zai sa wannan matar kishi ba. Kamar yadda wani Farfesa a fannin aikin jarida yake cewa "Babban abin da ya fi saurin haifar da sabani ko rashin fahimta, kai wani lokaci har da yake-yake babu kamar amfani da jita-jita ko daukar labarin da mutum ba ya da yakini a kansa."

Akwai mafi yawan mata wadanda kumallon kishinsu ba ya tashi sai lokacin da suka ji an ce wai mazajensu suna yunkurin neman wani aure ko suna hulda da matan banza. Ba tare da sun yi wani dogon bincike ba, sai su fara fito-na-fito da mazajensu. Wasu matan kuma sai ta tabbata mazajensu sun yi wani auren tukun, wasu kuma matan ko a cikin unguwarsu aka ga wata bazawara ko budurwa tana yawan gaishe da mazajensu, sai kishi ya tashi. Nan da nan su daura wa hannayensu zare domin su dambace da mazajensu da masu kokarin yi masu cin iyaka ko shiga huruminsu.

Wasu kuma matan saboda hassada da kyashi suna bakin ciki da kishi, wai domin kada mazajensu su auri matan da su ma za su zo suna shan lagwada da jin dadi kamar yadda su suka kasance suna shan lagwada. Wasu matan kuma tsufa da kidimewa ne ke jefa su kishi, domin suna tsoron mazajensu za su fita sha'aninsu kuma za su iya auren 'yan mata masu jini a jika su karkata zuwa gare su.

Wata macen kuma abin da zai sa ta kishi shi ne tana yiwuwa duk abin da ta mallaka har da dabbobinta da kaddarorinta ta sayar ta ba mijinta ya ja jari da shi, to duk lokacin da ya nuna alamar son yin wani auren, sai kishi ya tashi. Har ta rinka kiran sa butulu! Butulu.

Wata macen kuma saboda tsananin ladabi da biyayya da so da kauna da take yi wa mijinta, to duk ranar da ya nuna yana sha'awar yin wani auren, sai kishi ya tashi, saboda za ta dauka cewa ya mayar da son da take yi masa aikin banza.

IDAN BERA NA DA SATA...

Bai kamata ba a ce kullum idan ana batun kishi sai mu rufe ido mu kuma toshe kunnuwa muna ta faman zargin mata, wani sa'ilin ma har da zagin su. Wai su maza ba sa laifi ne? Idan mace, misali mijinta yana shan giya kuma har da yin caca, sai ta nuna kisihinta kan cewa lalle dole ya daina wadannan munanan abubuwan, ta yi daidai ko kuwa a'a? Domin ma'anar kishi wani lokacin yana nufin karkatar zuciya zuwa ga abin da kake so ko kuma take ki.

Kuma sad da ta bayyana ga mace cewa mijinta yana hulda da matan banza, kuma sai ta nuna tsananin kishinta cewa lalle sai dai ya daina wannan iskanci, ta yi daidai ko kuwa a'a? An taba ba ni labarin mutumin da yake da mata biyu kuma suke zaune a gida daya, ashe yana neman matan banza ba tare da saninsu ba. Kwatsam wata rana sai ga wata mata ta shigo gidan ta ce ina wane? Aka kira shi ya fito, duk a gaban sauran matansa wannan matar ta dinga surfa wa wannan mutumin zagi. Sannan ta ce "Ga danka nan. Ni ban iya rike dan shege ba!" Ta jefar da dan jaririn a kasa sannan ta bar gidan. matan kuma suka rike baki suna salati.

Kuma da yawan mazaje akwai wadanda idan suna da mata biyu sai su mayar da dayar 'yar mowa, dayar kuwa 'yar bora. Wato su mayar da daya matar kamar sarauniya a cikin kaji da lagwada da yi mata hidima iri-iri da atamfofi masu tsadar gaske da 'ya'yanta. Ita dayar kuwa an maishe ta tamkar baiwa, babu abinci mai kyau babu atamfa mai kyau, duk sun mutu, duk ta rame kuma ta lalace ta koma kamar wata 'yar aikin gida ko kuma baiwa. Idan mace ta nuna kishinta a wannan lokacin ta yi daidai ko kuwa a'a? sannan kuma idan aka sami azzalumin miji mai barin matarsa da yunwa, alhali yana da hali da wadata, ga yawan duka da rashin mutunta hakkinta, sai ta nuna kishinta, a irin wannan hali ta yi daidai ko kuwa a'a?

Misali kasar Thailand, kasa ce wacce babban hanyar samun kudinta babu kamar karuwanci. Har ya zamana otel-otel mallakin gwamnati ne, suk kuma karuwan gwamnati ce ta zaunar da su domin su rika sama mata kudin shiga ko haraji, sannan ita hukuma tana biyan su ladan wannan aikin nasu saboda tara mata haraji da suke yi. A 'yan shekarun baya sai ya kasance mafi yawan mazaje sun fi sha'awar karuwai fiye da matansu na aure. Su kuwa matan auren da suka lura karuwai suna janye masu mazajensu sai kowace mace ta rinka tanadin sabon wuka domin in dare ya yi ta yi wa mijinta kaciya! Kaciya fa. Matan suka shiga gutsire al'auran mazajensu. Dole ya sanya mazajen suka rinka jinya a Asibitoci. Kuma da wannan mataki ne suka yi maganin mazajensu masu biyewa 'yar gagara. Wannan hukunci na wadannan matan, sun yi daidai ko kuwa a'a? idan bera na da sata daddawa ma tana da wari, in ji hausawa.

YADDA ZA A MAGANCE KISHI?

Akwai mutane masu yawan gaske da suke da tunanin wai kishi ba shi da magani. Kuma har wala yau wasu matan sun yi imani da cewa wai duk wanda ya kwankwadi guban kishi, to sunansa marigayi, domin wai kishi ba shi da magani. Abin da ya kamata mu fahimta a nan shi ne dole mu yarda akwai maganin kishi. kuma akwai kishi mai kyau wacce shari'a ta aminta da shi, da kuma kishin da shari'a take kyama. Akwai hadisin da ya kawo bayanin mutane goma, wadanda suke riyawar su muminai ne. Annabi ya ce duk da haka su kafirai ne. Daga cikinsu akwai wanda ba ya kishin matarsa bilhasali yana tura ta zuwa aikata alfasha don kawai samun abin duniya. Wasu Malamai suna kafa hujja da irin wannan hadisin cewa, haka ita ma matar idan da mijinta zai koma hulda da karuwai kuma ta nuna rashin damuwa ko kishinta a bisa haka! Wallahu a'alamu. Dole ne mijinta ya yi kishin matarsa da kuma kishin kubutar da ita a lokacin da ya ga za ta auka wa sabon Allah a sarari. Kazalika ita ma matar. Wasu malamai suna cewa idan mace mijinta ya fada wani mau'in sabon Allah ta yi kokari domin ta yi masa saiti ya dawo kan tafarkin addini, amma duk da haka ya fandare kuma ya juya baya, to malaman suna ganin a irin wannan hali wajibi ne mace ta nemi khul 'i.

Manzo (s) yana cewa kishi wani bangare ne na imani, kuma wasannin banza da mata wani bangare ne na munafinci. Kuma Imam Ali (AS) yana cewa: Kishin kishiya zindikanci ne, kuma kishin namiji a kan matarsa wani bangare ne na imani. Wani zancen Imam Ali yana cewa: "Ku saurara ashe ba za ku ji kunya ba! Ku saurara ashe ba za ku yi kishi ba! Da har dayanku zai bar matarsa tana yawo tana ratsa mazaje tana kallon su, su ma suna kallonta."

Kishin da ya kamata mace ta nuna wa mijinta shi ne kada ta aminta ko ta bari mijinta ya kasance mashayin giya ko caca, luwadi, sata, fashi da makami ko hulda da matan banza da duk wani nau'in sabon Allah. Irin wannan kishi shi ake kira kishin addini kuma shi ne hakikanin imani. Ka so mutum don Allah, kuma ka ki mutum don Allah. Shi ya sa Imam Aliy (AS) ya ce a Nahjul Balagah "Amincewa mara imani tawaye ne ga Allah, amma tawaye ga mara imani shi ne imani da Allah. Kuma wajibi ne mace ta nuna wa mijinta bacin ranta da fushinta a lokacin da ta lura ya auka wa sabon Allah. Kuma wannan shi ne hakikanin kishin da ya kamata ta yi wa mijinta. Shi ne alamar tana da imani. Amma duk wani kishi koma bayan wannan da mace za ta yi wa abokiyar zamanta, wacce suke karkashin ikon namiji daya da ita, wannan kishin kenan ya zama bangare na munafinci da zindikanci. Sannan idan mace ta yi hakuri a bisa cutarwar abokiyar zamanta ko mugun halin kishiyarta, za ta samu garabasa iri biyu. A nan duniya Allah zai so ta domin yana son masu kyautatawa. A gobe kiyama za ta sami babban matsayi da lada saboda hakuri a bisa cutarwar kishiyarta. Da me kika manta?

Haka shi ma miji haramun ne da saninsa ya amincewa matarsa ta rinka zuwa karuwanci don neman abin duniya. Har Manzo (s) ya nuna mai irin wannan dabi'ar na rashin kishin matarsa kafiri ne, ko da yana zaton shi mumini ne. Kuma haramun ne a shari'a miji ya bar matarsa tana fita a cikin taburruji ta yi mugun caba kwalliya. Rabin gashinta a waje da wani irin daurin dan kwali wai shi ture-ka-ga-tsiya, da wani dan guntun gyale, wanda da kadan ya fi hankacif fadi, wai shi taya-ni-gantali. Matar ta zama ballagaza, shi kuma mijin ya zama sakarai. Ka ga irin auren sahoro da sahorama kenan.

Kuma wajibi ne kada namiji ya bar matarsa ta fita ko kofar gida ballantana unguwa, sai dai face da cikakken hijabi irin na addini, daga kanta zuwa 'kadamaini' dinta. Kuma wannan kishin matarsa wani bangaren ne na imani. Kuma kada miji ya aminta wani wanda ba muharraminta ba ya ga adonta face mutane goma da Kur'ani ya ambata. Aikata wannan wani bangare ne na kishin miji ga matarsa. Kuma bangare na imaninsa.

Kuma bisa nassin Kur'ani wajibi ne idan mutum yana da mace fiye da daya ya yi masu adalci. Rashin yi masu adalcin yana haifar da kishi a tsakanin su. Kamar idan shi mijin ya fi karkata zuwa dayansu, sannan ya mayar da dayansu saniyar ware a gidan. Adalci ya hada da wajen raba masu kwana, a wajen tufatarwa, wajen ciyarwa da shayarwa da muhallinsu, da kuma daidaita su wajen raba masu bukatun yau da kullum da kulawa da dukkanin 'ya'yansu, babu nuna bambanci ko son zuciya.

Wassalam.

   

Komawa Babban shafinmu