| Mata uwayen al’umma
Da sunan Allah mai rahma mai jin kai. Tsira da amincinsa su tabbata ga Fiyayyen halitta, Baban fiyayyar mata, Fatima (AS), Muhammad dan Abdullahi da Alayensa tsarkaka da wadanda suka bi tafarkinsa har zuwa ranar kiyama. Bayan haka, kasantuwar mata, sune kashin bayan duk wani ci gaba da ya samu a duniya, na ga ya kamata na yi magana kan wannan maudu’i, wato mata uwayen al’umma.
Cikin wannan muhadara, da izinin Allah, zan yi tsokaci ne kan rayuwar mata a Musulunci da kuma irin gudummawarsu ga gina al’umma. Da farko zan yi mukaddima ce kan rayuwa da kuma matsayin mata a wajen al’ummu daban-daban kafin, da kuma bayan zuwan Musulunci.
KAFIN ZUWAN MUSULUNCI
A’ummu daban-daban a waccan lokaci sun bai wa mata fassarori daban-daban, amma duk cikinsu ba wanda ya ajiye ta a matsayi mai daraja. Alal misali, Nasara sun dauki mace ce a matsayin shedaniya wadda ta tura Annabi Adam cikin halaka. Ita suka daura wa laifin cin itaciyar da Allah ya haramta wa Annabi Adam da Hawwa’u cin ta, don haka suke kyamar mace, wai kar ta tura su ga halaka.
Mutanen Hindu kuwa, dabba ma ta fi mace daraja, ta yadda za ka ga cewa su suke bai wa maza sadaki kafin su yi aure, sannan in mijinta ya mutu a hada su tare a kona. To ka ga a nan ko dabba ba a yi mata haka ba.
Su ko Larabawan Jahiliyya sun aje mace ce a matsayin dukiya kuma kayan ado. Da na iya gadon matar mahaifinsa in mahaifin ya mutu. Haka nan akan yi amfani da mata wurin shakatawa. Idan wani buki ya taso sai ka ga mata sun ci ado sun fito fili ana kallon su, ko ko su zo su yi rawa tsirara gaban maza.
Sai dai kuma, abinka da jahiliyya duk da haka suna bakin cikin matansu su haifa masu ‘ya’ya mata. Allah ya ce cikin Alkur’ani “Idan an yi bushara wa dayansu da haihuwar mace, sai fuskarsa ta wuni yana mai baki.”
Ba nan ta tsaya ba, ita ma mahaifiyar ta shiga uku kanta, don tun tana da cikin za a yi ta mata kashedin kar ta haifi mace. Ita kuma abin haihuwar ko dai a ruke ta bisa wulakanci ko ko a je a binne ta a rami. Allah ya ce “…yana nisantar mutane saboda munin abin da aka masa bushara da shi (tunani yake) ya rike shi (ta) ne kan bakin ciki ko ya turbude ta cikin kura (rami), abin da suke hukuntawa ya yi muni.”
Haka kuma daga cikin munanan al’adun Larabwa ga mata, yi masu zihari. Zihari shi ne mutum ya siffanta matarsa da muharramarsa kamar uwa ko ‘ya. Shi kenan sai ya zama ba zai yi wata mu’amala ta auratayya da ita ba, kuma ba ta da halin yin aure don bai sake ta ba. Haka za ta zauna a rataye ba aure ba saki.
Akwai al’adar ila’i, wato mutum ya rantse ba zai sadu da matarsa ba har na tsawon wani lokaci, kamar shekaru kamar biyu. Nan ma haka za ta yi ta zama har tsawon wannan lokaci ba miji ba saki. A cikin irin wannan yanayi, Musulunci ya zo ya samu mata.
A fitowa ta gaba insha Allah za mu yi nazarin yadda Musulunci ya zo ya daukaka mata sannan ya maishe su halittu masu daraja. Sai mun hadu.
Barakatu Ibrahim Sulaiman, Government College P.M.B 608, Toro, Bauchi State
|