Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 11                                     Rabi'ul Akhir 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 11
  Rabi'ul Akhir

Kikan duba shafin

Almizan

  kuwa?
Rayuwa
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Daga Isa Sulaiman Kaduna

Ma‘aurata wane lokaci ne suka fi bukatar soyayya a tsakanin su? Kafin su yi aure ko bayan sun yi aure? E, ma’aurata sun fi bukatar so lokacinsu na zaman aure, domin idan babu soyayya aure ba zai dore ba. Kuma a tsakanin dan karamin lokacin zai lalace. Ga wata aya da za mu gabatar: “Kuma daga ayoyinsa ya halitta maku daga kawunanku mata domin ku sami natsuwa zuwa gare ta kuma ya sanya soyayya da rahma a tsakaninku, lalle a cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani.” Suratur Rum. Ga kuma wani hadisi da ke cewa: “Abubuwa guda uku ba sa koshi daga wasu abubuwan guda uku. Namiji daga mace, kasa daga ruwa, Malami daga ilimi.”

Wasu Malaman tafsiri suna cewa: Zancen Aallah da ya ce ‘Kuma ya halitta daga rayukanku,’ ana nufin Adam (as) kenan. ‘Mata’ kuma ana nufin Hawwa’u (as). Kenan inda yake cewa ‘domin ku sami natsuwa zuwa gare ta, kuma ya sanya a tsakaninku soyayya da rahma.’ Sauran mazaje sun yi musharaka da Adamu (as) wajen samun natsuwa ga mata, domin kowane namiji yana samun natsuwa da sakina a wajen matarsa. Kamar haka zancen Imam Ali (as), inda ya ce “Daukakan idanu da kallon masoyi,” wato kallon masoyi yana zama sanyin ido zuwa ga masoyi. Akwai farin ciki da jin dadi a kallon masoyi izuwa ga masoyinsa.

Maganar cewa “Ya sanya soyayya da rahma a tsakaninku..” Wannan dabi`a ce da maza da mata suka yi musharaka a kai, kuma suka yi gadon sa daga kakanninsu Adamu da Hawwa’u. Misali a cikin mutane za ka so sauran ‘yan uwanka mutane, sai dai akwai soyayya mai tsananin karfi a tsakaninka da sauran ‘yan uwanka na jini fiye da sauran mutane. Mutum yana son kabilarsa fiye da sauran kabilu na daban. Kuma yana son ‘yan addininsa fiye da sauran na addinai. Kuma idan da za ka tambayi mutum cewa don Allah duk cikin matan duniya wacce ka fi so? Tabbas zai ce maka “Na fi son uwata sannan matata.” Kazalika ita ma matar.

‘Yan magana na cewa dan uwa rabin jiki, saboda tasirin soyayya da ‘yan uwantaka irin ta jini. Sa’annan namiji kan cewa matarsa “Ya rabin rayuwata.” Kazalika ita ma matar tana cewa mijinta “Ya rabin zuciyata.”

Abin da nake so in nuna a nan shi ne banda soyayya irin ta jini ba wata soyayya da take da tasiri ta rayuwar aure. Kashin bayan aure bai wuce abu guda biyu ba. Sune kiyaye addini da kuma soyayya.

Menene soyayya?

Akwai wani babban masanin falsafa da ya ce “Love is infinite,” wato soyayya wani abu ne mai wuyan bayani mai wahalar fassara, wanda ya keta hankali kuma ya zarce tunani. Wani kuwa masanin falsafa yana cewa so wani abu ne da yake dunkule zuciyar mutane biyu su zama tamkar zuciyar mutum guda. Malamin falsafar ga abin da yake cewa: “So wani abu ne da yake hade zuciyar makiya, ko abokan gaba su kasance tamkar zuciyar mutum guda.” Wani kuma ya ce soyayya ita ce take hada mutanen da suke da al’adu da addini daban-daban da harsuna mabambanta gami da kasashe, duk da haka sai su zama kamar zuciyar mutum daya. Wani kuma masanin falsafa yake cewa soyayya take sanya mutane masu ra`ayi da sabanin fahimta su kasance kamar jini da tsoka. Har yanzun wani kuma masanin falsafa yana cewa: So shi ne mutum ya sallama hankalinsa tunaninsa, kwakwalwarsa da gangar jikinsa gaba daya kuwa ga masoyinsa a bisa kashin kansa kuma ba bisa tsoro ba ko kuma bisa tursasawa! Wato ya mallaki huriyya a hannunsa ga haka!! Wani Malamin falsafa ya ce soyayya ita ce nuna tausayawa da juyayi da girmamawa da karramawa zuwa ga masoyi.

Akwai wasu manyan masana falsafa wanda daga cikinsu har da wanda ake wa kirari da uban fulsafa, wato Plato yana cewa kalmar soyayya (love) ta kunshi wasu kalmomi ne guda hudu. Haka ma ta rabu har kashi ko hawa hudu. Na daya ‘Eros’, wanda yake nufin so irin na sha`awa, wanda ana samun jima’i a tare da shi. So kenan tsakanin namiji da mace. Na biyu tunani ne wanda yake tattare da kauna ko zumuci, wanda ya takaita kawai a tsakanin abokai. Ana kiran sa ‘Philia’. Na uku wato ‘Storage’ ana nufin soyayya ce irin ta tsakanin da da uwa, ko tsakanin dan uwa da ‘yar uwa ko tsakanin uba da diyarsa, wacce babu sha`awa ko tunanin juna a cikinta. Kuma asalinta soyayya ce kawai ta haihuwa kuma iyakarta ba ta wuce iyali kawai. Na hudu ‘Agabe’ wato nuna kyautatawa zuwa ga makiyi duk kuwa da yadda yake munana maka.

Wasu kuma masu hikima sun ce: “Duk mai son wani abu yakan zama bawansa.” Zai zamana kenan duk safa da marwa da sa’ayinsa yana yin sa kawai domin ya dadadawa masoyinsa. Kuma a lokaci guda yana nisantar abin da zai bata wa masoyinsa rai. A takaice ina fatan ma`aurata sun fahimci ma`anar soyayya ko, da irinta, amfaninta a zamansu na aure?

Abu na gaba da za mu yi nazari a kansa, maganar ko me soyayya take bukata? da sauran matsaloli irinsu soyayya da adalci da soyayya da ‘yanci zuwa kammalawa.

Me soyayya take bukata?

Kamar zancen ‘yan magana akan cewa kare ana biki a gidanku ya ce in gani a kas! Bayan soyayya kasancewarta siffar Allah ce, to dan Adam an sam masa ita. Kuma muhallin zamanta a zuciya yake, kuma ana bambanta ta ko yin furucinta da harshe. Amma duk da haka wannan bai gamsar ba. Akwai sahabin da wani ya zo wucewa yake shaida wa Annabi ina son wane. Sai Annabi ya ce “Ka shaida masa?” Sahabin ya ce a`a. Annabi ya ce masa “Je ka ka shaida masa cewa kana son sa.” Tambaya, idan mutum ya ajiye soyayya a zuciyarsa kuma ya furta da harshensa shi kenan soyayya ta faru ta kare? Ko akwai sauran mas’uliya da nauye-nauye da suka hau kansa? Wace hanya ta fi fassara gaskiyar soyayya a aikace? Bari mu koma ga wani hadisin Manzo domin fayyace wannan al`amarin. Manzo (s) yana cewa: “Gaskiya cikin da`awar soyayya ta tabbata a cikin dabi`u guda uku, wato shi mai da`awar soyayya yakan fifita zancen masoyinsa a bisa zancensa, ya zabi yardar masoyinsa a kan yardar waninsa.”

Wata rana wani mutum ya je har gida ya sami wani mai hikima a bisa cewa yana son su kulla soyayya a tsakaninsu. Sai yake ce masa ba zai yiwu ba sai idan za ka kiyaye wadansu sharudda da zan gindaya maka. Sai mutumin ya ce na amince, menene wadannan sharudda? Sai mai hikima ya kada baki ya ce: “Ka so masoyana kuma ka yi gaba da makiyina, ka boye sirrina kada ka shaida wa kowa, ka taimake ni da dukiyarka tare da jikinka a lokacin da nake tsananin bukata. Sannan ka yi kuka a lokacin kukana, kuma ka yi dariya a lokacin dariyata. Na karshe zub da hawaye a lokacin da ka ji an ce na mutu. Ka halarci jana`izata, sannan ka rinka zuwa makabarta kana kawo mini ziyara. Kuma duk mako ka rinka mini sadaka.”

Har wala yau an tambayi masanin falsafa menene hakikanin ba da hakkin soyayya? Sai ya ce: “Dole ne ka yarda cewa masoyinka ya fi ka daraja, kuma ka fifita shi a birbishin kanka, kuma ka fifita bukatunsa a bisa naka. Sauran ka dauka cewa iyayensa naka ne, kuma danginsa danginka ne. Kuma ka yarda cewa kai bawansa ne duk lokacin da ya bukaci hidimarka. Sannan ka aminta cewa dukiyarka tasa ce, kuma duk lokacin da ya nema za ka mallaka masa ita.”

Kuma Imam Ali (AS) yana cewa: “Ka karfafa soyayya a cikin hurumi.” Abin da wannan zancen Imam Ali yake nufi da karfafa soyayya a cikin hurumi, hurumi yana nufin alfarma ko wani abu mai daraja ko mutum dan Adam ko dabba ko rana ko wata. Abin da ake nufi a nan shi ne wajibi ne, kuma tushen soyayya ka rinka girmamawa da daraja duk wani mutum da masoyinka yake girmamawa ko darajawa, kamar iyayensa, danginsa, addininsa, kabilarsa, al`adunsa, garinsu. Misali tufafi ne ko abincinsu. Kuma ko da masoyinsa yana da kyanwa to yana da kyau duk lokacin da za ka wurinsa ka sayawa kyanwar nan tasa misalin kifi soyayye da madaran ruwa na gwangwani. Kuma ka dauke ta ka dora ta a bisa cinyoyinka kana mai wasa da ita, ko da kuwa kai ba ka ra`ayin kyanwa a rayuwarka, domin nuna sonka ga wannan kyanwar yana komawa ne izuwa ga wannan masoyin naka ba ita kyanwar ba.

Wani mai hikima ya kasance yana cewa: “Duk wanda furta cewa yana son iyayena, dangina da kuma addinina, to wannan mutumin ya zama masoyina ko da bai yi da`awar sona ba. Kuma duk wanda nuna gabarsa a fili ga iyayena, dangina da addinina, to wannan ya zama makiyina ko da kuwa yana da`awar so na!”

Yanzu mun fahimci cewa ba a raba hanta da jini. Kuma wajibi ne ka yi ruwa ka yi tsaki a kan komai idan ya shafi masoyinka. Tambaya wane lokaci ne masoyinka ya fi bukatar soyayya daga gare ka? Imam Ali ya ce “Dan uwanka shi ne wanda ya taimake ka a lokacin tsanani.” Tsananin kuwa ko na talauci, ko rashin lafiya ko gobara ko hatsarin mota ko ambaliyar ruwa ko bari ko fari da sauransu. Za ka taimaka masa ta hanyoyi guda uku. Ka tausaya masa da jajantawa da bakinka, ka taimaka masa da gangar jikinka sannan ka taimaka da dukiyarka.

Kamar yadda wani babban Malamin falsafa, wanda duk masana falsafa suka cira masa hula kuma suke shakkar sa wato Aristotle yake cewa, “Babban abin da yake sa wa mutum damuwa a rayuwa shi ne tsoron wani bala`i da zai fada mashi, ko zai fada wa masoyinsa ko ya fada masa ko kuma ya fadawa masoyinsa.”

Imam Ali (AS) yana cewa: “Mafi alheri a cikin mata sune masu nuna soyayya ga mazajensu, kuma masu yawan haihuwa.” Amma menene yake nuna gaskiyar soyayyar mace zuwa ga mijinta? Mace ta ce wa mijinta “Ya rabin zuciyata, shi kenan ta gama ba da hakkin soyayya a kanta, ko ta kalle ka ta yi murmushi? Ga hadisin Manzo (s) da yake cewa: “Mafi girman hakki a cikin mutane ita ce uwa, kuma mafi girman hakki a kan mace shi ne mijinta.” Daga wadannan hadisan guda biyu za mu iya fahimtar wajibi ne da ke kan mace da ta yi biyayya ga mijinta a bisa komai banda sabon Allah.

Za ka ji wasu matan suna kiran mahaifiyar mijinsu uwar miji. Su matan suna nufin mahaifiyar mazajensu ba iyayensu bane? Dole uwar mijinki ita ma uwarki ce! Dangane da illar rashin biyayyar mata ga mazajensu ga wata ‘yar kissa. Akwai wani mutum manemin mata, wata rana wani Malami yana masa wa`azin ya ji tsoron Allah ya daina zuwa gidajen karuwai. Sai mutumin ya ce “Allah gafarta, ina neman karuwai ne saboda suna da wasu halaye guda biyu masu kyau, wanda matanmu na aure ba su da shi!” Sai Malamin ya ce menene wadannan halaye guda biyu? Sai mutumin ya ce: “Tsananin biyayya da kuma tsafta.”

Wata rana wata mata ta je wurin wani babban Malamin zamaninsu take cewa “Yaya zan iya fahimta ko ganewa cewa mijina yana so na?” Sai ya ce “Dole ya kasance ba ya zagin ki ko iyayenki. Kada ya mare ki, kada ya duke ki sai da hakki na shari`a, kuma ya so iyayenki da danginki, ya rinka dafa maki abinci sa`annan ku ci abinci tare a kwano guda, har ma ya rika sanya maki loma a baki. Idan kun gama ya wanke tukunyar da na kwanon abincin. Idan kayanki ya yi dauda ya dau tufafinki yana wanke miki. Ya kasance yana kai miki ruwan wanka bandaki, ya kuma kasance yana yi wa kananan yara wanka da shafa masu mai da sanya masu tufafi domin ya hutar da ke, kana ya hana kansa yin barci da cin abinci a lokacin da kike cikin bakin ciki. Kuma ya taya ki murna a lokacin da kike farin ciki. Sannan idan kin mutu ya yi maki kuka.”

Hakika yana daga cikin tawali‘u miji ya rinka taya matarsa hidima a gida. Kuma yana daga alamar son ta yin abubuwa kamar girki, wanke tufafi, yi mata guga da kuma yin hakuri a bisa cutarwar da take yi masa. Kuma wajibi ne namiji ya sani mace amana ce da Allah ya sanya a hannunsa. Bari mu takaita bayanin da muke yi a kan abin da soyayya take bukata zuwa gare shi. Mu kuma rufe shi da bayanin wani masanin falsafa da yake cewa “Soyayya tana bukatar abubuwa har guda biyar. Bin shawara ko umurnin masoyi. Yin farin ciki a lokacin da masifa ta fada wa masoyi. Yin farin ciki da alheri idan ya samu masoyi. Jawo duk wani alheri zuwa ga masoyi da kuma tunkude wani sharri zuwa ga masoyi.”

Dangantar soyayya da adalci

Bari mu fara da ma’anar dangantaka. Ma’anarsa wani abu ne ya yi kama da wani abu, amma kuma a lokaci guda akwai bambanci a tsakanin sa da shi. Misali Hasan da Husaini sun yi kama da juna ainun a fuska. Tsawonsu ya zo bai daya. Sun zauna a ciki tare har wata tara, kuma sun fito rana daya. Wannan ya nuna kenan babu bambanci a tsakaninsu? E, duk da haka akwai wani bambancin abu guda daya, wato a dabi’unsu da halayensu. Mun rigaya mun yi bayani a kan soyayya da abin da ta kunsa da dabi’arta duk a takaice.

Yanzun za mu yi dan bayani, shi ma a takaice a kan adalci da abin da ya kunsa da ma’anarsa da dabi’arsa. Sannan kuma mu yi nazari a kan dangantar da ke tsakanin sa da soyayya. Ga wani zancen Imam Ali (as) da yake bayani game da bambancin da ke a tsakanin adalci da karimci, inda yake cewa “Adalci yana sanya abubuwa a gurabensu, karimci kuma yana dauke abubuwa daga gurabensu. Adalci shi ne shari’a mai bai wa kowa da komai hakkinsa. Shi kuwa karimci akwai iyaka a bigirensa. Saboda haka kenan ashe adalci ne a gaba da karimci.”

Akwai wani Malamin falsafa da kuma sanin halayyar zamani mai suna Fletcher, ga abin da yake cewa a bisa dangantar soyayya da adalci. Fletcher ya ce “Soyayya da adalci abu guda ne. Domin adalci wani abu ne da ya samu tushe daga soyayya. Babu wani bambanci.” Saboda haka soyayya wata aba ce da ake amfani da ita wajen hulda mutane a rayuwa, yayin da kuma adalci ke daidaita shi. Adalci an ce yana kunshe ne da bai wa kowane mutum hakkinsa, kuma wani abu daya da ya zamana hakki ne a bai wa kowane mutum hakkinsa shi ne soyayya; ashe kenan adalci da soyayya ma’anarsu daya. Sad da muka hadu da mutum fiye da daya kamar uku ko hudu, muna da bukatar mu nuna musu soyayya, kuma adalci ne zai fayyace irin mikdarin soyayyar da ya kamata mu bai wa kowannensu.

Adalci shi ne soyayya wanda ya yi aiki don magance matsalolinsu. Soyayya ba za ta iya zaman kashin kanta ba, ba tare da adalci ba, saboda adalci shi ne soyayya wanda ake amfani shi a wasu abubuwa na musamman.

Har wala yau Fletcher ya ba da labarin lamarin wani mai suna Sammy Davis, wanda yake bakin fata ne Banasare, daga baya sai ya koma ya shiga addini Yahudu, saboda addinin kirista ya ce ka so makwabcinka, shi kuma addinin Yahudu ya ce adalci! Adalci! Sai ya kasance ana nuna masa soyayya amma ana hana masa adalci. Wato ana nuna masa bambancin launin fata, saboda haka ya ce shi dai yanzun adalci yake so ba soyayya ba! Fletcher ya ce sabanin da ake iya samu kenan idan an raba soyayya da adalci.

Haka ma wani Malamin falsafa mai suna Niebuhr dan Amurka yana cewa: “Soyayya abu ne mai zarce iyakansa. Kuma so wani abu ne mara yiwuwa. Alhali kuwa adalci wani abu ne da za mu iya aiwatarwa a wannan al’ummar tamu.”

Wani masanin falsafa mai suna Brunner yana cewa: Bambancin da ke tsakanin adalci da soyayya shi ne, ita soyayya ta takaita ne a tsakanin mutane biyu, alhali kuwa adalci abu ne wanda yake faruwa a tsakanin gungun jama’a, jama’a.

Wani masani falfasa yana cewa: “Adalci ne ke sanya mu kare dukiyar makiyinmu daga lalacewa, kuma mu tsare ran makiyinmu daga salwanta. Sannan adalci ne yake hana mu zaluntar makiyinmu daga duk wani irin cutarwa. Alhali ita soyayya dabi’arta ita ce juyawa duk wani makiyi baya. Kuma soyayya tana nuna fito-na-fito zuwa ga makiyi ba tare da la’akari da kiyaye duk wani hakki ba!”

Wani Malamin falsafa yana cewa: “Bambancin da ke akwai a tsakanin adalci da soyayya shi ne, adalci ne ke sa mu duk lokacin da muka samu masoyanmu sun yi wani laifi ko ta’addanci sai mu sa hannu mu rufe idonmu mu hukunta su, kuma mu bude bakunanmu mu ce masu ‘yan ta’adda, tsinannu! Alhali ita dabi’ar soyayya tana hana mu mu sanya hannu mu kama masoyanmu sad da suka aikata laifi, balle ta mu hukunta su. Kuma soyayya tana hana mu mu bude bakinmu mu tsine wa masoyinmu a lokacin da ya aikata laifi ko ta’adanci.” A takaice adalci yana bukatar mu da kyautata wa makiyi duk da yadda yake cutarwa da munawa a gare mu. Kuma adalci yana hana mu goyon bayan masoyi, duk kuwa da yadda yake kyautatawa da girmamawa a gare mu; idan har ya aikata laifi ko ta’addanci. Kuma adalci yana bukatar mu da mu kama masoyinmu mu hukunta shi a lokacin da ya aikata laifi ko ta’addanci. Adalci cinnaka ne wanda bai san na gida ba, kuma makaho ne wanda ba ya ganin na gabansa. Sannan adalci a dabi’arsa shi ne wanda sabo da kaza ba ya hana yanka.

Za mu gabatar da wasu ayoyi guda biyu a cikin suratun Nisa’i, sannan mu kawo fassarar wasu malamai game da su. “Kuma idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba, to ku auri guda daya (mace), ko kuma abin da hannayenku suka mallaka…” Sai kuma wata ayar “Kuma har abada ba za ku samu ikon yin adalci ba a tsakanin mata, ko da kuma kuna masu kwadayin haka, to kada ku karkata matukar karkata, sai ku bar ta kamar ratayayya…” An tambayi wani Malami cewa “Kun ce Kur’ani ba ya karo da juna. Ga shi a cikin Alkur’ani an ce idan ba za ku iya adalci ba ku auri mace daya, kuma a wata ayar ana cewa har abada ba za ku iya yin adalci a cikin mata ba. Sannan a lokaci guda kuma an umurce ku da ku yi adalcin.” Sai ya ce masa a wata ayar kuma Allah yana cewa: “Bai kasance ba mu sanya ga wani namiji daga zuciyoyi guda biyu a cikin cikinsa.” Abin da ake nufi ba zai yiwu ba ga mutum ya daidaita soyayyar mutane biyu a cikin zuciyarsa. Dole ne idan aka ce ga mutane biyu, zuciya ta fi son daya. A cikin mahaifa biyu- uwa da uba, da ya fi son uwarsa, a lokaci guda kukma bai ce ba ya son ubansa ba. A bisa mizani yana son dukkaninsu biyun, kuma a bisa fifiko ya fi son uwarsa.

Haka idan mutum yana da ‘ya’ya goma dole a cikinsu ya fi son daya, a lokaci guda kuma yana son dukkaninsu. Haka ma uwa idan misali tana da ‘ya’ya guda tara, dole ne a cikinsu ta fi son guda daya. Kuma idan abin ka mika mata wuka a hannu ka ce mata ta yanka daya daga cikin ‘ya’yanta ko ta cire daya wanda ba ta so, ba za ta iya ba. Amma ba ta musun ta fi son daya a cikinsu!

Haka ma idan mutum yana da abokai guda talatin, dole ne a cikin su ya fi son guda daya. Saboda dabi’ar zuciya tana karkata ne zuwa ga abu daya a lokaci daya. Kuma ba zai yiwu ba ta karkata zuwa ga abubuwa guda biyu a lokaci daya rak! Sai Malamin ya ci gaba da cewa idan yana da mata guda biyu dole ne ya fi son dayansu a bisa ‘yar uwarta. Ayar farko tana maganar idan mutum ba zai iya adalci ba, to ya auri mace guda daya. Wato idan ya hada mata biyu ko fiye da guda biyu, daga uku zuwa hudu, kuma ya tabbatar zai nuna karkata da son zuciya ga dayan, kuma ya mayar da dayan ‘yar bora, to auren daya ya fi masa. Sannan wajen tufafi, ciyarwa da raba masu abubuwan bukatu, idan ya kasance ba zai iya masu raba daidai ko rashin karkata, ko fifita daya a bisa daya ba, ma’anar wadannan abubuwa guda uku ake kira adalci, to kada ya auri mace fiye da daya.

Wasu malaman suna cewa: Abin da wadannan ayoyi suke magana a kai shi ne ba zai taba iya yiwuwa ba har abada mutum ya daidaita so na mata biyu ko fiye da haka a zuciyarsa a lokaci guda. Dole a dabi’ar zuciyarsa ta karkata ga mace guda a wajen so. Wannan adalci na daidaita son mata biyu a lokaci guda a cikin zuciyar mutum guda ba zai yiwu ba. Domin a dabi’ar zuciya tana karkata ne zuwa ga mutum daya ko abu daya a lokaci guda! Kuma irin wannan adalcin ne Kur’ani yake maganar ba zai taba yiwuwa har abada ba, ko da kuwa mutum ya yi bakin kokarinsa, kuma ya yi kwadayin da ya yi hakan. Daidaita soyayya ko son mata biyu a cikin zuciyar mutum shi ne Kur’ani yake maganar ba zai yiwu ba. Irin wannan adalcin na daidaita son mata a zuciyar mutum kuma a lokacin guda shi ne Kur’ani yake maganar ba zai yiwu ba.

Adalci na biyu wanda ake bukatar mutun ya nuna rashin bambanci, ko son zuciya ko karkata a wajen yi masu tufafi ko ciyarwa da wajen biya masu bukata, wannan mai yiwuwa ne, kuma wajibi mutum ya aiwatar da haka.

Haka ma wani Malamin addinin Musulunci yana cewa adalci ana bukatar sa ne ga mutumin da ke da mace fiye da daya. Daga biyu zuwa sama. Adalci ga mai mata biyu ko fiye da haka shi ne ya warewa kowace dayansu gidanta daban ko dakinta da wajen wanka da dakin dafa abincinta da bandakinta daban, kuma ya sanya katanga a tsakaninsu. Sa’annan ya daidaita su a wajen ciyarwa, tufatarwa da wajen biyan bukata, ba bambanci, kuma babu nuna son zuciya ko karkata zuwa ga dayansu.

Kuma bisa kaddarawa idan a ce matar mutum za ta daina sanya hijabinta kuma ta daina yin sallah sam-sam, ya yi shiru bai ce mata komai ba, kuma bai nuna mata alamar damuwa ba ko kadan, so kenan ko adalci? Idan kuma bisa kaddarawa mutum ya yi wa matarsa dukan kawo wuka, sannan ya watsa mata ruwan batur duk fatar jikinta ya sallabe ta kware, so kenan ko adalci? Bisa kaddarawa idan mace ta sa wa gidan mijinta wuta ya kone kurmus ba a fitar da ko da allura ba, so kenan ko adalci? Bisa kaddarawa idan da mace za ta tura uwar mijinta a cikin rijiya kuma ta rufe murfin rijiyar ta hana kowa shiga domin ceto uwar mijinta har ta mutu a cikin rijiya, so kenan ko adalci? Idan kuma bisa kaddarawa mace mijinta ya yi ridda ya koma kamar addinin kirista, kuma ya dauko duk littafanta na addini har da Kur’ani, sa’annan ya kona tufafinta na sanyawa, amma ta ci gaba, duk da haka, ba tare da wata damuwa ba, suna zaune tare, so kenan ko adalci? Mai karatu sai ka yi alkalanci da kanka, domin yanzu ka san ma’anar soyayya da kuma ma’anar adalci ko!

Alaka tsakanin soyayya da ‘yanci

Babban masanin falsafa mai suna Mista Schuon dan kasar Jamus ya ce “Allah yana da cikakken ‘yanci na ya yi halitta ko kada ya yi halittar. Amma a bisa ganin damarsa sai ya yi halitta. Kuma a lokaci guda Allah ya dau wannan ‘yancin ya bai wa dan Adam. Saboda dan Adam yana da hankali. Zai iya mayyaze kyakkyawa daga mummuna. Kuma zai iya tantance sharri da alheri. Sai dai wannan ‘yanci ya sa mutum ya zama shaidani mai halayyar dabbanci. Ba za mu zargi Allah bisa cewa ya yi kuskure da bai wa dan Adam wannan ‘yancin ba. Kuma ba za mu zargi dan Adam bisa cewa bai cancanci da ma tun farko a ba shi ‘yanci ba. Sai dai mu ce dan Adam kawai ya tozarta wannan ‘yancin da Allah ya ba shi!”

Wani masanin falsafa ya ce: “Ma’anar ‘yanci shi ne duk wani aiki da mutum zai aikata shi a bisa kashin kansa kuma a lokaci guda yana da ‘yancin ya ki aikata shi.” Masanin falsafar yana cewa: “Ma’anar ‘yanci shi ne ka bar mutum ya yi duk abin da ransa ya sawwala masa, ko da zai kai shi ne zuwa ga halaka, ko wani mugun sharri. Shi kuma ma’anar soyayya ka hana mutum duk wani abu wanda yana iya tura shi zuwa ga bala’i, masifa da duk wani mugun sharri, ko ta hanyar magana ko kuma ta hanyar karfi ko da kuwa yana tsammanin cewa shi yana da ikon aikata haka din.

Bambanci a tsakanin doka da ‘yanci. Doka tana shafar komai da komai, kowa da kowa, alhali kuwa ‘yanci yana shafan wani abu ne ya bar wani abu. Kamar a Musulunci. Allah ya haramta yin zina a lokaci guda kuma ya halatta yin aure. Allah ya haramta shan giya kuma a lokacin guda ya halatta shan nono da zuma. Allah ya haramta cin naman alade kuma a lokaci guda ya halatta cin naman wasu dabbobi kamar shanu da tumaki. Kuma ‘yanci yana karkashin doka ne, doka take fayyace hurumi da iyakokin ‘yanci.

Miji ba ya da ‘yancin ya hana matarsa addini. Kuma ba ya da ‘yancin ya sanya ta saba wa Allah. Kuma ba ya da ‘yancin ya hana ta bin umurnin Allah, kuma dole miji ya bai wa matarsa ‘yanci na dan adamtaka da mutuntaka da Allah Ta’ala ya ba ta. Wajibi a kan mace ta bi mijinta a kan komai banda sabon Allah. Wajibi daga ‘yancin mace mijinta ya koyar da ita addini kuma ya yi tsayuwar daka ya ga tana bin addini sau da kafa, ba wai kaulan bila amalin ba. Kuma miji ya sani mace amana ce da Allah ya sanya a hannunsa. Idan ya kiyaye ya samu rahmar Allah da Aljanna. Kuma idan ya tozarta amanar ya hadu da fushin Allah da azabar jahannama.

Abubuwan lura

Marubucin wannan mukala a bisa gaskiya jahili ne bai san komai ba a addini sai dai roro da kale da ya dan yi. Duk inda aka ci karo da kuskure, to jahilcinsa ne ya bayyana a sarari ba wani abu ba. Shi ya sa ma ya fi mai da akalar rubutunsa ga ilimin falsafa, inda ya fi wayo da bude ido. Domin magana a kan addini sai malamai ba karambana ba!

   

Komawa Babban shafinmu