Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 12                                     Jimada Thani1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 12
  Jimada Thani
 DAGA TEBURIN EDITA
Irin Wainar da muka toya
 SHARHIN MUJAHIDAH
A gaida 'yan uwa mata
 WASIKU
Wasiku uku daga 'yan uwa mata
 BABBAN LABARI
Taron Nasarar Hizbullah a Zariya

Hizbullah ba za ta taba daukan kaskanci ba

Dole ne Malamai su hada kansu

Wajibi ne mu zama abin koyi

 HIRA TA MUSAMMAN
Shawara ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a

 LABARI
Lalacewar mata a Nijeriya

 FADAKARWA
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata
 NASIHA
Rayuwar aure a Musulunci

Kishiya Ko Abokiyar Zama?

 YARA
Ka tausaya ma dabbobi
 LIKITA
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda
 TARIHI
Gwarzantakar Ummu Wahab(R.A)
 RAYUWA
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Shirin hana almajirai bara zai yi nasara kuwa?

Hattara 'yayan talakawa

Kikan duba shafin

Almizan
  kuwa?
The Witness
  kuma fa?
Rayuwa
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure (2)

Daga Isa Sulaiman Kaduna

A fitowa ta 10 muka soma buga wannan makalar, don haka a wannan fitowar mun karasa. Allah ya sa an amfana.

Haka ma idan mutum yana da abokai guda talatin, dole ne a cikin su ya fi son guda daya. Saboda dabi'ar zuciya tana karkata ne zuwa ga abu daya a lokaci daya. Kuma ba zai yiwu ba ta karkata zuwa ga abubuwa guda biyu a lokaci daya rak! Sai Malamin ya ci gaba da cewa idan yana da mata guda biyu dole ne ya fi son dayansu a bisa 'yar uwarta. Ayar farko tana maganar idan mutum ba zai iya adalci ba, to ya auri mace guda daya. Wato idan ya hada mata biyu ko fiye da guda biyu, daga uku zuwa hudu, kuma ya tabbatar zai nuna karkata da son zuciya ga dayan, kuma ya mayar da dayan 'yar bora, to auren daya ya fi masa. Sannan wajen tufafi, ciyarwa da raba masu abubuwan bukatu, idan ya kasance ba zai iya masu raba daidai ko rashin karkata, ko fifita daya a bisa daya ba, ma'anar wadannan abubuwa guda uku ake kira adalci, to kada ya auri mace fiye da daya.

Wasu malaman suna cewa: Abin da wadannan ayoyi suke magana a kai shi ne ba zai taba iya yiwuwa ba har abada mutum ya daidaita so na mata biyu ko fiye da haka a zuciyarsa a lokaci guda. Dole a dabi'ar zuciyarsa ta karkata ga mace guda a wajen so. Wannan adalci na daidaita son mata biyu a lokaci guda a cikin zuciyar mutum guda ba zai yiwu ba. Domin a dabi'ar zuciya tana karkata ne zuwa ga mutum daya ko abu daya a lokaci guda! Kuma irin wannan adalcin ne Kur'ani yake maganar ba zai taba yiwuwa har abada ba, ko da kuwa mutum ya yi bakin kokarinsa, kuma ya yi kwadayin da ya yi hakan. Daidaita soyayya ko son mata biyu a cikin zuciyar mutum shi ne Kur'ani yake maganar ba zai yiwu ba. Irin wannan adalcin na daidaita son mata a zuciyar mutum kuma a lokacin guda shi ne Kur'ani yake maganar ba zai yiwu ba.

Adalci na biyu wanda ake bukatar mutun ya nuna rashin bambanci, ko son zuciya ko karkata a wajen yi masu tufafi ko ciyarwa da wajen biya masu bukata, wannan mai yiwuwa ne, kuma wajibi mutum ya aiwatar da haka.

Haka ma wani Malamin addinin Musulunci yana cewa adalci ana bukatar sa ne ga mutumin da ke da mace fiye da daya. Daga biyu zuwa sama. Adalci ga mai mata biyu ko fiye da haka shi ne ya warewa kowace dayansu gidanta daban ko dakinta da wajen wanka da dakin dafa abincinta da bandakinta daban, kuma ya sanya katanga a tsakaninsu. Sa'annan ya daidaita su a wajen ciyarwa, tufatarwa da wajen biyan bukata, ba bambanci, kuma babu nuna son zuciya ko karkata zuwa ga dayansu.

Kuma bisa kaddarawa idan a ce matar mutum za ta daina sanya hijabinta kuma ta daina yin sAllah sam-sam, ya yi shiru bai ce mata komai ba, kuma bai nuna mata alamar damuwa ba ko kadan, so kenan ko adalci? Idan kuma bisa kaddarawa mutum ya yi wa matarsa dukan kawo wuka, sannan ya watsa mata ruwan batur duk fatar jikinta ya sallabe ta kware, so kenan ko adalci? Bisa kaddarawa idan mace ta sa wa gidan mijinta wuta ya kone kurmus ba a fitar da ko da allura ba, so kenan ko adalci? Bisa kaddarawa idan da mace za ta tura uwar mijinta a cikin rijiya kuma ta rufe murfin rijiyar ta hana kowa shiga domin ceto uwar mijinta har ta mutu a cikin rijiya, so kenan ko adalci? Idan kuma bisa kaddarawa mace mijinta ya yi ridda ya koma kamar addinin kirista, kuma ya dauko duk littafanta na addini har da Kur'ani ya kona, sa'annan ya kona tufafinta na sanyawa, amma ta ci gaba, duk da haka, ba tare da wata damuwa ba, suna zaune tare, so kenan ko adalci? Mai karatu sai ka yi alkalanci da kanka, domin yanzu ka san ma'anar soyayya da kuma ma'anar adalci ko!

Alaka tsakanin soyayya da 'yanci

Babban masanin falsafa mai suna Mista Schuon dan kasar Jamus ya ce "Allah yana da cikakken 'yanci na ya yi halitta ko kada ya yi halittar. Amma a bisa ganin damarsa sai ya yi halitta. Kuma a lokaci guda Allah ya dau wannan 'yancin ya bai wa dan Adam. Saboda dan Adam yana da hankali. Zai iya mayyaze kyakkyawa daga mummuna. Kuma zai iya tantance sharri da alheri. Sai dai wannan 'yanci ya sa mutum ya zama shaidani mai halayyar dabbanci. Ba za mu zargi Allah bisa cewa ya yi kuskure da bai wa dan Adam wannan 'yancin ba. Kuma ba za mu zargi dan Adam bisa cewa bai cancanci da ma tun farko a ba shi 'yanci ba. Sai dai mu ce dan Adam kawai ya tozarta wannan 'yancin da Allah ya ba shi!"

Wani masanin falsafa ya ce: "Ma'anar 'yanci shi ne duk wani aiki da mutum zai aikata shi a bisa kashin kansa kuma a lokaci guda yana da 'yancin ya ki aikata shi." Masanin falsafar yana cewa: "Ma'anar 'yanci shi ne ka bar mutum ya yi duk abin da ransa ya sawwala masa, ko da zai kai shi ne zuwa ga halaka, ko wani mugun sharri. Shi kuma ma'anar soyayya ka hana mutum duk wani abu wanda yana iya tura shi zuwa ga bala'i, masifa da duk wani mugun sharri, ko ta hanyar magana ko kuma ta hanyar karfi ko da kuwa yana tsammanin cewa shi yana da ikon aikata haka din.

Bambanci a tsakanin doka da 'yanci. Doka tana shafar komai da komai, kowa da kowa, alhali kuwa 'yanci yana shafan wani abu ne ya bar wani abu. Kamar a Musulunci Allah ya haramta yin zina a lokaci guda kuma ya halatta yin aure. Allah ya haramta shan giya kuma a lokacin guda ya halatta shan nono da zuma. Allah ya haramta cin naman alade kuma a lokaci guda ya halatta cin naman wasu dabbobi kamar shanu da tumaki. Kuma 'yanci yana karkashin doka ne, doka take fayyace hurumi da iyakokin 'yanci.

Miji ba ya da 'yancin ya hana matarsa addini. Kuma ba ya da 'yancin ya sanya ta saba wa Allah. Kuma ba ya da 'yancin ya hana ta bin umurnin Allah, kuma dole miji ya bai wa matarsa 'yanci na dan adamtaka da mutuntaka da Allah Ta'ala ya ba ta. Wajibi a kan mace ta bi mijinta a kan komai banda sabon Allah. Wajibi daga 'yancin mace mijinta ya koyar da ita addini kuma ya yi tsayuwar daka ya ga tana bin addini sau da kafa, ba wai kaulan bila amalin ba. Kuma miji ya sani mace amana ce da Allah ya sanya a hannunsa. Idan ya kiyaye ya samu rahmar Allah da Aljanna. Kuma idan ya tozarta amanar ya hadu da fushin Allah da azabar jahannama.

Abubuwan lura

Marubucin wannan makala a bisa gaskiya jahili ne bai san komai ba a addini sai dai roro da kale da ya dan yi. Duk inda aka ci karo da kuskure, to jahilcinsa ne ya bayyana a sarari ba wani abu ba. Shi ya sa ma ya fi mai da akalar rubutunsa ga ilimin falsafa, inda ya fi wayo da bude ido. Domin magana a kan addini sai malamai ba karambana ba!

   

Komawa Babban shafinmu