|
Shirin hana almajirai bara: Zi yi nasara kuwa?
Daga Husaina Ahmad
A ranar Talata 8-7-2000 Uwargidan Gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asma'u Makarfi ta turo wakilanta zuwa gidan Mal. Abubakar wanda ke zaune a unguwar Aska da ke cikin Zariya city. Wannan Malamin yana daga cikin Malamai bakwai da matar Gwamna ta zauna da su domin fara shirin hana bara a jihar.
Wakilan Hajiyar sun zo ne sun yi wa almajiran tambayoyin da suka hada da cewa "Waye sunanka, wane gari kake zaune, ka taba makaranta, wane sana'a kake sha'awar yi, kana sha'awar makaranta, in ka gama wane aiki kake so, sannan a ina kake samun abinci? Da dai sauransu. Bayan an gama wadannan tambayayoyi sai almajiran suka rika zuwa ana daukar su hoto, kuma tela na gwada su. Hakan kuwa an yi shi ne domin sa su a cikin shirin koyar da almajirai boko. Wadanda aka yi wa wadannan tambayoyi sun kama ne daga kan yara masu shekaru hudu zuwa 18.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin wakiliyar Hajiyar mai suna Hajiya Sa'adatu Sani, inda ya tambaye ta dalilinn da ya sa ake daukar hoton yaran. Sai Hajiyar ta shaida masa cewa ana daukar hoton ne dn a gane yaron da aka yi wa tambayar shi ne ba wani ba. Sannan kuma za su hada sai su sa a fayil. Sannan kuma za su dinka ma yaran kayan makaranta wato yunifom domin su zama cikin tsari. Bayan haka kuma take cewa za su rinka amfani ne da lokutan da ake tashin almajiran domin su tafi bara, sai su hana su zuwa wajen baran su sa su a aji a koyar da su na mintoci 30.
Hajiyar ta shaida ma Wakilinmu abin da ya shafi abinci za su nemi taimako ne daga masu kudi, sai a kawo gidajen Malaman ana dafa wa almajiran ana ba su.
Da yake tattaunawa da Wakilinmu, Malam Abubakar Ibrahim Danbarno, daya daga cikin Malaman da ke da almajirai, ya ce Uwargidan Gwamnan ta nemi Malamai bakwai ne zuwa gidan Gwamnati da ke Kaduna. An zabo malaman ne daga garuruwa biyu. Malamai biyu daga Zariya, biyu daga Kawo Kaduna, wasu biyu daga Rigasa Kaduna, sai kuma Limamin masallacin Juma'a na Barnawa Kaduna.
Ya ce Hajiyar ta shaida masu cewa ta sami ra'ayin wannan shiri ne daga Mahaifinta, wanda ya ce da ta rika yin irin shirin da wasu matan gwamnoni ke na kashe kudin gwamnati kan abin da ba shi da amfani gara ta rika mika wa almajirai da ke makarantun allo. Daga nan Hajiyar ta nemi kowane Malami ya fadi adadin almajiransa, suka kuma fada.
Malam Abubakar ya fadi cewa in har Hajiyar ta yi shirin ne saboda Allah, to Allah ya taimake ta a kan aniyarta. In kuma ta yi ne domin dakushe hasken addini, to Allah ya dakusar da manufarsu. Ya ce wannan ce addu'ar da su Malam suka fito da ita daga gidan gwamnati. Irin wannan dari-dari shi ke zuciyar kusan kowa kan wannan matsala ta bara da almajiran allo ke yi a duk fadin Arewacin kasar nan. Don haka ko wannan shiri zai yi nasara? Lokaci zai tabbatar da haka.
|