Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 12                                     Jimada Thani1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 12
 Jimada Thani
 DAGA TEBURIN EDITA
Irin Wainar da muka toya
 SHARHIN MUJAHIDAH
A gaida 'yan uwa mata
 WASIKU
Wasiku uku daga 'yan uwa mata
 BABBAN LABARI
Taron Nasarar Hizbullah a Zariya

Hizbullah ba za ta taba daukan kaskanci ba

Dole ne Malamai su hada kansu

Wajibi ne mu zama abin koyi

 HIRA TA MUSAMMAN
Shawara ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a

 LABARI
Lalacewar mata a Nijeriya

 FADAKARWA
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata
 NASIHA
Rayuwar aure a Musulunci

Kishiya Ko Abokiyar Zama?

 YARA
Ka tausaya ma dabbobi
 LIKITA
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda
 TARIHI
Gwarzantakar Ummu Wahab(R.A)
 RAYUWA
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Shirin hana almajirai bara zai yi nasara kuwa?

Hattara 'yayan talakawa

Kikan duba shafin

Almizan
  kuwa?
The Witness
  kuma fa?
Rayuwa
Hattara 'ya'yan talakawa

Daga Isa Khamis, Kaduna

Ba kawai Larabawan jahiliyya kidahumai ba, hatta masu fadin rai da tinkaho na kasashen Turai, tarihi ya tabbatar cewa ba su dauki mace a matsayin cikakkiyar mutum ba. Suna mata gani-gani. Sun dauke ta mara kwakwalwa, ba ta da 'yancin mutumci. Bala'i ce kuma masifa cikin al'umma. Wannan irin bakin mugunta da zalunci na kasashen Turai ya haifar da hargowa, hargitsi, yamutsi da kace-nace har sai da aka yarda mata mutane ne cikakku ala tilas, ba ko arziki. Wannan ta shige.

Shaidan kuma ya kada masu sabuwar kida, sai suka shiga tika mummunar rawa. Bayan sun shiga kasashen musulmi da zalunci da barna sun kuntuka tsiya, sun sato littafai da kayayyakin wayewa na musulmi sun zo sun girka a kasashensu, sai abin da suke kira ci gaba ya bayyana, ga shi kuma ba su da dokoki na kiyaye mutunci.

Wannan ya bude kofar tsiyataku daban-daban, har abin da suke kira 'yanci ya hankada su, ya fizge su suka shiga fagamniya da hauma-hauma. Rashin kunya, rashin mutunci da rashin mafadi suka taru a kansu. Sakarci kuma babu kama hannun yaro. Irin duk abin da namiji ya yi mace sai ta ce allambaran ita ma fa sai ta yi. In ba haka ba kuwa ta ce an take mata hakki. Yanzu kuwa ka ji kungiyoyin kare hakkin mata sun shiga hargowa. Abinka da gayyan na gayyaro, yanzu ka ga an ba ta dama ta aikata duk tsiyar da Shaidan ya sawwala mata.

Lokaci na tafiya, zuciyoyinsu na dada bushewa, linzami kuma ya tsinke. Yanzu kam an gangara kogin bala'i saboda tsabar wayewa da 'yanci. Suna kuma da magoya baya, masu gurbatacciyar fahimta irin tasu a kasashe da dama, wadanda suka zama dabbobi kuma marasa hankali, mahaukata tuburan. Sune miskinai abin tausayi wadanda aka rude su da 'yancin rudu. Suka biye ma Sisi London ko Sisi Amerika. Ta zama Sisi Legas ko Sisi Sakkwato. Haba wayayyiya, yanzu da 'yancinki da komai za ki yarda a maishe ki furannin kan hanya? Wani ya kalle ki ya yi dariya ya wuce, wani kuma ya tsinka ya yar. Wani kuma ya bada maki kura ya wuce. Wai duk da sunan ke wayayyiya ce mai 'yanci. Kin caba ado, kin yi kwalliya, kina tafiya senta-senta, ke ga 'yar boko mai 'yancin walawa. Wannan ai kina wulakanta kalmar 'yanci da wayewa ne. Kuma tonon asiri ne kan cewa rayuwa Shaidaniya ta yi galaba a kanki. Wai ma shin kina da hankali kuwa?

Na ji labarin irinku da aka gurbata ma tunani har gashi suke saya dan kanti su kwama su burge mazaje. Wai suna koyi da watsattsu makamantansu na kasashen Turai. Kaico! A haka ne kuke cusa kanku zuwa ga wulakanci nau'i-nau'I, domin biya ma kanku sha'awa na dabbanci. Abin ya kai wadansunku da suka fitsare idanuwansu har shafe-shafe suke yi wai su yi fari kamar Turawa. Babu shakka suna daburcewa. Idan ka gan su sai ka ce kadangare jangwalagwada. Lalai kam an raina hankalinku, an maishe ku kayan kyale-kyale na jawo hankalin marasa hankali don su sayi wani kayan gwanjo. Kamar mujalla ko jarida ko tallar bakin mai a 'Sign board' kan hanya ko wani tarkacen, sai a lafta hotonku a jiki, ku kuma a cunna muku wasu 'yan Nairori, ku amsa kuna masu watsar da wayewar da kuke homan sa saboda rashin zuciya.

Saboda kazamin son duniya wasunku har fita suke yi garuruwa domin gudanar da kazamiyar sana'a ta watsewa. A wasu garuruwa ana kiran ku 'yan 'gudi ibinin' saboda irin kaskancin da kuke dauka da kunya, mai dan kyakkyawan riga sai ku kama gaisuwar munafunci, wai ku ga masu ladabin karya da yaudara. Kuna gallafiri, kuna sintiri kan hanya. Idan kun hadu da lalatattu irinku shi kenan jaki ya ga jaka. Assha kaiconku tir! Dabbobi kawai masu dabbanci, suna tinkahon wayewa amma suna bijiro da lafiyarsu zuwa ga tawaya da rugujewa.

Wane irin 'yanci kuke takama da shi alhali kuna tauye hakkin mutanen kirki ta hanyar bayyanar da kuke yi cikin shigar yara a lunguna-lunguna, kan titi, da kasuwanni. Don tsabar tauye hakkin mutane har makarantu da asibitoci kuke zuwa cikin dattin nan naku, wanda ke sa mutanen kirki amai da hararwa. Ku kuna fankaman ci gaba 'yanci da wayewar kai, sakewa da walawa. Kuna inkarin nasiha da bin ka'idoji, wai kun ce hakan yana tauye basira kuma wai yana haifar da ciwon damuwa.

Hala dai kuna fama da ciwon kwakwala ne! Ga alama kuna da saurin mantuwa in har kun mance sanadiyyar mutuwar 'yar Nijeriyar nan Samira Adamu a 'yan kwanakin baya. Ai tauyewar basira da kuke korafi, tare da cawon damuwa da kuka ce nasiha na haifarwa alama ce kan cewa har yanzu ba ku fahimci ma'anar 'yanci da wayewa ba, kuma ba ku san dalilin zaman lafiya, jin dadi da kwanciyar hankali ba.

Kun fa ishe mu! Tonon fadan naku ya cika yawa! Kuna fa addabar mu! Kuna zaluntar bayin Allah fa! Ai dabbobi su aka sani da yawace-yawace da shiga harkar da ba ta gamo su ba. To amma ku kyanzu kun ara kun yafa. Yara kun kwace masu kaya kuna ta kakabawa haka kurum ba gaira ba dalili, abin ko tsari babu.

Ni na san wasunku 'ya'yan talakawa ne. Kuma kuna da bukatu a matsayinku na mutane. Amma ai talauci ba hujja bane na watsar da mutunci, kamar dai yadda kashe kai bai zama adalci ba ga wacce bakin ciki ya uzzura mata. Wannan hanya ce da aka ratse kuskurarrriya. Ku dai kawai kun sanya hadama da kwadayi, mabudin wahala, a gaba. Idan ba ku fadaka ba tun wuri, to kuwa za su budo muku kofofin masifa da bala'i nau'i-nau'i. Ina jiye muku hatsarurrukan da za ku rinka shiga matukar ba ku shafa wa kanku lafiya ba. Su ma kansu fitsararrun da ke can kasashen Turai sun zama jangwam a kasashensu, suna shan zazzafar azaba. A cikin zukatansu ga rashin natsuwa da tashin hankalin da abin da suke kira 'yanci ya jawo masu. Balle kuma ku 'ya'yan talakwa da ke cikin mishkiloli goma da ishirin. Ga dai tsabar jahilci, ga duhun kai da tabarbarewar komai. Hattara dai in kuna da sauran hankali. Ku yi taka-tsantsan ko kwa sami albarkar kasancewa cikin salihan mata masu mutunci ababen girmamawa. Idan kuwa kun ki ji ba kwa ki gani ba. Karshen alewa kasa. Kuma tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwan kan tare ya lakada masa mugun duka!

   

Komawa Babban shafinmu