Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 11                                     Rabi'ul Akhir 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 11
  Rabi'ul Akhir

Kikan duba shafin

Almizan

  kuwa?
Sharhin Mujahidah
Mata kar a bar ku a baya!

A kwana a tashi ba wuya wurin Allah. Yau sama da shekaru ashirin kenan da Malama Zakzaky ya assasa kiran a koma ga littafin Allah a kasar nan. Kuma tun sannan ya shelanta cewa a harkar addini ana yi da mata. Ba fage ne da ya kebantu ga maza kawai ba. Tun lokacin aka soma ganin ‘yan uwa mata cikin hijabi, kuma duk wanda ya san su ya san su mutane ne da ke kokarin bin Allah a rayuwarsu ta yau da kulum.

A wancan lokacin da kuma kusan a ce shekaru goman farko na wannan kira da Malam ke yi, jama’a suna dari-dari da da’awarsa. Ta fuskacin mata, an yi zamanin da mace mai hijabi ta zama abar kallo, kusan kowa gani yake Malam Zakzaky ya zo da sabon abu.

Amma alhamdulillahi yanzu kusan in ka ga mata biyar, to biyu zuwa uku sun sa hijabi, ko kuma akalla lullubinsa. Yanzu ma wani salon ya shigo, har da masu rufe fuskarsu dungurungum. Launin baki da wasu suke sukan ‘yan uwa mata a kansa shi ne abin yayi.

Ba ta bangaren hijabi ba ma kawai, ta fuskacin zuwa makaranta, ‘yan uwa mata sune na farko. An yi zamanin da cikin zarge-zargen da ake wa Harka Islamiyya da Malam Zakzaky ke ja, akwai karatun mata. To amma yanzu karatun mata ya zama ruwan dare game duniya. Gidan kowa da shi. Da wuya ka shiga biranenmu da ma akasarin kauyukanmu ba ka tarar da dimbin mata da matan aure sun dukufa suna karatun Musulunci ba.

Har ila yau ‘yan uwa mata tun farkon kiran nan ba a yin tarururrukan wa’azi ka tarar ba su a gefe guda. A wancan lokaci wannan abin suka ne, kamar yadda mutanen Shehu Usmanu suka rika zargin cewa Shehu na tara mata a wajen wa’azozoinsa.

Ta wannan janibi ma sai mu sake shukura da hamdala don kuwa a yanzu har kungiyoyin mata musulmi ake da su. Kuma mata kan gayyaci ‘yan uwansu mata su taru a yi musu wa’azin Musulunci.

A shekarun baya ‘yan uwa mata da ke shiga sahun muzahara abin kallo ne. Su kansu mata da kan yi dafifi a gefen titi suna kallon muzaharar abin da suke cewa shi ne “La har da matansu suka fito!”

Sai ga shi yanzu Allah ya kawo mu lokacin da an yarda cewa fitowar mata a rin wadannan shirye-shirye ba aibi bane. Muna sane da yadda mata musulmi suka yi dafifi a Kaduna zuwa majalisa, suna cewa “Shari’a muke so!”

Banda wadanann misalai da muka kawo akwai wasu al’amura da daman gaske da asali ‘yan uwa musulmi almajiran Malam Zakzaky suka soma yin su a nan kasar, wanda da farko Malamai sun rika inkarinsu, amma yanzu sun amshe su sun zama kiraye-kirayensu.

Sanin kowa ne cewa yanzu musulmin wannan kasa sun yarda cewa a gwagwarmayar samarwa da Musulunci izzarsa da daukakarsa, mata na da rawar takawa.

Da yake Mujahidah na magana kan mata ne musamman, sai mu ce duk wadannan abubuwa da ke faruwa suna tabbatar da abu guda ne-gaskiyar da’awar Malam Zakzaky. Hakikatan mutanen kasar nan ba su san mafita bane, suna lalube ne, kuma a laluben nan nasu sai suna koyi da fahimta da kuma koyarwar Malam Zakzaky.

Gaskiya kwara daya ce. Allah ma ya ce in ba ku sani ba ku tambayi masana. Maimakon al’ummar Musulmi su tsaya suna lalube, to su amsa kiran Malam Zakzaky kawai, su sallama masa. Wannan ita ce gaskiya, kuma mafita.

Yanzu don Allah matar da za ta sa hijabi, watakila har ta rufe idonta, tana zuwa makarantar Islamiyya, tana kuma cewa shari’a take so, me zai hana ta ta shigo cikin sahun ‘yan uwa mata musulmi wadanda sun shafe shekaru akalla gomomi biyu suna wannan da’awa ba su fasa ba?

Ya kamata a ce duk mata musulma da ta kai wancan mataki, ta yi nazarin wannan dan bahasin da muka gabatar. Ko ba komai ‘yan uwa mata musulmi, almajiran Malam Zakzaky na gaba da su, ga shi kuma an ce bin na gaba bin Allah. Don haka Mujahidah na kira ga mata kar a bar ku a baya!

   

Komawa Babban shafinmu