| A gai da 'yan uwa mata
A watan Jimada Ula da ya gabata ne 'yan uwa mata masu gwagwarmayar Musulunci karkashin Malam Zakzaky suka shirya wani taro na murnar nasarar da kungiyar Hizbullah ta Lebanon ta samu kan Yahudawan Isra'ila. An yi wannan taro a Zariya, tare da gayyatar Shehunnan Malaman kungiyar guda biyu-Shaikh Ali da Shaikh Mahir.
A gaskiya wannan kokari na 'yan uwa mata abin a yaba. Don haka Mujahidah na jinjina masu. Da farko dai shirya wannan taro da suka yi ya nuna cewa sun soma kafada da kafada da bangaren maza na wannan harka. Yadda 'yan uwa maza kan shirya tarurrukan fadakarwa a kashin kansu su ma yanzu suna iyawa.
|