| Da karfinmu muka dawo!
Bismillahir rahmanir rahim
Mai karatu ga shi mun kuma dawowa. Kafin mu dawo sai da muka kalli gaba muka dubi baya, muka yi nazarin wane tsari ne zai fi burge jama’a a wannan sabon karni na gomiyar shekaru? A karshe muka ga cewa gara mu shiga cikin ajin mujallun Turanci ‘yan kadan da suke fitowa cikin launi ko kala. Mun yi amannar cewa wannan tsari zai sa ko a birnin London ko Los Angeles ko Paris mutum ya daga mujallar Mujahidah ya san za ta iya gogoriyo da mujallun da ake samu a irin wadannan birane.
Abin yana da wuya, musamman da yake mu muka san irin wahalar da ke tattare da harhada labaru, tsara su, bugawa, rarrabawa ga ‘yan talla da kuma tattara cinikin. Duk da haka dai mun shirya tsaf, shi ya sa ma muka dawo da karfinmu. Kuma kamar takwararmu Almizan mun shirya shiga hanyar sadarwa ta zamanin nan da ake kira ‘Internet’, ta yadda ‘yan uwa da ke warwatse a biranen duniya za su rika samun mujallar cikin sauki.
Wani sauyi mai ban sha’awa da muka fito da shi shi ne na shigar da ‘yan uwana mata cikin kusan dukkan harkokin mujallar nan. Shi ya sa ma na sami mukamin Editan Riko. Kuma bayan wannan fitowa zan tuntubi wasu ‘yan uwa mata da ke manyan biranen kasar nan don su zama zaunannun wakilanmu. Amma kafin nan ina kira ga ‘yan uwana mata cewa kamfanin IMP fa ya sakar mana kota, don haka mu tashi mu ba mara da kunya. Don haka wadanda Allah ya yi wa basirar rubuce-rubuce su dau alkalami su shiga aiki, Mujahidah tasu ce.
A wannan fitowa babban labarinmu shi ne rahoto kan irin wahalhalun da aka jefa mata a cikin rikicin Kaduna. Da fatan masu ta da irin wannan rikici za su hankalta su mai da wukar. Kuma jama’a su natsu cewa fitina a kwannce take…Ita kuma gwamnati ta agaza wa wadanda abin ya shafa.
Sannan mun yi hira ta musamman da Malama Zeenat Ibrahim Uwargidan Malam Zakzaky. Fa’idojin da ke cikin wannan hira ba su kirguwa, da fatan jama’a za su hankalta.
Dadin dadawa akwai mu da mukaloli da ‘yan uwa mata da dama suka rubuta. Sannan kuma ga jawabin da Malam Zakzaky ya yi wa ‘yan uwa mata na Zariya, a inda ya nuna cewa me za a yi da mace jahila? Don haka sai in ce a sha karatu lafiya!
|