| Wainar da muka toya
Bismillahir rahmanir rahim
Kafin in labarta maku irin wainar da muka toya a wannan fitowa ta 12, dole in ba ku hakuri kan jinkirin da aka samu. Babban dalili shi ne Hukumar gudanarwarmu ta mai da hankalinta sosai ga mallakar sabbin kwamfuta da sauran kayan aiki, abin da zai sa insha Allah mu ci gaba da fitowa ba kakkautawa.
Wainar da muka toya tana da yawa, don haka ba zan iya lissafo su ba. Amma dai mafi girmansu ita ce labarin abubuwan da suka wakana a taron da 'yan uwa mata suka shirya na murnar nasarar da kungiyar Hizbullah ta Lebanon ta samu kan Yahudawa 'yan kaka-gida a Lebanon. Kai wannan kokari na 'yan uwa mata abin alfahari ne, ko ba komai shi ne na farko a wannan harka Islamiyya, a inda aka gayyato Shehunnan Malamai daga makarantu biyu na addinin Islama-Shi'a da Sunni. Wakilinmu Yusuf Abdullah ya dauko mana komai. Ya kawo jawabin Shaikh Ali da Shaikh Mahir, da Shaikh Zakzaky da na Farfesa Ahmad Khani. Kai abin dai sai kun karanta.
Wata wainar kuma ita ce hirarrakin da Wakilanmu suka yi da Jami'an kungiyar dalibai musulmi (MSS) na Jami'o'in Ahmadu Bello Zariya, Jami'ar Bayero Kano, Jami'ar Usman Danfodiyo Sakkwato da Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Kaduna. Ba mu gina wani labari kwara daya kan abubuwan da suka ce ba don mai karatu ya tsinkayo darussan da ke cikin hirarrakin da kansa. Wannan babbar nasara ce ga mujallar nan, domin za ta sami shiga a wadannan wurare da muke matukar son mu jawo su a jika. Don haka ina labarta wa 'yan wadannan manyan makarantu cewa wannan mujalla tasu ce, kuma tana sa ran ganin rubuce-rubuce daga gare su.
Hmn aka ce wai kishi kumallon mata. Ina ga ba haka bane. In mutum ya karanta makalarmu kan haka na tabbata zai gamsu. Waina ta uku kenan.
Wainarmu ta hudu ita ce maganar bara da ake kokarin a kau da ita a Arewacin Nijeriya. Wannan matsala ce da ta yi katutu a kasar nan. Labarinmu kan Wakilan da Hajiya Asma'u, matar Gwamna Makarfi na Jihar Kaduna ne ta tura Zariya karkashin Hajiya Sa'adatu Sani.
Sai kuma wainar da ya kamata in ambata a karshe ita ce wacce Isah Khamis ya rubuta, inda yake gargadi ga 'ya'yan talakawa. Allah ya sa mu amfana. Sauran wainar sai an duba ciki a gan su.
A ci ko a karanta lafiya zan ce?
|