| Shahararrun mata a Musulunci
Daga Nuruddin Usman Danja
Shaharbanun, matar Imam Husain (AS)
Ibn Babuwaih, wani shahararren masanin ruwaya ya ce a kan Imam Ridha (AS), lokacin da aka ci Khurrasan da yaki, ‘ya’yan Sarki Yazdgerd biyu an kama su a matsayin fursunonin yaki. Gwamnan lokacin ya yi nufin ya aure su. Imam Ali (AS) ya ce “Ka bar su don radin kansu; kar ka tilasta su a kan abin da ba shi suke so ba.”
Sai Gwamnan ya yi umurni da a sayar da matan biyu, ya ce a sanar da jama’a. Imam Ali (AS) ya ce “Bai dace ba a sayar da ‘ya’yan Sarki (gimbiya) ko da kafirai ne!” Daga nan ya nuna Shaharbanu da ta zabi miji da kanta. Da farko ta ki. Imam Ali (AS) ya sake cewa: “Ya ke yarinya tashi mana don ki zabi mijin aure don a yi addu’ar shaidar aure a tsakaninku. Ko ko ba ki son yin aure ne?”
Daga nan sai Shaharbanun ta yi shiru. Sai Imam (AS) ya ce “lallai shirunta alamar mika wuya ne.” Daga nan dai ya sake ba ta damar (‘yanci) ta yi zabin duk wanda take so cikin tawagarsa. Shaharbanu ta ce “Ni fa ba matar da zan wadatu da abin da ke kasa da hasken rana mai kwarara bace, kuma ga kyakkyawan tauraro mai walkawa, ni fa a gaskiya na zabi Imam Husain (AS).”
Nan take Imam Ali (AS) ya hada dansa Imam Husain (AS) da Shaharbanun, ya yi masu addu’ar daurin aure. Ya kuma ce da shi: “Wannan kyakkyawar (alheri) dace ne a gare ka, ka yi mata adalci.”
Imam Zainul Abidin shi ne dan da Allah ya azurta su da shi. Saboda haka Shaharbanun ta kasance irin da ke tsurar da tataccen ‘ya’ya na Imam Ali (AS) da Annabi Muhammad (SAW) bayan haihuwar Imam Sajjad (AS).
Robab, wata matar Imam Husain (AS)
Ita ‘yar Amr al-qais ce, mahaifiya ga Sakina da Abdullah (Ali asgar). Imam Husain (AS) ya kiyaye da ita sosai, kuma ya yi la’akari da ba ta matsayi da hakki matuka. Har ma an ce bayan shahadar Imam Husain (AS) Sayyida Robab ta sami masu son su aure ta da yawa, amma ba ta yarda ta auri kowa ba. Ta ce haba bayan kuma na hada zuriyya (auratayya) da Ahlin Manzo (SAW) kuma bayan samun wadatuwa da Imam Husain (AS) a matsayin mijina, ba na bukatar na abokanci kowa a matsayin miji.”
Lokacin da rundunar Ibn Ziyad (L) ta far ma su Imam Husain (AS) ta daga idonta ta ga kan mijinta, sai duk ta fice daga hayyacinta. Ta daga wannan kai (mai albarka da aka cutar) ta sumbanta tana kuka sosai, sannan ta sanya shi gefenta tana mai yabon sa.
Robab ta kasance tun wannan lokacin cikin dawwamammen bakin ciki, kuma ba ta wuce shekara daya ba ta koma ga Mahaliccinta.
Sayyida Laila, mahaifiyar Ali Akbar dan Imam Husain (AS)
Ita Laila ‘ya ce ga Abu Murrah, kuma mahaifiyarta ita ce Maimuna ‘ya ga Abu Sufyan Ibn Harb, kuma ita ce mahaifiyar Ali Akbar dan Imam Husain (AS). Ta kasance matar Imam Husain (AS), kuma daya daga cikin fiyayyun mata a zamaninta, wadda ba za a samu wata mata da za ta yi takara da ita ba a matsayi da falala a lokacin. Har ta kasance tana ci da talakawa, baki da abokai matukar gaya.
Ali Akbar (AS) danta, wanda ke daya daga cikin wadanda suka yi shahada a Karbala ya kasance yana da matukar kama da Manzo (SAW) sosai, har Imam Husain (AS) yakan ce “Duk lokacin da muka rasa Manzo (gare mu) sai mu dubi fuskar Ali Akbar.”
Ya kasance kodayaushe mai yawan (kyautatawa) da daraja (karramawa) kuma gwarzo ne tamkar Imam Ali (AS). A ranar Ashura ya ja daga da makiyansu matuka, kuma ya ga bayansu, yana mai yaze fushi ba tare da shakka ko kadan ba, tamkar Imam Ali (AS) yadda yake darkake makiya. Ya kashe da daman su wurin fadan gaba-da-gaba, har yana mai bayyana masu bakin cikinsa da damuwarsa gare su bisa zaluncinsu.
An ce bayan waki’ar Karbala Ummu Laila, mahaifiyar Ali Akbar ta kasance cikin matsanancin dawwammen bakin ciki, kuma an sami maganganu da yawa game da gudummawar da Laila ta bayar a ranar Ashura a Karbala.
Fatima ‘yar Imam Husain (AS)
Sayyida Fatima ‘ya ce ga Imam Husain (AS). Mahaifiyarta kuwa ita ce Ummu Ishak ‘yar Dalhat Ibn Abdullah Taimiyah. Imam Husain (AS) ya aurar da ita ga dan dan uwansa Hasan Musannah. Allah ya azurata su da ‘ya’ya uku. Sune: Abdullah Mahz, Ibrahim Ghamr da Hasan Musalla.
Fatima,wajen daukaka tsantsa da karama ta yi fice wajen kyau, har ma akan yi mata lakabi da Hurul-in. Mijinta kuwa Hasan Musanna ya yi matukar kwazo wurin fafatawa da makiya a Karbala. Har a nan ne ma aka yi masa munanan raunuka, a tsakanin shahidai da sojoji ya fadi.
Lokacin da makiya (LA) suka kai gaya wurin sarar su (fille wuyayensu) sai suka riske shi da rai, amma da kyar yake numfashi. Kasancewar mahaifiyar Hasan Musanna, Khul ‘yar kabilar Fazar ce, sai suka dauko shi zuwa Kufa (wurin danginsa) aka yi masa magani har ya warke.
Daga nan ya koma Madina, wanda a nan ne Allah (SWT) ya yi masa cikawa yana da shekaru 35. An kuma bisne shi a Baki’a a inda matarsa Fatima ta sanya tanti a kabarinsa na shekara guda don kokwanta masa.
Ummu Wahb
Wahb dan Abdullah ne dan Habib Kalbiy wanda ya kasane shi da matarsa da mahaifiyarsa suna rundunar Imam Husain (AS) ranar Ashura. Shi Wahb ya kasance kuma daga cikin sojojin Imam, wanda mahaifiyarsa Ghumra take karfafar sa don ya kare Imam.
Yakan fafuri makiya da sara da kisa har sai ya dire, sannan ya koma wurin mahaifiyarsa ya ce “Ya Ummi shin na sami yardarki?” Sai ta ce lallai ba zan yardar maka ba, har sai ka mutu (shahada) kana mai kare Imam Husain (AS).”
Haka matarsa ta roke shi da cewa lalle ya tsaya kar ya tafi a kashe shi ya bar ta bazawara. Amma sai Umminsa ta ce da shi ka tafi ka taimaka wa Imam Husain, in ba tare da yardarsa da yardata ba, ba abin da za ka samu (ceto) wurin kakansa Manzo (SAW).”
Matar Wahb din takan ce ma Imam Husain “Idan mijina ya rasu ya bar ni bazawara kenan fa!” Sai Imam ya ce “Za ki sami wuri a cikin ahlina.” Saboda haka Wahb ya koma fagen fama yana fafatawa har sai da aka sare masa hannun dama, amma duk da haka ya ci gaba da fada har sai da aka sake sare hannun hagu.
A nan ne matarsa ta sheka da gudu zuwa gare shi dauke da ginshikin tanti, ta ce da shi tana mai kuka, “ka yi fada iyakar fada har sai ka kubutar da Imam Husain daga hannun makiya.” Wahb ya ce wa matarsa “yaya kodayaushe kike kashe min gwiwa, kike dakatar da ni, kuma yanzu har kike karfafa ni in ci gaba da dauki-ba-dadi da makiya?”
Sai matarsa ta ce da shi, wallahi lokacin da na ji Imam Husain yana cewa “shin a nan babu wani mai taimakonmu ya taimake mu? Sai na yi tunani, na tabbatar lallai rayuwa bayan ba Manzo da ahlinsa ba ta da muhimmanci ko kadan.”
To a nan ne Wahb ya gamsu ya umurce ta da ta koma tanti, amma ko sauraron sa ba ta yi ba. A nan ne fa Imam Husain ya daga murya ya ce “lallai ki dawo za ki sami shiga da karbuwa ga Ahlina.” A nan ne matar Wahb ta koma cikin matan tawagar.
Nan take Wahb ya ci gaba da gumurzu har sai da ya cimma burinsa (ya yi shahada). Lokacin da aka sanar da matarsa, sai ta tafi a guje ta sanya fuskarta bisa tasa (sumbatarsa) ita ma nan gefen mijinta ta yi shahada.
Mutanen Kufa sun dauki Shahid Wahb zuwa ga Ibn Sa’ad, sai Ibn Sa’ad ya ce “Wane irin tsanantawa da zafi ka yi na yakar mu! Sannan ya ba da umurni a sare kansa daga gangan jikinsa, aka jefa shi cikin sojojin Imam Husain (AS). Nan take mahaifiyar Wahb (Ghumra) ta dauki kansa ta sumbata tana mai fadin. “Ya Ubangiji na gode ma saboda dana ya ba da jininsa gaba ga Imam, ban ji kunya ba gaban Imam Husain (AS).”
Sannan ta waiwayo ga mutanen Kufa ta ce da su “Ya ku makaskantan mutane! Wallahi na yi rantsuwa kiristawan da ke bauta a coci da matsafan da ke tsafinsu a gidan tsafi sun fi ku daukaka da matsayi.”
Nan da nan tana mai tsananin fushi da harzuka ta jefa kan danta cikin sojojin Ibn Sa’ad, azzalumi kuma babban kwamandan sojojin Yazid bin Mu’awiyya bin Abi Sufyan bin Harb, tana dauke da ginshikin tanti ta fafare su sai da ta kashe gwaraza biyu. Sannan Imam Husain ya kira ta ta koma gare shi. Imam ya ce “Ke da danki Wahb lallai kuna daga makusantana kuma makwabta wurin kakana Manzo (SAW) a Aljanna (bushara).” Ummu Wahb ta koma wajen mata tana cewa “Ya Allah kada ka kunyata ni.”
An samo daga Mahjuba vol.16 No.156 May 1997
|