Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 12                                     Jimada Thani 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 12
  Jimada Thani
 DAGA TEBURIN EDITA
Irin Wainar da muka toya
 SHARHIN MUJAHIDAH
A gaida 'yan uwa mata
 WASIKU
Wasiku uku daga 'yan uwa mata
 BABBAN LABARI
Taron Nasarar Hizbullah a Zariya

Hizbullah ba za ta taba daukan kaskanci ba

Dole ne Malamai su hada kansu

Wajibi ne mu zama abin koyi

 HIRA TA MUSAMMAN
Shawara ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a

 LABARI
Lalacewar mata a Nijeriya

 FADAKARWA
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata
 NASIHA
Rayuwar aure a Musulunci

Kishiya Ko Abokiyar Zama?

 YARA
Ka tausaya ma dabbobi
 LIKITA
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda
 TARIHI
Gwarzantakar Ummu Wahab(R.A)
 RAYUWA
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Shirin hana almajirai bara zai yi nasara kuwa?

Hattara 'yayan talakawa

Kikan duba shafin

Almizan
  kuwa?
The Witness
  kuma fa?
Tarihi
Gwarzantakar Ummu Wahb (R.A)

Wahb dan Abdullah ne dan Habib Kalbiy, wanda ya kasance shi da matarsa da mahaifiyarsa suna rundunar Imam Husain (AS) ranar Ashura. Shi Wahb ya kasance kuma daga cikin sojojin Imam, wanda mahaifiyarsa Ghumra take karfafar sa don ya kare Imam.

Yakan fafuri makiya da sara da kisa har sai ya dire, sannan ya koma wurin mahaifiyarsa ya ce "Ya Ummi shin na sami yardarki?" Sai ta ce lallai ba zan yardar maka ba, har sai ka mutu (shahada) kana mai kare Imam Husain (AS)."

Haka matarsa ta roke shi da cewa lalle ya tsaya kar ya tafi a kashe shi ya bar ta bazawara. Amma sai Umminsa ta ce da shi "Ka tafi ka taimaka wa Imam Husain, in ba tare da yardarsa da yardata ba, ba abin da za ka samu (ceto) wurin kakansa Manzo (SAW)."

Matar Wahb din takan ce ma Imam Husain "Idan mijina ya rasu ya bar ni bazawara kenan fa!" Sai Imam ya ce "Za ki sami wuri a cikin ahlina." Saboda haka Wahb ya koma fagen fama yana fafatawa har sai da aka sare masa hannun dama, amma duk da haka ya ci gaba da fada har sai da aka sake sare hannun hagu.

A nan ne matarsa ta sheka da gudu zuwa gare shi, dauke da ginshikin tanti, ta ce da shi tana mai kuka, "Ka yi fada iyakar fada har sai ka kubutar da Imam Husain daga hannun makiya." Wahb ya ce wa matarsa "Yaya kodayaushe kike kashe min gwiwa, kike dakatar da ni, kuma yanzu har kike karfafa ni in ci gaba da dauki-ba-dadi da makiya?"

Sai matarsa ta ce da shi, wAllahi lokacin da na ji Imam Husain yana cewa "Shin a nan babu wani mai taimakonmu ya taimake mu? Sai na yi tunani, na tabbatar lallai rayuwa bayan ba Manzo da ahlinsa ba ta da muhimmanci ko kadan."

To a nan ne Wahb ya gamsu ya umurce ta da ta koma tanti, amma ko sauraron sa ba ta yi ba. A nan ne fa Imam Husain ya daga murya ya ce "Lallai ki dawo za ki sami shiga da karbuwa ga Ahlina." A nan ne matar Wahb ta koma cikin matan tawagar.

Nan take Wahb ya ci gaba da gumurzu har sai da ya cimma burinsa (ya yi shahada). Lokacin da aka sanar da matarsa, sai ta tafi a guje ta sanya fuskarta bisa tasa (sumbatarsa) ita ma nan gefen mijinta ta yi shahada.

Mutanen Kufa sun dauki Shahid Wahb zuwa ga Ibn Sa'ad, sai Ibn Sa'ad ya ce "Wane irin tsanantawa da zafi ka yi na yakar mu! Sannan ya ba da umurni a sare kansa daga gangan jikinsa, aka jefa shi cikin sojojin Imam Husain (AS). Nan take mahaifiyar Wahb (Ghumra) ta dauki kansa ta sumbata tana mai fadin. "Ya Ubangiji na gode ma saboda dana ya ba da jininsa gaba ga Imam, ban ji kunya ba gaban Imam Husain (AS)."

Sannan ta waiwayo ga mutanen Kufa ta ce da su "Ya ku makaskantan mutane! WAllahi na yi rantsuwa kiristawan da ke bauta a coci da matsafan da ke tsafinsu a gidan tsafi sun fi ku daukaka da matsayi."

Nan da nan tana mai tsananin fushi da harzuka ta jefa kan danta cikin sojojin Ibn Sa'ad, azzalumi kuma babban kwamandan sojojin Yazid bin Mu'awiyya bin Abi Sufyan bin Harb, tana dauke da ginshikin tanti ta fafare su sai da ta kashe gwaraza biyu. Sannan Imam Husain ya kira ta ta koma gare shi. Imam ya ce "Ke da danki Wahb lallai kuna daga makusantana kuma makwabta wurin kakana Manzo (SAW) a Aljanna (bushara)." Ummu Wahb ta koma wajen mata tana cewa "Ya Allah kada ka kunyata ni."

An samo daga Mahjuba vol.16 No.156 May 1997

   

Komawa Babban shafinmu