| Barka da dawowa abokiyar hira
Daga Maryam (Jazbah) Abdullahi Unguwar Sanusi Kaduna
A gaskiya na yi farin ciki wanda ban san iyakarsa ba a lokacin da na ga sanarwar dawowar Mujahidah domin wanai mabudi ne da karin haske ga ‘yan uwa musamman wadanda ba su jin Turanci, domin ina mata kallon ‘yar uwa ce ga Mahjubah wacce take ta Turanci.
A karshe ina mika godiyata ga wadanda suka tsayu domin dawo da ita, da fatan Allah (T) ya kara tabbatar da mu tare da Malam Zakzaky. Su kuma ‘yan uwa mata kada su ba da kunya, su dage wajen aiko da rubutunsu akai-akia domin ci gaban wannan harka. Allah ya yi mana jagora, amin.
Gare mu ‘yan uwa mata
Daga ‘Yar uwa a Musulunci, Jamila Sabo Jahun
Godiya ta tabbata ga Madaukaki, tsarkakken Sarki. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin rahma, Baban Fatima, shugabar mata baki daya da iyalan gidansa tsarkaka.
Na ji dadin ganin sanarwar da aka yi dangane da fitowar wannan mujallah Mujahidah mai tarin albarka. Abin nufina a nan da jan hankalin da zan mana shi ne mu yunkuro mu yi wa addinin Allah hidima. Mu sani fa mune kashin bayan wannan addini, domin mune muke tare da yara manyan gobe, insha Allah. Dole mu tashi mu sadaukar da kanmu, mu isar da da’awa ta hanyar wannan mujalla.
Allah ya taimake mu karkashin Malam Ibrahim Zakzaky.
Nasiha ga ‘yan uwa mata
Daga ‘Yar uwa a Musulunci, Jamila Sabo Jahun
Ina farawa da sunan Ubangiji (SWT). Amincin Allah ya kara tabbata ga iyalan gidan Manzon rahma, Muhammad dan Abdullahi. Godiya ga Allah wadda ba ta da iyaka da Allah ya dawo mana da wannan mujalla mai tarin albarka. Allah ya tabbatar da mu, ya ba mu sabati da istikama karkashin Malam Ibrahim Zakzaky (H).
Duk da abin da zan fada an saba jin sa, wato tunatarwa ga ‘yan uwana musulmi, sai dai ita tunatarwa tana amfanar mumini, kuma a kodayaushe aka tunatar wasu sukan amfanu da tunatarwar.
Kasancewar mun sami kanmu cikin wannan addini mai daukaka da daraja (Musulunci) kuma muka kasance cikin masoya Allah masu gwagwarmaya domin a dawo kan tafarki irin wanda Manzon rahma ya bi ya isar da sakon Allha (T) yana da kyau mu ji tsoron Allah a duk rayuwar. Domin ita rayuwa ta hada duk wani abu. Sana’a ce, mu’amala da jama’a da sauransu. Idan har kina tsoron Allah to zai kasance komai naki yana tafiya bisa tsari na Allah (SWT). Ko da sabon Allah za ki yi, idan kika tuna da girman Allah da kuma tsoron saba masa, to za ki fasa wannan sabo. Kuma ko da karya za ki yi idan kina tsoron Allah cewa ya hana karya, to za ki fasa karyar.
Kuma mu dage wajen neman kusanci izuwa ga Mahaliccinmu, domin yardar Allah ta fi komai a wajen abin halitta. Kuma mu sani yardar Allah ba a samun ta haka zikau, sai mun tashi mun nema. Domin idan muka tuna da bayin Allah Madaukaka masu daraja, duniya da lahira ba haka nan suka sami daukakar ba. Suba tarihinsu ka gani, wace irin sallah suke yi? Ya nau’in azuminsu yake? Yaya hakura da bukatuwarsu don su wadatar da mai bukata take? Duk wannan abin mu yi koyi da su ne.
Mu kasance masu gaskiya. Mu sani duk fa abin da muka shuka shi za mu girba tsakanin alheri da sharri. Mu zauna da junanamu yadda addini ya tsara, kar mu cutar da junanmu da baki ko da hannu. Mu kasance ‘yan uwan juna masu son Allah ya hada mu a rahmarsa kamar yadda muka hadu a duniya dominsa.
Allah ya amfanar da mu.
Muhimmancin ilimi ga mace
Daga Aliya bn Muhammad Sadisu, College of art and Islamic Legal Studies, P.M.B 33, Minna, Niger State, Nigeria.
Zuwa Edita. Ina fata aiki na ci gaba. Allah ya sa haka amin. Dalilin wannan takarda tawa kuwa shi ne: A gaskiya na yi farin ciki da dawo da wannan mujallah mai farin jini wato Mujahida. Allah (T) ya taimake mu, amin. Kuma dangane da sanarwar da ka bayar a cikin Almizan, sanarwa ta farko, to gaskiya ko ni na dauka ba a bukatar maza su dan ce wani abu. To amma wannan sanarwar ta baya-bayan nan sai ta warke abin da ya dan yi ciwo. To Allah ya saka da alheri.
Saboda haka ne nake so Edita ya dan taimaka min da wani dan wuri a cikin mujallar don in ce ‘Muhimmancin ilimi musamman ga mace.’ Ba wai ina nufin ba shi da muhimmanci ga maza bane, don watakila a dan zarge ni kan hakan. Abin da ya sa na ce haka: Idan muka tsaya muka dubu namiji muka dubi mace, muka ga yadda Allah ya halicci kowa, da kuma irin al’amuran da ya jarrabi kowa, za mu ga cewa mata sune kan gaba. Misali mu dubi haila, janaba, nifasi, shayarwa ko kuma reno. Za mu ga daya ne maza suke da shi, amma mata duk sun hada. Kuma kowanne yana bukatar ilimi mai zaman kansa. Kuma dole ne Malama ta zama tana da ilimin kowannen, alabashi ma ta zama kwararriya a kai.
Idan aka ce mace na da ilimi, za ka ga yaranta, mu’amalarta, dabi’unta, sun bambanta da na wadda ba haka ba. Domin ita Allah da Manzo ne suke jagorantar ta. Ka ji kira’a ga ‘ya’yanta, ba zagi, ba yawo a kwararo. Ita kuma haba Malam, duk yadda jini yake yankewa ta sani, goshin magariba ne, bayan lisha ne ko kafin, ko bayan ketowar alfijiri ko kafin, da duk matsaloli da irin yadda za ta yi sallar. A gaskiya mata al’umma ne, don haka suna bukatar ilimi. Za ka ga ‘ya’yan wasu matan gwanin ban sha’awa, amma ‘ya’yan wasu kash!!
Saboda haka wallahi duk abin da za mu yi mu yi shi don Allah (T), mu tuna fa za mu tsaya a gaban Allah (T), ranar da dukiya da ‘ya’ya ba su amfana sai wanda ya zo da zuciya tsarkakka.
Wassalamu alaikum
|