Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 11                                     Rabi'ul Akhir 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 11
  Rabi'ul Akhir

Kikan duba shafin

Almizan

  kuwa?
Yara
Muhimmancin shayar da nonon uwa

Daga Zulaiha Husain Samaru

Ana so da zarar an yi haihuwa a wanke nono a shayar da yaro kafin uwa ta biyo. Domin wannan tsotso da jariri ke yi na shiga cikin kwakwalwa yana taimakawa wajen faduwar mahaifa ta biyo da sauri. Likitoci sun ce wannan hanya suke bi don taimaka wa mai haihuwa fadowar uwa da wuri. Ba kamar yadda wasu ke cewa ba wai sai bayan kwana uku da haihuwa.

Za a ci gaba da shayar da yaro nonon uwa har tsawon wata shida, sannan a fara ba shi abinci. Ba kuma kowane irin abinci za a ba shi ba, sai irin wanda zai yi masa amfani a jiki. Ko da uwa ta tashi bai wa danta abinci gara ta shirya masa da ta sayi na gwangwani. Misali ‘cerelac’, masara ne zalla sai dai dan sinadirin da suke sawa. Gara uwa ta shirya wa danta kamu.

Ga abin da za ta tanada wajen yin kamun: masara, waken soya da gyada. A jika su. In sun jiku sai a wanke a kai nika. In an nika sai a tace. In ya kwanta sai ta tsiyaye ruwan a kwano mai tsafta. In ta tashi dama kamun, in ruwan ya tausa sai ta dauki kullun ta rika zubawa a hankali tana juyawa har sai ya yi kauri. Sannan ta sauke ta juye a ‘flask’. In kuma ba ta da shi sai ta dama daidai wanda yaro zai sha a lokacin. Sannan a rika canza ruwa a kullum don kaucewa tsami daga waken soyan.

In kuma yaro ya fara cin tuwo, sai ki sami waken soya gwangwanin alale biyu, ki jika, ki wanke. In kin wanke sai ki kai nika. In an nika ki tace, ki sa sanwar abinci da shi a madadin ruwan sanwan tuwo. In ya tausa, sai ki yi dame ki tuka tuwo. Yana karawa yaro kuzari.

Yayen yara

Ya kasance idan mace za ta yaye danta sai ta tanaji wasu kayayyaki, wanda yake baban yaron zai siya da za a rinka ba yaron saboda hana shi shan nonon da ake yi. Uwargida ko amarya za ta nemi kamar su, kayan shayi biskit, kwai, hanta, nama da su kifi kafin a yi yayen. Wasu idan ba su tanadi wadannan kayayyaki ba yakan hana uwa yin yayen har sai lokacin da aka sami kayan da ake bukata.

Wadansu mata Hausawa da na zanta da su sun nuna a irin al’adarsu, ta Hausawa dole ne ki sami abubuwan da aka lissafa a zamanin nan kafin ki yi yayen yaron. Suka ce abu na farko da uwa za ta fara nema shi ne rubutu da ake yi wa yaran saboda kawazucin nonon uwarsa. Kuma akasarin Hausawa suna yayen ‘ya’yansu ne ranar Juma’a, wanda yake idan ba ranar Juma’a kika yi ba har sukan dan yi masa wani irin tunani irin na al’ada.

To dama ranar Juma’a wanda zai yi wa yaron rubutu zai yi, yana idar da sallar subuhi sai ya hau rubutu, da ma ya riga ya tanadi allonsa da alkalaminsa da kuma tawada kafin ya fara sallah. Yana idarwa sai ya dauko saboda ba ma a son ya tashi daga inda ya yi sallar. Idan ya gama, da ma akwai ruwansa a kusa da shi, da kuma kwanon sha, sai ya wanke a ciki. Sannan a aikawa da mahaifin yaron, wanda yake rubutun ne za a fara ba yaron ya sha, kafin nan a ba shi abincin da aka ga yaron nan ya fi bukata. Idan tuwo ya fi so ko kwai, ko dai wani nau’in abinci, sai a ba shi.

Ta bangaren uwa daman ta riga ta yi tanajin shuwaka da za ta shafa a kan nonon, idan yaron ya zo komawa idan ya ji daci sai ya saki. Wasu kuma matan suna shafa ja-da-yalo, shi ma wai idan yaron ya zo ya nemi nonon zai ji daci. Wasu kuma suna shafa toka ne a kan nonon ta yadda, idan yaron ya zo zai sha ya ga duk an bade da toka, sai a rinka ba shi tsoro, ana cewa “Dodo.” Yaron kuma sai ya tsorata ya ki kamawa. Amma wadansu yaran masu wayo, har sa harshensu suke yi suna gogewa da miyon bakinsu.

Wasu kuma suna kai yaran ne wajen kakanninsu ko kuma wajen abokan arzikin iyayensu. Don wasu suna cewa idan aka tashi yayen wance ko wane a kawo mani shi ko ita. Idan an kai yaron don yaye yakan yi mako daya ko biyu, sannan a dawo da shi a matsayin wai yaron ya manta da nonon mahaifiyarsa. Wasu irin wannan kaiwan da akan yi yakan jawo wa yaron matsala tunda yayen yakan dawo sabo ne, sai yaran su rinka yawan kuka. Alhali ana ganin kamar sun manta ne, shi ya sa ma aka dawo da su wurin iyayensu. Kuma Hausawa sukan ba yaron su wake da gero, a dafa wa ‘yan yayen din, wai zai daure masu ciki saboda yawan kashin da suke yi bayan an yi, wanda suke cewa suna yin kashin nonon da suka sha da can ne. Wasu kuma suna bayar da tunkuza ne, irin gyadan da aka matse domin fitar da mai a matsayin abin da zai daure wa yaron ciki, saboda irin kashin da suke yi na yaye, amma an ce ba dukkan yaran yake daure ma ciki ba.

Wata Malamar asibiti cewa ta yi idan za ki yaye danki kuma ba za ki yi kamar yadda Hausawa suke yin yayensu ba, ko kuma wata kabila ba, da take tsige yaro daga nonon mahaifiyarsa dare daya, kamar yadda akasarin mutane suka fi yi, abin da ya fi kyau a ka’idance shi ne mace idan tana shayarwa sai ta rinka rage adadin bayar da nonon. A misali kamar idan tana bayar wa sau barkatai a rana, sai ta rage irin bayarwan gwargwadon irin watannin da yaron yake da shi, har zuwa sau uku ko sau hudu a rana. Wannan zai sa idan ya kai watan da ya kamata a yaye shi, to ya riga ya saba da cin wasu nau’in abinci, kenan in an cire shi ba zai damu sosai ba.

Wannan tsari binsa yana da wuya ga mata saboda da yawansu ba su san iya adadin da suke ba wa yaransu nono ba. Duk da haka ganin irin illolin da ‘yan yaye ke fuskanta, ya kamata tun da wuri mata su rika nazarin sau nawa suke ba ‘ya’yansu nono? Tunda ga shi nazari na zamani ya nuna cewa daukan yara a kai su wurin yaye zai iya haifar masu da matsalar ciwace-ciwace, domin raba yaro da mahaifiyarsa ba karamin cutar da yara ke yi ba. Domin ta yiwu za a kai shi inda kila bai saba da su ba, ko bai ma san su ba, kin ga ga rashin mahaifiyarsa ga kuma rashin sabo da bai yi ba. Ga kuma rashin nonon mahaifiyarsa.

   

Komawa Babban shafinmu