Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Mujahidah

Babu Hukuma Sai ta Allah      -       Malam Zakzaky

     Fitowa ta 12                                     Jimada Thani 1421
 
Abubuwan ciki:
Fitowa ta 12
  Jimada Thani
 DAGA TEBURIN EDITA
Irin Wainar da muka toya
 SHARHIN MUJAHIDAH
A gaida 'yan uwa mata
 WASIKU
Wasiku uku daga 'yan uwa mata
 BABBAN LABARI
Taron Nasarar Hizbullah a Zariya

Hizbullah ba za ta taba daukan kaskanci ba

Dole ne Malamai su hada kansu

Wajibi ne mu zama abin koyi

 HIRA TA MUSAMMAN
Shawara ga iyayen da za su tura 'yayansu Jami'a

Da'awarmu na samun karbuwa a wajen dalibai

Mace mai tsoron Allah ya kamata ta je Jami'a

 LABARI
Lalacewar mata a Nijeriya

 FADAKARWA
Aikin da ke gaban 'yan uwa mata
 NASIHA
Rayuwar aure a Musulunci

Kishiya Ko Abokiyar Zama?

 YARA
Ka tausaya ma dabbobi
 LIKITA
Toshewar fitowar jariri da tsawaitar nakuda
 TARIHI
Gwarzantakar Ummu Wahab(R.A)
 RAYUWA
Muhimmancin soyayya a rayuwar aure

Shirin hana almajirai bara zai yi nasara kuwa?

Hattara 'yayan talakawa

Kikan duba shafin

Almizan
  kuwa?
The Witness
  kuma fa?
Yara
Ka girmama dabbobi

Daga Husaini Tahir Samaru

Wata rana Imam Hasan, alaihis-salam yana cikin cin abinci, sai kare ya zo ya tsaya gabansa, yana kallon sa. Imam Hasan (AS) ya sanya loman abinci a bakinsa ya kuma jefa ma kare nasa a gabansa. Ya ci ya kada jelarsa don godiya, ya yi haushi ya daga kansa ya kalli Imam Hasan (AS).

Imam Hasan (AS) ya jefa wani loman abinci a gaban karen. Wani mutum wanda zai wuce ta wurin ya zo gaba ga Imam ya ce, "Ba daidai bane wannan kare ya tsaya a gabanka ya hana ka cin abinci cikin natsuwa, ka yi mani izini sai in buge shi in korai." Sai Imam Hasan (AS) ya ce masa "A'a kar kai haka. Allah da ya halicce shi dabba yana son shi. Ai yunwa ce. Zan ji kunya gaban Allah in ci abincinsa da albarkansa sannan in ki bai wa halittarsa, duk da yana jin yunwa yana kallo na."

An fassaro daga Children guide to Islam na Hujjatul Islam Ibrahim Amini.

   

Komawa Babban shafinmu